Yar Tsohon Shugaban Kasa Ta Gana da Tinubu, Ta Rada Masa Shirinta na Takarar Gwamna

Yar Tsohon Shugaban Kasa Ta Gana da Tinubu, Ta Rada Masa Shirinta na Takarar Gwamna

  • Yar tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ta gana da Shugaba Tinubu a Lagos inda ta yaba da jagorancinsa
  • Iyabo Obasanjo ta jaddada kudirinta na tsayawa takarar gwamnan Ogun a zaben 2027 mai zuwa a jam'iyyar APC
  • Ta bayyana cewa tattaunawarsu ta mayar da hankali kan shugabanci, inganta dimokuradiyya da ci gaban kasa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abeokuta, Ogun - Sanata Iyabo Obasanjo wacce ta shiya neman takarar gwamnan Ogun karkashin jam’iyyar APC, ta gana da Bola Tinubu .

Iyabo Obasanjo ta yaba da yadda Shugaba Bola Tinubu ke kokarin karfafa dimokuradiyya da shugabanci a kasar nan.

Yar Obasanjo ta gana da Tinubu
Iyabo Obasanjo yayin ganawa da Bola Tinubu a Lagos. Hoto: @asovilladigital.
Source: Twitter

Iyabo Obasanjo ta bayyana hakan ne a wata sanarwa ta Punch ta samu inda ta yi karin bayani kan ganawarta da Shugaban Najeriyan a Lagos.

Kara karanta wannan

Gwamna ya ba Tinubu takobi, ya fadi bangaren da ya ke son ya yaka

Iyabo Obasanjo ta gana da Bola Tinubu

Yar siyasar ta bayyana cewa tattaunawar ta kasance mai amfani da kuma cike da darussa wanda zai kawo ci gaban kasa.

Iyabo Obasanjo, tsohuwar kwamishinar lafiya kuma sanata mai wakiltar Ogun ta tsakiya tsakanin 2007 da 2011, ta ce tattaunawar ta mayar da hankali kan shugabanci da ci gaban kasa.

Ta ce:

“Na samu damar ganawa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Lagos, kuma mun tattauna kan shugabanci, tafiyar da mulki da kuma ci gaban kasa da Ogun.
“Ina matuƙar gode wa Shugaban ƙasa bisa lokacinsa, hikimarsa da kuma jajircewarsa na dindindin wajen ƙarfafa dimokuradiyyarmu da tallafa wa sabqbbin shugabanni masu tasowa.
“Yayin da muke ci gaba da tuntuba gabanin zaɓen 2027, zan ci gaba da kasancewa mai kishin yi wa jama’a hidima da gaskiya, ƙwarewa da kuma tsarin da ya mayar da hankali kan jama’a.”
Iyabo Obasanjo za ta nemi takarar gwamna
Yar tsohon shugaban Najeriya, Iyabo Obasanjo. Hoto: Osigwe Omo-Ikirodah.
Source: Facebook

Iyabo ta nemi alfarmar Tinubu ta zama gwamna

Iyabo ta gode wa Shugaban kan lokacinsa da shawarwarinsa, tare da jaddada kudirinta na ci gaba da tuntuba yayin da ake shirin zaben 2027.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano za ta sauya salo bayan ganawar Shekarau da Tinubu, Abba Kabir

Ta ce za ta yi aiki da gaskiya, kwarewa da kuma tsarin da ya mayar da hankali kan bukatun jama’a idan ta samu damar zama gwamna.

Ta kuma bayyana cewa tana da gogewa a siyasar jihar Ogun, tana fahimtar bukatun jama’a da kalubalen da suke fuskanta.

A cewarta, abin da Ogun ke bukata a yanzu shi ne shugabanci mai fahimtar jama’a da kuma kudirin kawo sauyi a dukkan bangarorin tattalin arziki.

Ta kara da cewa idan aka ba ta dama, za ta mayar da hankali kan bunkasa ilimi, inganta kiwon lafiya da samar da ayyukan yi ga matasa, cewar Daily Post.

Iyabo ta jaddada cewa burinta shi ne ganin kowanne yanki na Ogun ya samu cigaba na gaskiya tare da inganta rayuwar al’umma baki daya.

Gwamna ya ba Tinubu kyautar takobi a ganawarsu

Tun farko, kun ji cewa Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun ya bayyana jin dadinsa bayan ganawa da Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu.

Gwamna Abiodun ya bukaci Tinubu ya ci gaba da yaki da laifuffuka da cin hanci da kuma ta'addanci a fadin kasar baki daya inda ya ba shi kyautar sabon takobi.

Ya tabbatar da cikakken goyon bayan yan Ogun ga shugabancin Tinubu inda ya ce yan jiharsa suna tare da shugaban a kowane irin hali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.