Nafiu Bala: Abubuwan da Ya Kamata a Sani game da Matashin da ke Neman Hana Ruwa Gudu a ADC
- Nafiu Bala dan siyasa ne daga Gombe, wanda ya tsaya takarar gwamna a 2023 da yanzu yake neman kawo matsala a jam’iyyar ADC
- Yanzu haka ya zama babban wanda ya hana jam'iyyar hamayya ta ADC sakat yayin da ya fara jayayya da shugabancin David Mark
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Gombe – Nafiu Bala, jigo a ADC da ke adawa da tsagin su Sanata David Mark matashi ne daga jihar Gombe wanda bai dade da fara siyasa ba.

Source: Facebook
Wane ne Nafiu Bala?
Daily Trust ta wallafa cewa ba a samu cikakken tarihin yarintarsa da karatunsa ba, amma maƙwabta a Nassarawo sun tabbatar cewa Bala ya halarci firamaren Nassarawo.
An haife shi a Unguwar Nassarawo, karamar hukumar Gombe, jihar Gombe shekaru kusan 35 da suka wuce.
Karatu a Gombe da fara aikin Nafiu Bala
The Cable ta ruwaito Nafi'u Bala ya yi karatu karamar sakandaren Nassarawo, sannan daga baya ya ci gaba da Government Day Technical College (Vocational) Gombe inda ya samu takardar shaidar SSCE a 2010.
Bayan haka, ya halarci AD Rufai College for Legal and Islamic Studies a Misau, Bauchi, inda ya kammala Difloma a shari’a a 2012.
Yaushe Nafiu Bala ya shiga siyasa?
Nafi'u Bala ya fara aiki a matsayin mai sa kai a ofisoshin lauyoyi masu zaman kansu a Gombe kafin ya shiga harkar siyasa a jam’iyyar DPP da tsohon gwamnan Sakkwato, Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya kafa.
Daga baya Nafi'u Bala ya koma PRP kafin ya shiga ADC inda ya tsaya takarar gwamna a zaben 2023 a Gombe, amma Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na APC ya doke shi tare da sauran ‘yan takara.
Mustapha Hadi, jagora a ADC Gombe, ya ce fitowar Bala ta siyasa ta karu sosai bayan zaben 2023, inda ya fafata sosai har zuwa kotun kolin kasa.

Kara karanta wannan
Tafiyar Gawuna ADC ta fara lahanta APC a Kano, shugaba a jam'iyya ya bi ubangidansa
Nafi'u Bala ya sha wahala a shari’ar zaben, wanda hakan ya kawo masa suna a kasa baki daya kuma ya ba shi damar samun matsayi a tsarin jam’iyya na kasa.

Source: Twitter
Daya daga cikin ‘yan uwan jigon da ya nemi a boye sunansa, ya bayyana cewa Nafi'u Bala ya fito daga gidan mutane masu rufin asiri.
Ya ce:
“Na san Nafiu tun yarintarsa. Ya shiga siyasa shekaru da dama da suka wuce, amma ba babban dan siyasa ba ne. Bayan zaben 2023 sai ya fara nuna ya isa, har ya kwashe matarsa zuwa Kaduna yayin da shi yake zaune a Abuja."
Da ake magana da shi game da zargin yi wa APC aiki a ADC, Nafi'u Bala ya musanta zargin cewa jam’iyyarsa na samun goyon bayan jam'iyya mai mulki don jawo tangarda.
Ya ce:
“Wannan zargi babu tushe. Ni ɗan ADC na tsawon shekaru 10. Mu dai muna so a bi tsarin jam’iyya."
Nafi'u Bala ya ce a matsayin sa na shugaban jam'iyya na kasa na wucin gadi, ya kamata a girmama matsayinsa har zuwa yau.
Jam'iyyar ADC ta sake darewa
A baya, mun wallafa cewa rikicin jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ya kara tsananta bayan bullowar sabon bangare ana shirin baban zaben 2027.
Sabon tsagin ya nesanta kansa daga bangaren David Mark da Nafiu Bala wanda ake ta yin rigima kan shugabancin ADC tun bayan farfadowarta a kwanakin baya.
Don Norman Obinna ya ce su ne sahihan shugabannin jam’iyyar, wacce yan adawa suka cika domin kifar da gwamnatin APC, saboda haka ba za su yi ƙasa a gwiwa ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

