Bayan Ya Yi Murabus, Majalisa Ta Canza Shawara kan Mataimakin Gwamnan Jihar Kano
- Majalisar dokokin jihar Kano ta janye sanarwar yunkurin tsige Kwamared Aminu Gwarzo daga kujerar mataimakin gwamna
- Hakan ya biyo bayan murabus din da ya yi bisa ra'ayinsa kansa, wanda hakan ya kawo karshen yunkurin majalisar na tsige shi
- Shugaban masu rinjaye, Lawan Hussaini ya ce janye shirin ya yi daidai da tanadin sashe na 3, ka’ida ta 6A na dokokin gudanarwa na majalisar
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Majalisar Dokokin Jihar Kano ta janye sanarwar tsige tsohon mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo.
Majalisar dokokin ta janye yunkurinta na tsige Aminu Gwarzo ne biyo bayan murabus din da ya yi daga mukaminsa.

Source: Facebook
Majalisa ta janye shirin tsige Aminu Gwarzo
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa an yanke wannan shawarar ne yayin zaman majalisar da Shugaban Majalisar, Rt. Hon. Jibril Isma’il Falgore ya jagoranta ranar Talata.
Bayanai sun nuna cewa Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar, Lawan Hussaini, ne ya gabatar da kudirin janye yunkurin tsige tsohon mataimakin gwamnan a zaman majalisa.
Yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan zaman, Hon. Hussaini ya bayyana cewa janyewar ta yi daidai da tanadin sashe na 3, ka’ida ta 6A na dokokin gudanarwa na majalisar.
Dalilin Majalisar Kano na janye shirinta
Hon. Hussaini haka nan kuma, ya nuna cewa murabus din da tsohon mataimakin gwamnan ya yi da kansa ya sanya babu bukatar ci gaba da daukar wani mataki daga bangaren majalisa.
“Mun janye dukkan tuhume-tuhumen da ake yi masa, sannan an riga an rufe maganar. Ba za mu ci gaba da bin diddigin wadannan laifuffuka ba domin aikinmu ya tsaya ne kawai ga tsige jami’i idan aka same shi da laifi.
"Tun da ya yi murabus da kansa, ta yaya za mu ci gaba? Mu ba EFCC ba ne ko ICPC; aikinmu ya kammala,” in ji shi.
Abin da ya jawo yunkurin tsige Aminu Gwarzo
Murabus din Gwarzo ya biyo bayan matakan da majalisar jihar Kano ta fara dauka na tsige shi bisa zarge-zargen da suka shafi gudanar da ayyukan rashin gaskiya, cin zarafin ofis, da kuma cin amanar kasa.
An fara shirin tsige shi ne a ranar 5 ga watan Maris, 2026, inda yayin gabatar da korafin a wancan lokacin, Majalisar ta kafa hujja da sashe na 188 na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999, cewar The Nation.

Source: Facebook
Zarge-zargen dai suna da alaka da lokacin da Aminu Gwarzo ya yi aiki a matsayin Kwamishinan Kananan Hukumomi tsakanin 2023 zuwa 2024, inda ake zargin sa da tafka wasu kura-kurai.
Abba na tsaka mai wuya a Kano
A wani labarin, kun ji cewa rikicin siyasa ya ƙara ƙamari kan naɗin Mataimakin gwamnan Kano bayan Kwamred Aminu Abdussalam Gwarzo ya yi murabus.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, na fuskantar babban ƙalubalen kan zaɓen sabon mataimakin gwamna, yayin da rikici ke ƙara tsananta a APC gabanin ganawarsa da ‘yan majalisa.
Hakan ya biyo bayan ziyararsa zuwa Abuja inda ya gana da tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, domin ƙarfafa alaƙa da tsofaffin jagororin jam’iyyar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

