Nafiu Bala: Kwankwaso Ya Mika Bukatar Ceto Jam'iyyar ADC ga Sarkin Gombe
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana kan rikicin da ya bulla a jam'iyyar ADC kan shugabanci kwanaki kadan bayan sauya sheka
- A wata hira da aka yi da shi, Kwankwaso ya bayyana cewa ya nemi zama da Nafiu Bala da ya ke cewa shi ne halastaccen shugaban ADC
- Madugun Kwankwasiyya ya yi kira ga manyan mutane ciki har da mai martaba Sarkin Gombe su ja kunnen Nafiu Bala kan shigar da ADC kotu
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Sanata Rabiu Kwankwaso ya bukaci manyan mutane, ciki har da mai martaba Sarkin Gombe, Abubakar Shehu Abubakar III kan shiga rikicin ADC.
Hakan na zuwa ne bayan wani dan jihar Gombe, Nafiu Bala ya nuna cewa shi ne halastaccen shugaban jam'iyyar a Najeriya ba Sanata David Mark ba.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro bayanan da Madugun Kwankwasiyya ya yi ne a wani bidiyo da DCL Hausa ta wallafa a shafinta na Facebook.
Kiran Rabiu Kwankwaso ga Sarkin Gombe
Kwankwaso ya bayyana cewa ya ji labarin cewa Nafiu Bala dan jihar Gombe ne saboda haka ya yi kira ga manyan jihar da su ja masa kunne.
Ya ce:
"Musamman shi Mai martaba Sarkin Gombe da ya sa baki, ko shi ko iyayensa ko wasu mutane da sauran sarakuna su sa abaki da dukkan 'yan siyasa da suka san shi, har da malamai da sauransu."

Source: Facebook
Kwankwaso ya bayyana cewa lamarin ya shafi miliyoyin 'yan Najeriya, saboda haka bai kamata a kyale Nafiu Bala ya lalata tafiyar ADC ba.
Sanata Kwankwaso ya nemi zama da Nafiu
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa ya nemi zama da Nafiu Bala da ya ke cewa shi ne shugaban ADC amma kuma hakan bai yiwu ba.

Kara karanta wannan
Gaskiya ta fito kan zargin Tinubu da haddasa rikicin ADC bayan hadewar Atiku, Obi da Kwankwaso
Kwankwaso ya ce:
"Jiya muka yi za mu sadu da shi to amma har asuba ina jiransa Allah bai sa ya zo ba, kuma dama wasu sun ce da ni ba zai zo ba, wannan ya sa na samu rashin jin dadi.
Kwankwaso ya sanar da cewa duk da ba su hadu ba, yana sanar duk wanda ya gan shi ya sanar da shi sakon da ya ke son isar masa.
Ya bayyana cewa dama yana son ba shi shawarar 'da da uba ne a matsayin shi na matashi:
"Bai kamata ya zama kadangaren bakin tulu ba."
Kwankwaso ya ce a fada masa:
"Abin da ya dauko a halin yanzu na tabbata ba zai taimake shi ba, ba zai taimaki ADC da ya ke so ya shugabanta ba, ba zai taimaki Najeriya, ba ba zai taimaki dimokuradiyya ba."
Ya yi kira ga duk wadanda suka gan shi da su ba shi shawara da ya hakura da batun shugabancin da ya dauko yana son kawo cikas.
Ya kara da cewa:
"Wannan zai zamo kuskure ne babba, kuma ya kamata ya sani musamman a wajen shi shi matashi.
Kwankwaso yi magana kan takara
A wani labarin, mun kawo muku cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana kan takarar shugaban kasa a zaben 2027 mai zuwa.
Da aka tambaye shi kan batun takara a ADC, Rabiu Kwankwaso ya sanar da cewa a yanzu za su fi mayar da hankali kan kawo wanda zai kawo sauyi a Najeriya.
Haka zalika ya yi kira ga 'yan Najeriya da su shiga jam'iyyar ADC da ya koma cikinta a makon da ya wuce, inda ya ce za su hada kai su ceto kasar daga hannun APC.
Asali: Legit.ng

