'Dan Marigayi Buhari Ya Amsa Kira, Ya Bayyana Kujerar da Zai Nema a Zaben 2027
- Yusuf Buhari, ɗan marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya bayyana sha'awar tsayawa takarar kujerar majalisar wakilai ta tarayya
- Ya aika da wasiƙar neman goyon baya ga jam'iyyar APC domin wakiltar mazaɓar Daura, Sandamu da Mai’Adua dake jihar Katsina a zaben 2027
- Tun mako guda da ya gabata ne jiga-jigan jam'iyyar APC na ƙaramar hukumar Sandamu suka amince da shi a matsayin ɗan takarar da suke so
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Katsina – Yusuf Muhammadu Buhari, ɗan gidan marigayi tsohon shugaban ƙasa, ya fito fili ya bayyana aniyarsa ta takarar kujerar majalisar wakilai ta tarayya.
Wannan na kunshe ne a cikin wata wasiƙa mai kwanan wata 3 ga Afrilu, 2026, wacce aka yi wa lakabi da "Nuna sha'awar tsayawa takarar kujerar majalisar wakilai ta mazaɓar Sandamu/Daura/Mai’Adua."

Source: Facebook
'Dan marigayi Buhari zai fito takara
A cikin wasiƙar, Yusuf ya bayyana cewa ya yanke wannan shawarar ne bayan tattaunawa mai zurfi da masu ruwa da tsaki na mazabar, a cewar rahoton Vanguard.
Ya jaddada cewa yana son bayar da gudunmawarsa wajen samar da ingantaccen shugabanci ga al'ummar mazabar Sandamu/Daura/Mai’Adua a majalisar wakilai ta tarayya.
Yusuf Muhammadu Buhari ya bayyana cewa babban burinsa shi ne kawo ayyukan raya ƙasa da kuma inganta rayuwar mutanen mazaɓarsa ta hanyar ilimi da sana'o'i.
A cikin wasiƙar tasa, ya bayyana cewa:
"Goyon bayanku zai taimaka wa burina na samun nasara, domin kawo ci gaban ababen more rayuwa da kuma gina mutane a wannan mazaɓa."
Yusuf Buhari zai yi takara karkashin APC
Tsohon mataimaki na musamman ga tsohon shugaban ƙasa, Bashir Ahmad, ya tabbatar da wannan labari a shafinsa na X (wanda aka sani da Twitter a da).
Bashir Ahmad ya bayyana cewa wannan matakin da ɗan gidan marigayi tsohon shugaban ƙasar ya dauka ya biyo bayan doguwar shawara da aka yi da manyan 'yan siyasa.
"Bayan doguwar tuntuba, Yusuf Buhari, ɗa ga tsohon ubangidanmu, marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, ya sanar da masu ruwa da tsaki burinsa na tsaya wa takarar kujerar majalisar wakilan tarayya don wakiltar mazabar Sandamu/Daura/Mai'Adua karkashin jam'iyyar APC."
- Bashir Ahmad.
Karanta sakon Bashir a kasa:

Source: Twitter
Masu ruwa da tsaki sun gamsu da Yusuf
Fitowar Yusuf Muhammadu Buhari takara na zuwa ne mako guda bayan da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a ƙaramar hukumar Sandamu suka nuna gamsuwarsu da takararsa.
A wani taron gaggawa da aka yi a sakatariyar ƙaramar hukumar, shugaban ƙaramar hukumar, Usman Na-Lado, ya bayyana cewa amincewa da Yusuf Buhari matsaya ce ta bai-ɗaya.
"Mun zaɓi Yusuf ne saboda cancantarsa da kuma yadda mambobin jam'iyya suka karɓe shi hannu biyu-biyu."
- Usman Na-Lado.
Ya ƙara da cewa baya ga Yusuf, taron ya sake jaddada goyon bayansa ga Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Dikko Radda domin su sake tsayawa takara a zaɓen 2027 dake tafe.
Rigima ta barke a APC kan takarar Yusuf
Tun da fari, mun ruwaito cewa, rikici ya barke a cikin jam’iyyar APC a Daura bayan wasu ‘yan jam’iyya sun amince da takarar Yusuf Buhari.
Hakan ya biyo bayan amincewa da dan marigayi Muhammadu Buhari a matsayin ɗan takara a majalisar wakilai daga jihar Katsina.
Wasu manyan jiga-jigan APC daga ƙananan hukumomi biyar sun yi fatali da zargin ɗora ‘yan takara, suna cewa ba za su amince da hakan ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


