Siyasar Kano: Abba na Zawarcin Shekarau Ya Dawo APC bayan Sun Rasa Kwankwaso

Siyasar Kano: Abba na Zawarcin Shekarau Ya Dawo APC bayan Sun Rasa Kwankwaso

  • Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf na ƙara zama domin jawo Sanata Ibrahim Shekarau zuwa APC
  • Sauye-sauyen siyasa da aka fara gani a jiharsun rikita tafiyar jam’iyyu a Kano gabanin babban zaben 2027
  • Tattaunawa na gudana a ɓoye kan yiwuwar sauya sheƙar Shekarau , yayin da jam'iyyu ke rububin ya dawo cikinsu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ƙara kaimi wajen ganin ya dawo da tsohon gwamnan jihar, Ibrahim Shekarau, cikin jam’iyyar APC, a wani bangare na sababbin sauye-sauyen siyasa.

Rahotanni sun nuna cewa lissafin siyasa a Kano ya sauya ne bayan da Abba Kabir Yusuf ya fice daga jam’iyyar NNPP ya koma APC, matakin da ya girgiza tsarin siyasar jihar.

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida ya shiga ruɗani game da naɗin mataimakin gwamnan Kano

Abba ya fara neman Shekarau ya dawo APC
Shugaban APC na Kano Umar Doguwa, Gwamna Abba Kabir Yusuf tare da Malam Ibrahim Shekarau Hoto: Imam Hannafi Shafi'u
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa a gefe guda kuma, jagoran NNPP na ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso, shi ma ya bar jam’iyyar inda ya koma ADC, lamarin da ya ƙara rikitar da tsarin haɗin gwiwar siyasa a Kano.

Siyasar jihar Kano ta rikice

Trust radio ta rahoto cewa sauye-sauy4 na kara rikita siyasar Kano inda tsohon ɗan takarar gwamna na APC a zaɓen da ya gabata, Nasiru Yusuf Gawuna, ya fice daga jam'iyyar zuwa ADC.

Tsohon Ministan tsaro, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya tarbe shi hannu bibbiyu tare da halartar rajistarsa a sabuwar jam’iyyar da ya koma.

Bayan dawowarsa daga Abuja, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aika da saƙo mai ƙarfi ga jam’iyyar ADC, yana mai cewa ba za su taɓa cin zaɓe a Kano ba.

Majiyoyi sun bayyana cewa gwamnan na ƙoƙarin shimfiɗa dabaru tun da wuri domin tabbatar da cewa ya ci gaba da riƙe kujerarsa bayan zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Tafiyar Gawuna ADC ta fara lahanta APC a Kano, shugaba a jam'iyya ya bi ubangidansa

Abba na neman Shekarau ya koma APC

Wani rahoto ya bayyana cewa gwamnan ya gana da Shekarau a Abuja kafin ya dawo Kano, a wani mataki na neman jawo shi cikin APC.

Wata majiya kusa da Shekarau ta tabbatar da ganawar, tana mai cewa tana daga cikin manyan shawarwari da ake yi domin lallashin tsohon gwamnan ya koma APC.

A yayin ziyarar, gwamnan ya je tare da shugaban APC na jihar Kano, Umar Haruna Doguwa, wanda hakan ke nuna muhimmancin ganawar.

Abba na son Shekarau ya dawo APC bayan Kwankwaso ya ƙara kafa ADC a Kano
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf yayin jawabi a wani taro Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Ziyarar na zuwa ne kasa da mako guda bayan da Shekarau ya nuna yiwuwar ficewa daga PDP, duk da cewa ya bayyana ba zai shiga ADC ba.

Shekarau, wanda ya taba rike mukamin ministan ilimi, har yanzu ana kallonsa a matsayin dattijo mai tasiri a siyasar Kano da PDP, kuma ana ganin zai iya sauya alkiblar siyasa idan ya yanke hukunci.

Har yanzu dai tsohon gwamnan bai fito fili ya bayyana matsayinsa ba, amma bayanai daga masu ruwa da tsaki na nuni da cewa ana ci gaba da tattaunawa, kuma akwai yiwuwar ya sake komawa APC nan gaba.

Kara karanta wannan

Jagora a APC, Danbilki Kwamanda ya fadi wanda zai ci zaben Kano a 2027

An cire rai Kwankwaso zai koma APC

A baya, kun ji cewa jigon APC a Najeriya, Alwan Hassan ya bayyana tasirin da Rabiu Musa Kwankwaso ke da shi a siyasar Kano da Arewacin Najeriya.

Alwan ya ce jam'iyyar APC na cikin matsala bayan komawar Kwankwaso zuwa jam'iyyar ADC mai adawa da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da ke mulkin kasa.

Jigon ya ce ba za a iya samun nasara a Kano ba tare da Kwankwaso ba, ya kuma zargi wasu gwamnoni da rashin kaunar Bola Tinubu yayin da zaɓe ke zuwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng