Abba Gida Gida Ya Shiga Ruɗani game da Naɗin Mataimakin Gwamnan Kano
- Rikicin siyasa ya ƙara ƙamari kan naɗin Mataimakin gwamnan Kano bayan Kwamred Aminu AbdulSalam Gwarzo ya yi murabus
- Fadar Shugaban Ƙasa na goyon bayan a naɗa Murtala Garo, amma ‘yan majalisa na matsa wa domin a naɗa shugabansu, Jibrin Isma'il Falgore
- Gwamna Abba Yusuf na cikin matsin lamba daga ɓangarori daban-daban domin ya nada wanda suke so gabanin zaɓen 2027
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, na fuskantar babban ƙalubalen kan zaɓen sabon mataimakin gwamna, yayin da rikici ke ƙara tsananta a APC gabanin ganawarsa da ‘yan majalisar dokokin jihar a gidan gwamnati.
Wannan mataki ya biyo bayan ziyararsa zuwa Abuja inda ya gana da tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, domin ƙarfafa alaƙa da tsofaffin jagororin jam’iyyar.

Source: Facebook
Labarin da ya kebanta ga Daily Nigerian ya bayyana cewa majiyoyi daga cikin jam’iyya sun bayyana cewa Ganduje da kuma Fadar Shugaban Ƙasa na da wanda suke so a nada a muƙamin.
Abba Kabir na cikin ƙalubalen siyasa a Kano
Rahoton ya ce Fadar Shugaban ƙasa na goyon bayan tsohon kwamishinan kananan hukumomi, Murtala Sule Garo, a matsayin wanda ake so ya zama mataimakin gwamnan Kano.
Sai dai wannan matsayi ya gamu da adawa daga manyan ‘yan siyasa daga Kano ta Arewa da Kano ta Kudu, daga ciki har da Sanata Barau Jibrin da Sanata Kawu Sumaila, waɗanda ke son a fitar da jerin mutane uku maimakon mutum guda.
Daga cikin masu adawa da Garo akwai tsohon shugaban APC na jihar, Abdullahi Abbas, wanda ke nuna damuwa kan rashin daidaito a jam'iyyar, ganin cewa Garo da Sanata Barau daga karamar hukuma ɗaya suke.
Bugu da ƙari, ana ta ce-ce-ku-ce kan shari’o’in cin hanci da rashawa da Garo ke fuskanta tare da Ganduje a babbar kotun Kano, tare da wata ƙara da ke gaban kotun ɗaukaka ƙara.
Abba: Barau, Fadar shugaban ƙasa sun rike wuta
A ɓangaren Sanata Barau, an ce sun gabatar da sunayen irin su Salisu Sagir Takai, Kabiru Lakwaya da kuma tsohon ministan kasuwanci, Ahmed Garba Bichi.
Labaran da ake samu sun ce a gefe guda, ɓangaren Kano ta Kudu na goyon bayan Kabiru Rurum wanda ya taba zama Shugaban majalisar dokoki a Kano.
Rahotanni sun nuna cewa tun farko gwamnan ya yi yarjejeniya da kakakin majalisar dokokin jihar, Jibrin Falgore, cewa zai ba shi kujerar mataimakin gwamna idan ya sauya sheƙa tare da wasu ‘yan majalisa.
Amma wannan yarjejeniya na fuskantar barazana sakamakon matsin lamba daga sama a kan lallai sai ya zabi wanda ake so, wato Sule Garo.
An kuma ruwaito cewa akalla ‘yan majalisa 28 daga cikin 40 na goyon bayan Falgore ya zama mataimakin gwamnan jihar Kano.
Sai dai wani sabon umarni daga Fadar Shugaban Ƙasa ya fito, inda ake zargin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci mataimakinsa, Kashim Shettima, da ya isar da goyon bayansa ga Garo ga gwamnan.
Ana ganin wannan matsayi ya samo asali ne bayan ficewar tsohon ɗan takarar gwamna na APC, Nasiru Yusuf Gawuna, daga jam’iyyar.
Duk da haka, rikicin cikin gida na ci gaba da ƙamari, yayin da gwamnan ke ƙoƙarin sasanta ɓangarori domin samun wanda kowa zai amince da shi.
A halin yanzu, gwamnan na tsaka mai wuya, inda yake tantance zaɓuɓɓuka masu muhimmanci da za su iya tabbatar masa da nasara ko kuma kawo masa cikas a zaɓen 2027.
Gwamna Abba da Ganduje sun zauna
A baya, mun wallafa cewa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da tsohon Shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje sun sa labule a kan siyasar jihar.
Shugabanni biyu sun yi wata ganawar sirri a Abuja kan rikicin siyasar Kano da ke sauya salo kuma tana ɗaukar zafi da batutuwa da suka shafi naɗin mataimakin gwamna.
Haka kuma tattaunawar ta shafi sauya sheƙa da ake samu a jihar, musamman bayan Nasiru Yusuf Gawuna ya sauya sheka zuwa jam'iyyar haɗakar hamayya ta ADC.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


