Rikicin ADC: Jam'iyyar Adawa Ta Roki Kwankwaso, Atiku da Obi Su Dawo Cikinta
- Wata jam’iyyar adawa a Najeriya ta bukaci manyan ‘yan adawa kamar Atiku Abubakar, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso su dawo cikinta
- Jam'iyyar ta bayyana haka ne domin ceto dimokuradiyya a Najeriya wanda ake zargin ana neman rikita jam'iyyun hamayya
- Hakan na zuwa ne yayin da jam'iyyar ADC ta sake burmawa cikin matsala wanda ake zargin gwamnatin APC da hannu a ciki
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ikeja, Lagos - Jam’iyyar PRP mai adawa a Najeriya ta ba manyan yan adawa kuma yan siyasa shawara kan zaben 2027.
Jam'iyyar ta bukaci manyan shugabannin ‘yan adawa, Atiku Abubakar, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso, su hade domin kare dimokuradiyyar Najeriya daga barazana.

Source: Twitter
Shugaban PRP na Lagos, James Adeshina ne ya bayyana hakan yayin wata hira da yan jarida, cewar rahoton Vanguard.
PRP ta fadi muhimmancin hadin kai a siyasa
James Adeshina ya jaddada muhimmancin hadin kai musamman a siyasar Najeriya duba da yadda aka sako adawa a gaba.
Ya yi wannan kira ne yayin da yake mayar da martani kan rikicin shugabanci da ke addabar ADC, jam’iyyar da wasu fitattun ‘yan adawa suka runguma gabanin zaben 2027.
Adeshina ya bayyana cewa sabon rikicin da ke faruwa a cikin ADC barazana ce ga hadin kan ‘yan adawa da kuma kokarin samar da madadin gwamnati mai karfi.
Ya ce:
“Yanayin siyasar Najeriya na sake fuskantar girgiza, a wannan karon a cikin ADC, inda rikice-rikice da rashin tabbas ke ci gaba da karuwa.”
Ya kara da cewa wannan matsala tana nuna wata babbar matsala a siyasar ‘yan adawa, wato rarrabuwar kai da ke hana su samar da karfi guda daya.
A cewarsa, a lokacin da kasa ke bukatar hadin kai, irin wadannan rikice-rikice na cikin gida na rage karfin ‘yan adawa wajen samar da sahihin madadi ga gwamnati.
Ya gargadi cewa hakan na iya bai wa bangare daya damar mamaye siyasa, tare da kara fargabar komawa tsarin jam’iyya daya a Najeriya.

Source: Facebook
An jaddada karfin PRP a Najeriya
Adeshina ya ce yayin da PDP da jam'iyyar ADC ke fuskantar matsalolin shugabanci, PRP na nan a matsayin jam’iyya mai karko ba tare da rikici ba.
Ya jaddada cewa halin da ake ciki na bukatar matakai masu karfi daga shugabannin ‘yan adawa domin ceto kasar daga halin da take ciki.
Ya bukaci ‘yan siyasa su daina ganin kansu a matsayin masu hamayya kawai, su fara aiki tare domin cimma manufa guda ta ceto Najeriya.
Ya kuma gayyaci fitattun ‘yan siyasa kamar Rauf Aregbesola da sauran shugabanni su shiga PRP domin samar da hadin kai mai karfi.
A cewarsa, PRP ita ce jam’iyya mafi dadewa a Najeriya mai tarihi na hadin kai, tsari da kuma akida mai karfi, cewar rahoton Daily Nigerian.
ADC ta zargi APC da shirin wargaza ta
An ji cewa jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta fara gano wani makarkashiya da gwamnatin APC mai mulki ke yi mata gabanin zaben 2027.
ADC ta zargi gwamnatin APC da yunkurin tarwatsa jam’iyyar bayan sauya sheƙar Rabiu Musa Kwankwaso zuwa cikinta.
Jam’iyyar ta yi alkawarin tunkarar duk wani yunkuri da doka tare da kira ga hukumar INEC ta kasance mai zaman kanta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


