Jerin 'Yan Siyasar da Suka Shiga ADC bayan Sauya Shekar Kwankwaso
Bayan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya sauya sheka zuwa ADC a ranar Litinin, 30 ga watan Maris, 2026 wasu 'yan siyasa sun koma jam'iyyar.
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - A ranar 30 ga watan Maris na shekarar 2026, tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya fita daga jam'iyyar NNPP zuwa ADC.
Sauya shekar kwankwaso ta sanya wasu 'yan siyasa sauya sheka daga jam'iyyun PDP, NNPP da APC zuwa jam'iyyar adawa ta ADC.

Source: Facebook
A wannan rahoton, Legit Hausa ta tattaro muku jerin 'yan siyasar da suka bi bayan Sanata Rabiu Kwankwaso zuwa jam'iyyar ADC.
1. Gawuna ya shiga jam'iyyar ADC
Dan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar APC a zaben 2023, Nasiru Gawuna, ya shiga jam’iyyar ADC a ranar Talata, 31 ga Maris 2026.

Kara karanta wannan
Bayan shigar Kwankwaso cikin jam'iyyar, ADC ta fallasa makarkashiyar da ake kulla mata
Punch ta rahoto cewa Gawuna ya yi rajista a cikin jam’iyyar tare da karɓar katin shaidar zama ɗan ADC a mazabarsa ta Gawuna da ke ƙaramar hukumar Nasarawa.
Taron ya samu halartar manyan ’yan siyasa ciki har da tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso; tsohon mataimakin gwamna, Aminu Gwarzo; da shugaban jam’iyyar ADC a jihar, Musa Ungogo.

Source: Facebook
Da yake jawabi bayan kammala rajistarsa, Gawuna ya gode wa magoya bayansa da shugabannin jam’iyyar, inda ya ba su tabbacin jajircewarsa wajen ƙarfafa jam’iyyar ADC a Kano.
2. Mustapha Kwankwaso ya shiga ADC
Biyo bayan sauya shekar Rabiu Kwankwaso, dan shi da ya rike kwamishinan matasa na Kano, Mustapha Rabiu Kwankwaso ya koma ADC daga NNPP.
A wani sako da ya wallafa a Facebook, Mustapha ya ce:
"Ina sanar da al’umma baki ɗaya cewa daga yau na na fita daga jam’iyyar NNPP a hukumance."

Source: Facebook
Biyo bayan haka, Mustapha ya sanar da shiga jam'iyyar ADC:
"Ban yanke wannan shawara cikin gaggawa ba, ina so in tabbatar muku cewa shawara ce da aka yi da natsuwa da tunani mai zurfi.
"A halin yanzu ina kan hanyar shiga jam’iyyar ADC, kuma ina farin ciki da wannan sabon mataki a tafiyata ta siyasa."
3. Yaya Bauchi ya shiga ADC
A ranar 31 ga watan Maris, 2026, dan majalisa mai wakiltar Gombe, Kwami da Funakaye a majalisar wakilai, Hon. Yaya Bauchi Tongo ya sanar da fita daga PDP.
A sakon da ya wallafa a Facebook, ya ce:
"Ina sanar da al’umma baki ɗaya a hukumance cewa na fita daga jam’iyyar PDP."

Source: Facebook
Wani rahoto da jaridar Tribune ta wallafa ya nuna cewa Hon. Yaya Bauchi na cikin 'yan majalisar wakilai da suka koma ADC bayan barin PDP.
4. Aminu Gwarzo ya shiga ADC
Mataimakin gwamnan Kano da ya yi murabus, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo ya bi Sanata Rabiu Kwankwaso zuwa jam'iyyar ADC.
A wani sako da ya wallafa a X, ya ce:
"Cikin matuƙar godiya nake farin cikin hada hanya da mai girma Sanata Rabiu Musa Kwankwaso wajen yin rajista da jam’iyyar ADC"

Source: Facebook
5. Godfrey Gaiya ya koma ADC
Mai ba shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas shawara kan harkokin siyasa, Godfrey Gaiya ya fice daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam’iyyar adawa ta ADC.
Gaiya, wanda tsohon shugaban kwamitin wasanni na majalisar wakilai ne, ya tabbatar da ficewarsa a wata hira ta musamman da Punch a ranar Alhamis, 2 ga Maris 2026.

Source: Facebook
A bayanan da ya yi bayan sauya shekar, Godfrey Gaiya ya bayyana cewa zai nemi kujerar Sanata a Kaduna ta Kudu a zaben 2027 mai zuwa.
6. Muktar Umar Tarauni
Hon. Muktar Umar Tarauni da ke wakiltar mazabar Tarauni a majalisar wakilai ya sanar da fita daga NNPP zuwa ADC tare da Kwankwaso.
Ya wallafa a Facebook cewa:
"Na fice daga jam’iyyar NNPP a hukumance, kuma na koma jam’iyyar ADC."

Source: Facebook
7. Isa Ashiru Kudan
Dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a 2019 da 2023 a jihar Kaduna, Isa Ashiru Kudan ya sanar da shiga jam'iyyar ADC bayan Rabiu Kwankwaso.
A sakon da ya wallafa a Facebook, Kudan ya sanar da cewa ya fita daga jam'iyyar PDP ne domin cigaba da fafutukar kawo cigaba a Kaduna.

Source: Facebook
INEC ta goge sunan 'yan ADC
A wani labarin, mun kawo muku cewa Shugaban hukumar INEC, Farfesa Joash Amupitan ya sanar da goge sunan shugabannin ADC a shafinsu na yanar gizo.
INEC ta sanar da cewa ta dauki matakin ne saboda karar da wani dan jam'iyyar ya shigar a gaban kotu yana cewa shi ne shugaban ADC.
Amupitan ya bayyana cewa INEC ba za ta cigaba da hulda da kowane bangare na jam'iyyar ba har sai bayan kotu ta yi hukuncin karshe.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


