INEC Ta Goge Sunayen Shugabannin ADC, Tafiyar Hadaka za Ta Iya Rushewa
- Hukumar INEC karkashin shugabancin Farfesa Joash Amupitan ta rusa shugabannin jam'iyyar adawa ta ADC da David Marka ke jagoranta
- INEC ta fitar da sanarwar rusa shugabannin ne a ranar Laraba, 1 ga watan Maris, 2026, inda ta ce an riga an shigar da korafi a gaban kotu
- A shekarar da ta gabata ne manyan 'yan adawan Najeriya kamar Atiku Abubakar, Nasir El-Rufa'i da sauransu suka karbi ragamar ADC
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta sanar da cire sunayen kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na jam’iyyarADC ƙarƙashin jagorancin David Mark daga shafinta na yanar gizo.
Matakin ya zo ne yayin da rikicin shugabanci ke ci gaba da ta’azzara a cikin ADC, inda ɓangarori masu goyon bayan Nafiu Bala Gombe da David Mark ke fafatawa wajen riƙe shugabancin jam’iyyar a matakin ƙasa.

Source: Twitter
Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a Facebook, inda ta ce za ta dawo da al’amura yadda suke kafin rikicin ya ɓarke, har sai an yanke hukunci a kan shari’ar da ke gaban kotu.
Hukumar INEC ta rusa shugabannin ADC
INEC ta ce a hukuncin kotu na ranar 12 ga Maris, 2026, ta umarci dukkan ɓangarorin da su bar yadda al’amuran shugabanci suke kafin rikicin, tare da gujewa duk wani mataki da zai iya shafar sakamakon shari’ar.
Sanarwar ta ƙara da cewa hukumar za ta guji ɗaukar duk wani mataki da zai iya sa a tilasta wa kotu wani sakamako ko kuma ya kawo cikas ga shari’ar da ke gaban kotun farko.
INEC ta kuma bayyana cewa duk da cewa ta ɗaura sunayen sababbin shugabannin NWC a ranar 9 ga Satumba, 2025, an riga an shigar da ƙarar da ke ƙalubalantar shugabancinsu tun ranar 2 ga Satumba, 2025.
Saboda haka, jaridar Daily Trust ta rahoto hukumar ta ce za ta bi umarnin kotu ta hanyar cire sunayen har sai an kammala shari’ar.
INEC ta dakatar da hulda da ADC
Bugu da ƙari, hukumar ta ce za ta dakatar da duk wata hulɗa da ɓangarorin jam’iyyar, ciki har da sa ido kan taruka, zaɓe na cikin gida ko manyan taruka, har sai an warware rikicin a kotu.
Ta jaddada cewa ba za ta karɓi wata wasiƙa ko hulɗa daga kowanne ɓangare ba dangane da harkokin jam’iyyar a wannan lokaci.

Source: Twitter
Haka kuma, INEC ta ƙi amincewa da buƙatar ɓangaren Bala na a ayyana shi a matsayin shugaban riƙo na jam’iyyar, tana mai cewa hakan zai saɓa wa umarnin kotu.
ADC: Gawuna ya hadu da Kwankwaso
A wani labarin, kun ji cewa Sanata Rabiu Kwankwaso da ya shiga jam'iyyar ADC ya gana da tsohon mataimakin gwamnan Kano, Nasiru Gawuna.
Ganawarsu ta biyo bayan murabus da Gawuna ya yi daga mukamin da shugaban kasa Bola Tinubu ya ba shi kafin shiga jam'iyyar ADC.
Tun a baya dai an ji Rabiu Kwankwaso na yabon Nasiru Gawuna, yana cewa tsohon mataimakin gwamnan na cikin kwamishinoninsa masu daraja.
Asali: Legit.ng

