Abba da Ganduje Sun Yi Zaman Sirri kan Batun Mataimaki, Sarki da Wasu Matsaloli a Kano
- Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da tsohon Shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje sun sa labule
- Jagororin biyu sun yi wata ganawar sirri a Abuja kan rikicin siyasar Kano da ke sauya salo kuma tana ɗaukar zafi
- Tattaunawar ta shafi sauya sheƙa da ake sama jihar, musamman bayan Nasiru Yusuf Gawuna ya sauya sheka zuwa ADC
Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, sun gana a babban birnin tarayya, Abuja.
Tattaunawar na zuwa ne kwanaki kadan bayan jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya tattare magoya bayansa sun shiga ADC.

Source: Facebook
A labarin da ya kebanta ga Daily Nigerian, an gano tattaunawar ta danganci manyan abubuwa uku da suka dabaibaye siyasar Kano a halin yanzu.
Abdullahi Ganduje da Abba Kabir sun gana
Rahotanni sun nuna cewa zaman ya mayar da hankali ne kan manyan batutuwa da suka hada da yadda ake fuskantar yawaitar sauya sheƙa daga jam’iyyarsu ta APC.
Kana an tattauna rikicin sarautar Kano da kuma batun gurbin mataimakin gwamna, wanda Kwamred Aminu AbdulSalam Gwarzo ya bari makonni kaɗan da suka wuce.
Tun da fari, Ganduje ya gana da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, inda ya yi masa bayani kan halin da ake ciki a siyasar Kano.
An duba sauya sheƙar tsohon dan takarar gwamna na APC, Nasiru Yusuf Gawuna, da kuma fargabar cewa wasu na iya bi sahu.
Majiyoyi sun ce Ganduje ya nuna rashin jin daɗi kan yadda fadar shugaban kasa ba ta rika tuntubarsa yadda ya kamata ba kan harkokin jam’iyya a Kano, abin da ya danganta da karuwar rikici a cikin jam’iyyar.
A yayin ganawar da shugaban kasa, an ce Tinubu ya ba da shawarar a ba Gawuna mukamin minista, amma Ganduje ya bayyana cewa wannan ya zo ne a makare, domin tuni ya koma jam’iyyar ADC.

Kara karanta wannan
Babban taron APC ya ci rayuka, hadimin gwamna da kansiloli 2 sun riga mu gidan gaskiya
Kan rikicin sarauta kuwa, Ganduje ya goyi bayan Aminu Ado Bayero, yana mai kira da a warware matsalar cikin gaggawa domin kada ta shafi lissafin siyasa gabanin zaben 2027.
Ganduje ya kawo wa Abba maganar Garo
Haka kuma, ya sake jaddada bukatar a yi la’akari da Murtala Sule Garo a matsayin mataimakin gwamna domin karfafa hadin kan jam’iyya.
Majiyoyi sun bayyana cewa bayan wannan, shugaban kasa ya umurci Gwamna Abba Kabir Yusuf da Ganduje da su gana domin nemo mafita kan matsalolin.
An ce Gwamna Gwamna Abba Kabir Yusuf ya isa gidan Ganduje da ke titin Haile Selassie a Asokoro, Abuja, da 1.00 na dare ranar Laraba, 1 ga watan Afrilu, 2026.
Ya je tare da dansa Al-Amin da kuma Mai ba shi shawara kan siyasa, Mohammed Jamu, inda jama’an Ganduje suka tarbe su.
Rahoton ya kara da cewa daga baya kuma dan majalisar tarayya mai wakiltar Bichi, Abubakar Kabir Bichi, ya halarci taron da aka yi a Abuja.

Source: Facebook
Bayanai sun nuna cewa an tattauna yadda za a dakile yawaitar sauya sheƙa da ke girgiza daidaiton jam’iyya a Kano, tare da nemo mafita ga rikicin sarautar da ya shafi Muhammadu Sanusi II da Aminu Bayero.
An ce Ganduje ya shawarci gwamnan da ya nada Murtala Garo a matsayin mataimakin gwamna, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen daidaita jam’iyya da kuma kara karfinta gabanin zaben 2027.
Sai dai a martaninsa, Gwamna ya nemi karin lokaci domin yin tuntuba kafin daukar mataki kan wadannan batutuwa. Rahotanni sun ce an kammala taron da misalin 2:40 na dare.
'Yan majalisa sun yi watsi da taron Abba
A baya, mun wallafa cewa ɗan majalisar Kano ta Kudu ya kauracewa taron da gwamnan jiharsa, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kira domin duba muhimman batutuwa.
Sanata Kawu Sumaila ya janye jikinsa daga wancan taro, inda ya gudanar da nasa taron tare da kiran jiga-jigan yan siyasa daga yankinsa tare da bayyana korafinsu.
Yan majalisar sun nuna damuwa kan abin da suka kira nuna wariya ga yankin Kano ta Kudu a lokacin da ake samun gagarumin sauyi a siyasar jihar gabanin zaben 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

