An Buga Kugen Siyasa; Kwankwaso Ya Sa Labule da Atiku, an Ji Abin da Suka Tattauna
- Manyan jiga-jigan jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya sun kai ziyara gidan tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
- Daga cikin jiga-jigan da suka ziyarci madugun na Kwankwasiyya har da tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar
- Ziyarar na zuwa ne bayan Kwankwaso ya sauya sheka zuwa jam'iyyar ADC sakamakon ficewarsa daga NNPP wadda ya yi takara karkashin inuwarta a 2023
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya gana da Alhaji Atiku Abubakar.
Rabiu Musa Kwankwaso ya karɓi bakuncin tsohon mataimakin shugaban kasar na Najeriya a gidansa na Abuja a ranar Laraba, 1 ga watan Afirilun 2026.

Source: Twitter
Tsohon dan takarar shugaban kasar ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a ranar Laraba, 1 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan
"Ba Legas ba ce"; Tsohon 'dan takarar gwamna ya fadi abin da Tinubu ba zai iya a Kano ba
Rabiu Kwankwaso ya gana da Atiku Abubakar
Sanata Kwankwaso, wanda yake tare da wasu jiga-jigan jam'iyyar ADC, ya bayyana jin daɗinsa na karɓar baƙin nasa.
Tsohon dan takarar shugaban kasar ya bayyana cewa ya yi amfani da damar ganawar wajen yin godiya ga Atiku kan tarbar da aka yi masa zuwa ADC.
"Na ji daɗin tarɓar ɗan uwana, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, da tawagarsa mai daraja a gidana da ke Abuja a yammacin yau."
“Tawagar tasa ta haɗa da Aminu Waziri Tambuwal, Alhaji Kashim Imam, Sanata Dino Melaye, Alhaji Adamu Maina Waziri, da sauran manyan shugabanni."
"Na yi amfani da wannan dama don gode wa Wazirin Adamawa bisa kyakkyawar tarbar da ya yi mani zuwa cikin jam'iyyar ADC, sannan na jaddada jajircewarmu na ganin jam’iyyar ta samu nasara a kowane mataki.”
- Rabiu Musa Kwankwaso
Me Kwankwaso ya tatauna da Atiku?
A ɓangarensa, Atiku ya tabbatar da ziyartar tsohon gwamnan na jihar Kanoa wani rubutu a shafinsa na X.
Atiku ya bayyana cewa sun tattauna muhimman batutuwan da suka shafi ci gaban jam'iyyar ADC.
“Na kai ziyarar ban girma zuwa gidan ɗan uwana kuma abokin tafiyata, Rabiu Kwankwaso, a yammacin yau."
"Mun yi kyakkyawar tattaunawa kan ci gaban jam’iyyar mu ta ADC, da kuma yadda ya kamata mu ci gaba da aiki don tabbatar da kyakkyawan shugabanci da farfaɗo da ƙasa cikin hanzari domin al'umma.”
- Atiku Abubakar

Source: Twitter
Ganawar tasu dai na zuwa ne bayan Kwankwaso ya sauya sheka zuwa jam'iyyar ADC a hukumance.
Tinubu ya girgiza kan komawar Kwankwaso ADC
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano na jam'iyyar PRP a zaben 2023, Salihu Tanko Takasai, ya yi tsokaci kan sauya shekar Rabiu Musa Kwankwaso zuwa ADC.
Salihu Tanko Yakasai ya bayyana cewa sauya shekar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ta rikita APC da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Tsohon dan takarar gwamnan ya bayyana cewa akwai abubuwa da dama da suka tabbatar da cewa siyasar Kano ta canja kuma an girgiza APC daga kasa har sama.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
