‘Mun Rasa Kano’: Jigon Jam’iyyar APC Ya Cire Rai bayan Kwankwaso Ya Koma ADC

‘Mun Rasa Kano’: Jigon Jam’iyyar APC Ya Cire Rai bayan Kwankwaso Ya Koma ADC

  • Jigon APC a Najeriya, Alwan Hassan ya ce Rabiu Musa Kwankwaso na da karfin siyasa sosai a Kano da Arewa
  • Alwan ya ce jam'iyyar APC na cikin matsin lamba bayan komawar Kwankwaso zuwa jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya
  • Jigon ya ce ba za a iya samun nasara a Kano ba tare da Kwankwaso ba, ya kuma zargi wasu gwamnoni da rashin kaunar Bola Ahmed Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Jigon jam'iyyar APC, Alwan Hassan ya yi magana game da tasirin da Rabiu Musa Kwankwaso ke da shi a jiha Kano.

Alwam Hassan ya bayyana cewa APC na cikin tsaka mai wuya tun bayan da Kwankwaso ya shiga jam'iyyar ADC mai adawa a kasar.

Dan APC ya ce ficewar Kwankwaso zai taba APC
Sanata Rabiu Kwankwaso da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso, Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Jigon APC ya bayyana haka ne a cikin wani bidiyon YouTube yayin hira da gidan talabijin Channels TV a jiya Talata 31 ga watan Maris 2026.

Kara karanta wannan

NNPP ta zama marigayiya: Kwankwasiyya ta faɗi yadda Kwankwaso zai raya ADC gabanin 2027

Kwankwaso: Jigon APC ya fadi kuskuren jam'iyyar

Alwan ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf bai da karfin siyasar da zai iya kayar da Rabiu Kwankwaso a Kano duba da yanayin siyasar jihar.

Ya bayyana cewa tun farko ya kamata APC ta yi kokarin shawo kan Kwanwkaso zuwa cikin ko kuma hadaka da shi a wata jam'iyyar.

Dan APC ya kuma bayyana yadda wasu suka hana Kwankwaso ganin Tinubu a lokuta da dama inda ya ce da an yi ganawar watakila a samu damar jawo shi cikin APC a sauki.

Ya ce:

"Bana tsammanin gwamnan Kano yana da karfin da zai yi nasara kan Kwankwaso a Kano.
"Idan da APC shawo kan Kwankwaso da ana maganar kuri'u miliyan uku da rabi ne, amma wasu na kusa da Tinubu sun hana Kwankwaso ganin shugaban kasa.
"Ba za mu taba yin nasara a Kano ba, ba tare da Kwankwaso ba, sai dai mu jawo shi APC ko kuma mu yi hadaka da shi a wata jam'iyya."

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Gawuna ya shiga sabuwar jam'iyya don karawa da Abba a 2027

Game da gwamnoni da suka sauya sheka zuwa APC da ma sauran yan asalin jam'iyyar, ya ce ba su son Shugaba Bola Tinubu ko kadan a ransu.

Yace a yanzu ana ba su makudan kudi na cire tallafi da aka yi amma kwata-kwata ba su kaunar shugaban, su na yin sane saboda bukatar kansu ta siyasa.

"Mafi yawan gwamnonin na da suka koma APC ba su kaunar Tinubu, yana ba su kudi masu yawa bayan cire tallafin mai."

- Alwan Hassan

Maganar tikitin Obi, Kwankwaso ta yi karfi

A wani labarin, an ji cewa maganar hadakar Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso na kara daukar hankali yayin da APC ke ci gaba da karfafa iko.

Wasu na ganin hadakar za ta kawo sauyi a zaben 2027, yayin da wasu ‘yan siyasa ke cewa ba za ta zama barazana ga gwamnati ba.

Rahotanni sun nuna cewa ana tattaunawa a boye kan tikitin hadaka musamman a kujerar shugaban kasa, amma har yanzu akwai sabani kan wanda zai yi jagoranci

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.