Buhari ya nada Alwan Hassan a matsayin mukaddashin shugaban bankin manoma

Buhari ya nada Alwan Hassan a matsayin mukaddashin shugaban bankin manoma

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Alwan Hassan a matsayin mukaddashin shugaban bankin manoma.

Shugaban kasar ya amince da sauke kwamitin rikon kwarya tare da nada mukaddashin shugaba.

Alwan Ali Hassan kwararren ma'aikacin bankin ne na sama da shekaru 20. Ya goge ba kadan ba a bangaren da ya shafi masana'antar bankuna.

Ministan aikin noma da raya karkara, Alhaji Muhammad Sabo Nanono ne ya sanar da hakan ta wasika mai kwanan wata 5 ga watan Mayu.

Buhari ya nada Alwan Hassan a matsayin mukaddashin shugaban bankin manoma
Buhari ya nada Alwan Hassan a matsayin mukaddashin shugaban bankin manoma Hoto: PRNigeria
Asali: UGC

Kamar yadda wasikar ta bayyana, nada Hassan a wannan matsayin shugaban bankin zai kawo babban cibgaba ballantana idan aka duba gogewarsa na shekaru masu yawa.

Ya yi aiki ba bankin PHB, First Bank, bankin UBA da kuma babban bankin Najeriya.

KU KARATA KUMA: An samu korona a jikin 'yan Lebanon 25 da suka koma kasarsu daga Kano

Alwan dan asalin jihar Kano ne kuma yana da digiri har na biyu a fannin kasuwanci.

Ya yi aiki da bankin Orient da ke Uganda, Bankin PHB a kasar Gambia da kuma Platinum Capital and Trust Limited a Najeriya.

Kafin a nada Alwan Hassan, ya yi aiki a matsayin shugaban Midrange Universal Biz Ltd, mamba ne a tsangayar kwararrun ma'aikatan banki da sauransu.

Yana da gogewa a fannin kasuwanci saboda ya halarci sananniyar makarantar kasuwanci ta IMD da Lausanne, makarantar kasuwanci da ke Switzerland da kuma makarantar kasuwanci ta Intrados da ke birnin Washington DC.

A matsayin bankin manoman na ma'aikatar habaka ayyukan noma da raya karkara wacce ke da alhakin kula tare da tallafawa al'amuran noma, za ta matukar amfana da gogewa irin ta Alwan Ali Hassan.

Hassan na da aure tare da yara.

A wani labarin kuma, fadar shugaban kasar Najeriya ta bada sanarwar cewa an yi wasu sauye-sauye a hukumar NBET da ke karkashin ma’aikatar wutar lantarki.

Shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatar da Marilyn Amobi a matsayin shugabar NBETE, sannan ya amince da nadin wasu sababbin manyan darektoci da za su sa ido a kamfanin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel