NNPP Ta Zama Marigayiya: Kwankwasiyya Ta Faɗi Yadda Kwankwaso Zai Raya ADC gabanin 2027

NNPP Ta Zama Marigayiya: Kwankwasiyya Ta Faɗi Yadda Kwankwaso Zai Raya ADC gabanin 2027

  • Ƙungiyar Kwankwasiyya ta bayyana cewa a halin yanzu, babu wani tasiri da jam'iyyar da suka bari ta NNPP ta ke da shi a Najeriya
  • Mai magana da yawun Kwankwasiyya ya ce ficewar Rabiu Musa Kwankwaso daga NNPP ya sa jam’iyyar ta mutu murus a jihar Kano
  • Ya ƙara da cewa shigarsa ADC na jawo ƙarin mabiya daga jihohi makwabta gabanin zaɓen 2027 mai zuwa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Mai magana da yawun ƙungiyar Kwankwasiyya, Habibu Mohammad, ya bayyana cewa ficewar Rabiu Musa Kwankwaso daga NNPP ya kawo ƙarshen jam’iyyar ne, musamman a jihar Kano.

A cewarsa, kowa ya san cewa NNPP ta yi fice ne saboda Kwankwaso, don haka barin da ya yi ya bar jam’iyyar cikin raunin da ya sa ake ganin ta mutu murus.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Gawuna ya shiga sabuwar jam'iyya don karawa da Abba a 2027

Kwankwasiyya ta ce za su yi wa ADC aiki
Sanata Rabiu Kwankwaso a lokacin da ya ke yankar tikitin zama dan ADC Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Twitter

Arise News ta ruwaito Habibu Mohammad ya ce hakan na iya shafar jam’iyyar ba a Kano kaɗai ba, har ma a faɗin ƙasa baki ɗaya.

'Kwankwaso zai yi wa ADC aiki' – Kwankwasiyya

Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya fice daga NNPP a ranar 29 ga Maris, 2026, sannan ya shiga jam’iyyar ADC a hukumance a ranar Litinin 30 ga Maris, 2026.

Kwankwaso shi ne jagoran NNPP na ƙasa kuma wanda ya kafa tsarin siyasar Kwankwasiyya, wanda ya zama ginshiƙin karfin jam’iyyar musamman a Arewa.

Habibu Mohammad ya ce:

"Kowa ya san NNPP da Kwankwaso abu ɗaya ne. Ficewarsa daga jam’iyyar kai tsaye yana nufin NNPP ta mutu a Kano, kuma watakila har a ƙasa baki ɗaya. Game da ADC kuwa, kamar yadda Kwankwaso yake ga NNPP a Kano, yanzu haka shi ne zai zama ADC a jihar.”

ADC na samun ƙarfi gabanin 2027

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya jawo wa ADC canji mai girma awanni kadan bayan ya sauya sheka

Mohammad ya kuma bayyana cewa sauya sheƙar Kwankwaso zuwa ADC na jawo hankalin ‘yan siyasa da dama daga jihohi makwabta, lamarin da ke ƙarfafa jam’iyyar a matakin jiha da na ƙasa.

Ya ce akwai alamun cewa siyasa a Kano za ta ɗauki sabon salo, inda ya ambaci cewa wasu fitattun ‘yan siyasa suna shirin shiga babbar jam'iyyar ADC.

A cewarsa, mutane da dama na ganin Kwankwaso a matsayin shugaba mai tsayawa kan gaskiya kuma mai yanke shawara kai tsaye.

Kwankwasiyya na cewa Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ne jagora a Kano
Rabiu Kwankwaso a wurin zama cikakken ɗan ADC Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Twitter

Haka kuma ya ce akwai ƙaruwa mai yawa na masu rajista a ADC cikin awanni 24 bayan tabbatar da shigowar Kwankwaso, abin da ya nuna yadda jam’iyyar ke ƙara karɓuwa.

Ya ƙara da cewa ana ci gaba da tattaunawa da haɗa kai a jihohin Katsina, Zamfara da Jigawa, inda ƴan Kwankwasiyya da ma wasu da ba su cikinta ba ke shirin shiga ADC domin ganin jam’iyyar ta samu nasara a zaɓen 2027.

Dangane da rade-radin rikici a cikin ADC, Mohammad ya musanta hakan, yana mai cewa jam’iyyar a haɗe, inda ya jaddada cewa ƙarfin Kwankwasiyya ba mutum ɗaya ba ne, akida ce ta talakawa.

Kara karanta wannan

NNPP ta gaza hakura da jagoranta, za ta yi haɗaka da ADC bayan Kwankwaso ya sauya sheka

Sanata Kwankwaso ya kawo wa ADC canji

A baya, mun wallafa cewa ADC ta tsinci dami a kala bayan shigar tsohon Shugaban NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso zuwa jam'iyyar a farkon wannan mako.

Jam'iyyar ta sanar da cewa tun bayan da Kwankwaso ya shige ta aka fara samun tururuwar masu rajista domin zama ƴan ADC domin a shirya tunkarar Bola Tinubu.

A lokacin da ya sauya sheka, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya umarci dukkanin magoya bayansa su koma ADC, kuma sun amsa kira suna tururuwar rajista.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng