Zuwan Kwankwaso ADC Ya Tayar da Magana, Jam’iyyar Ta 'Gano' Shirin APC
- Jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta fara gano wani makarkashiya da gwamnatin APC mai mulki ke yi mata gabanin zaben 2027
- ADC ta zargi gwamnatin APC da yunkurin tarwatsa jam’iyyar bayan sauya sheƙar Rabiu Musa Kwankwaso zuwa cikinta
- Jam’iyyar ta yi alkawarin tinkarar duk wani yunkuri da doka tare da kira ga hukumar INEC ta kasance mai zaman kanta
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Jam’iyyar ADC ta fara tuhumar gwamnatin APC karkashin Bola Tinubu da neman kawo mata cikas a lamuranta yayin da ake shirin zaben shekarar 2027.
ADC ta zargi gwamnatin tarayya karkashin APC da kokarin tarwatsa jam’iyyar bayan sauya sheƙar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso zuwa cikinta.

Source: Twitter
Hakan na cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya sanya wa hannu wanda Tribune ta samu.
Abin da ADC ke zargi game da INEC
Jam’iyyar ta ce gwamnati na kokarin matsa wa shugaban hukumar zabe ta (INEC), Farfesa Joash Ojo Amupitan, domin ya tsoma baki a harkokin shugabancinta.
ADC ta ce wata wasika da wasu manyan lauyoyi suka rubuta ana amfani da ita ne domin tilasta INEC ta soke wasu matakan jam’iyyar kafin kotu ta yanke hukunci.
Jam’iyyar ta bayyana cewa wannan wani babban shiri ne na tarwatsa babbar jam’iyyar adawa da ta rage a kasar, tana mai cewa za ta yi amfani da duk hanyoyin doka domin tinkarar lamarin.
ADC ta bukaci INEC da ta tsaya kan tsarin mulki, ta ki amincewa da duk wani matsin lamba, tare da gudanar da aikinta cikin adalci.

Source: Facebook
ADC ta fadi abin da APC ke tsoro
Sanarwar ta kara da cewa karuwar farin jinin ADC na tayar wa jam’iyyar APC hankali, amma ‘yan Najeriya ba za su bari hakan ya dakatar da su ba a kowane lokaci.
Ta ce:
“Matakin da Rabiu Musa Kwankwaso ya dauka na shiga jam’iyyarmu ya jefa tsoro a zuciyar jam’iyya mai mulki, wanda ya sa manyan jami’an gwamnati ke kara kai hare-hare kanmu.”
Jam’iyyar ta kuma zargi cewa ana amfani da rikicin shari’a wajen matsa wa INEC lamba domin ta dauki bangare, duk da cewa kotu ba ta kammala sauraron karar ba.
A cewarta, babu wani matsin lamba ko rudani da zai dakatar da ci gaban da jam’iyyar ke samu, tana mai cewa ‘yan Najeriya na ci gaba da shiga cikinta yayin da ake gina ingantacciyar adawa a kasar, cewar rahoton Daily Post.
Sakon Kwankwaso ga jama'a bayan shiga ADC
Mun ba ku labarin cewa tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar ADC.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi muhimmin kira ga 'yan Najeriya kan zaben shekarar 2027 da ake tunkara inda ya bayyana muhimmancinsa.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa zaben 2027 yana da muhimmanci matuka saboda haka bai kamata a yi wasa da shi ba.
Asali: Legit.ng

