Kwankwaso Ya Jawo wa ADC Canji Mai Girma Awanni kadan bayan ya Sauya Sheka

Kwankwaso Ya Jawo wa ADC Canji Mai Girma Awanni kadan bayan ya Sauya Sheka

  • ADC ta tsinci dami a kala bayan shigar Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso zuwa jam'iyyar a farkon wannan mako
  • Jam'iyyar ta sanar da cewa tun bayan da Kwankwaso ya shige ta aka fara samun tururuwar masu rajista domin zama ƴan ADC
  • A lokacin da ya sauya sheka, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya umarci dukkanin magoya bayansa su koma ADC

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Jam’iyyar ADC ta fara samun alheri tun bayan da tsohon Gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya koma cikinta.

A wata sanarwa da Sakataren yaɗa jam'iyyar na kasa, Mallam Bolaji Abdullahi ya fitar, ya ce ana ganin amfanin umarnin da Kwankwaso ya ba wa magoya bayansa.

Kara karanta wannan

"Kwankwaso ne mai falle 1": Shugaban hukuma ya yi watsi da tasirin ADC a Kano

Kwankwaso ya kawo wa ADC alheri
Jiga-jigan ADC a yayin tarbar Rabiu Musa Kwankwaso zuwa jam'iyyar Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Twitter

Daily Trust ta wallafa cewa Kwankwaso ya umarci magoya bayansa a fadin kasar su shiga ADC, wani abu da ya haifar da karuwar rajistar ƴan jam'iyya a shafin yanar gizon jam’iyyar cikin sa’o’i 24 kacal.

ADC ta yi maraba da Rabiu Kwankwaso

Daily Post ta wallafa cewa Bolaji Abdullahi ya bayyana shigar Kwankwaso zuwa ADC a matsayin hanyar kawo gagarumin canji.

Sanarwar ta ce: “Jam’iyyar ADC na yi wa tsohon Gwamnan Jihar Kano da dan takarar shugaban kasa a zaben 2023 karkashin NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, maraba a wannan lokaci mai muhimmanci a tafiyar kasarmu."
“Wannan yana nuna karuwar fahimta cewa Najeriya na bukatar sabon shugabanci, kuma lokaci ya yi da shugabanni da ‘yan kasa za su hada kai don samun madadin sahihi da ke sanya mutane a gaba.”

Kwankwaso ya zo wa ADC da alheri

Jam'iyyar ADC ta bayyana cewa a cikin sa'o'i kadan da Kwankwaso ya koma cikinta, an samu karuwar jama'a da ke don a yi tafiyar canji da su.

Kara karanta wannan

NNPP ta gaza hakura da jagoranta, za ta yi haɗaka da ADC bayan Kwankwaso ya sauya sheka

Jama'a na haɓakar tikitin zama ƴan ADC saboda Kwankwaso
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso a yayin da ya yanki tikitin zama dan ADC Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Twitter

Jam'iyyar ta ce:

“Matakin Sanata Kwankwaso ya nuna abin da yawancin ‘yan Najeriya suke ji, cewa kasar na bukatar shugabanci da ya fahimci matsalolin yau da kullum da kuma shirye-shiryen warware su. Kwarewarsa a mulki, alaka mai karfi da talakawa, da ikon kawo mutane tare, Ya sa ya zama ginshikia wannan yunkurin sake gina Najeriya.
“A cikin sa’o’i 24 kacal, shafin yanar gizo na rajistar ADC ya samu karuwar sosai, alamar cewa ‘yan Najeriya da dama suna fara bin sabon tsarin da jam’iyya ke bayarwa. ADC ba kawai jam’iyya bace; hadin kai ne wajen gina kasa mai mutunci da damar rayuwa ga kowa."

ADC: An gano shirin jam'iyyar APC

A wani labarin, mun wallafa cewa jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta fara gano wani makarkashiya da gwamnatin APC mai mulki ke yi mata gabanin zaben 2027.

Jam'iyyar ADC ta zargi gwamnatin APC da yunkurin tarwatsa jam’iyyar bayan sauya sheƙar Rabiu Musa Kwankwaso zuwa cikinta a ranar Litinin, 30 ga watan Maris, 2026.

Jam’iyyar ta yi alkawarin tunkarar duk wani yunkurin kawo mata matsala ta hanyar bin doka tare da kira ga hukumar INEC ta kasance mai zaman kanta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng