APC da ADC Sun Kece Raini yayin da 'Yan Majalisar Tarayya 27 Suka Sauya Sheka
- Majalisar wakilai ta shaida sauya shekar 'yan majalisu 27 zuwa jam'iyyun APC, ADC sakamakon rikicin cikin gida a tsofaffin jam'iyyunsu
- Jam'iyyar APC ta samu karin mambobi 14, ciki har da 'yan majalisu 10 daga jam'iyyar NNPP, wadanda dukka suka fito daga jihar Kano
- Legit Hausa ta tattaro sunayen 'yan majalisun 27 da jam'iyyun da suka koma, yayin da ake tunkarar kakar zabe ta shekarar 2027
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - A wani gagarumin sauyi na siyasa gabanin babban zaɓen 2027, an samu sauya sheƙar ɗumbin ƴan majalisar wakilan Najeriya zuwa jam'iyyun ADC, APC, da sauran su.
Shugaban majalisar, Tajudeen Abbas, ne ya karanta wasiƙun sauya sheƙar ƴan majalisu 27 yayin zaman majalisar, matakin da ake ganin zai sauya taswirar siyasar ƙasar nan.

Source: Facebook
'Yan majalisa 27 sun sauya sheka
Mafi yawan waɗanda suka sauya sheƙar sun bayyana cewa rikicin cikin gida da rarrabuwar kai a tsofaffin jam'iyyunsu ne ya tilasta musu neman mafita, in ji rahoton Channels TV.
Babban abin lura a wannan sauya sheƙar shi ne yadda APC ta samu gagarumar nasara a Kano, inda ƴan majalisu 10 daga jam'iyyar NNPP suka koma cikinta.
Daga cikin waɗanda suka koma APC har da mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar, Aliyu Madaki (Dala) da kuma Tijjani Abdulkadir Jobe (Tofa/Dawakin-Tofa).
Karuwar tagomashi ga jam'iyyar ADC
Jam'iyyar hadakar 'yan adawa ta ADC ta fito a matsayin gidan adawa mai ƙarfi, inda ta karɓi ƴan majalisu takwas daga jam'iyyun PDP da LP.
Daga cikin waɗanda suka shiga ADC har da George Ozodinobi (Anambra) da Abdussamad Dasuki (Sokoto), matakin da ke nuna cewa jam'iyyar tana ƙara samun karɓuwa.
Wannan yana zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi suka fara nuna alamun haɗa kai a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar ta ADC domin fuskantar zaɓen 2027.
Sabon tsarin siyasa a sauran jihohi
Baya ga manyan jam'iyyun biyu, jam'iyyar Accord ta samu ƴan majalisu biyu daga jihar Osun, yayin da sabuwar jam'iyyar APP ta samu ƴan majalisu biyu daga jihohin Imo.
Wani abin mamaki shi ne sauya sheƙar Philip Agbese daga jam'iyyar APC mai mulki zuwa jam'iyyar LP, matakin da ya sa aka rinka tattaunawa a harabar majalisar, in ji rahoton Punch.

Source: Twitter
Jerin 'yan majalisun da suka sauya sheka
Sunayen 'yan majalisa | Tsohuwar jam'iyya | Sabuwar jam'iyya | Mazaba/Jiha | |
1 | Aliu Madaki | NNPP | APC | Dala (Kano) |
2 | George Ozodinobi | LP | ADC | Njikoka/Anaocha/Dunukofia (Anambra) |
3 | Philip Agbese | APC | LP | Ado/Okpokwu/Ogbadibo (Benue) |
4 | Ugochinyere Michael Ikeagwuonu | PDP | APP | Ideato (Imo) |
5 | Abdussamad Dasuki | PDP | ADC | Kebbe/Tambuwal (Sokoto) |
6 | Tijjani Abdulkadir Jobe | NNPP | APC | Tofa/Dawakin-Tofa/Rimingado (Kano) |
7 | Seyi Sowunmi | LP | ADC | Ojo (Lagos) |
8 | Mohammed Bassi | PDP | APC | Mayo Belwa/Ganye/Jada/Toungo (Adamawa) |
9 | Ghali Tijjani Mustapha | NNPP | APC | Ajingi/Albasu/Gaya (Kano) |
10 | Shehu Bello | NNPP | APC | Fagge (Kano) |
11 | Dankawu Idris | NNPP | APC | Kumbotso (Kano) |
12 | Hussain Hassan Shehu | NNPP | APC | Nassarawa (Kano) |
13 | Rabiu Yusuf | NNPP | APC | Sumaila/Takai (Kano) |
14 | Garba Mohammed Chiroma | NNPP | APC | Gezawa/Gabasawa (Kano) |
15 | Ibrahim Mohammed (Kano) | NNPP | APC | Gwale (Kano) |
16 | Jaafaru Yakubu | PDP | APC | Bali/Gassol (Taraba) |
17 | Sadiq Abbas Tafida | PDP | APC | Jalingo/Yorro/Zing (Taraba) |
18 | Ibrahim Mohammed (Kebbi) | PDP | APC | Birnin-Kebbi/Kalgo/Bunza (Kebbi) |
19 | Bello Shinkafi | PDP | APC | Shinkafi/Zurmi (Zamfara) |
20 | Harris Okonkwo | LP | ADC | Idemili ta Arewa/Kudu (Anambra) |
21 | Yaya Bauchi Tongo | PDP | ADC | Gombe/Kwami/Funakaye (Gombe) |
22 | Mustapha Abdullahi | APC | ADC | Ikara/Kubau (Kaduna) |
23 | Mani Maishinko Katami | PDP | ADC | Binji/Silame (Sokoto) |
24 | Umar Yusuf Yabo | PDP | ADC | Yabo/Shagari (Sokoto) |
25 | Nwogu Mathew | LP | APP | Aboh Mbaise/Ngor Okpala (Imo) |
26 | Akanni Clement Ademola | PDP | Accord | Boluwaduro/Ifedayo/Ila (Osun) |
27 | Oladebo Lanre Olomololaye | PDP | Accord | Ayedaade/Irewole/Isokan (Osun) |
'Yan majalisar Kano sun yi taron sirri
A wani labari, mun ruwaito cewa, ‘yan majalisar wakilai daga yankin Kano ta Kudu sun gudanar da abin da suka kira muhimmin taro a ranar Litinin, 30 ga watan Maris, 2026.
Sun zauna ne domin tattauna makomar siyasarsu, yayin da suke bayyana rashin jin dadinsu game da jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Wasu daga cikin wadanda suka halarci taron sun haɗa da manyan ‘yan majalisar wakilai kamar Alhassan Doguwa, Kabiru Rurum, Abdulmumin Jibrin da Abdullahi Rogo.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


