Manyan 'Yan Siyasar Adawa da Suka Je Kano domin Karbar Kwankwaso cikin ADC

Manyan 'Yan Siyasar Adawa da Suka Je Kano domin Karbar Kwankwaso cikin ADC

  • Tsohon ɗan takarar Shugaban ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya fice daga NNPP, ya koma jam’iyyar ADC a hukumance
  • An ba shi katin zama ɗan jam’iyya a Kano, a Gidan Kwankwasiyya a ranar Litinin, 30 ga watan Maris na shekarar 2026
  • Legit ta tattaro fitattun ‘yan siyasa da dama da suka hallara a gidansa domin halartar bikin sauya shekar a jiya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano –Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, zama cikakken ɗan ADC a hukumance.

Kwankwaso, wanda ya taɓa rike mukamin ministan tsaro a Najeriya, ya kammala rajista a sabuwar jam’iyyarsa inda aka karɓe shi tare da ba shi katin zama ɗan jam’iyya.

Kwankwaso ta samu tarbar mutunci zuwa ADC
David Mark, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, Rauf Aregbesola da wasu a yayin da Madugu ya yanki katin ADC Hoton: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Channels TV ta wallafa cewa an gudanar da wannan muhimmin taro ne a Gidan Kwankwasiyya da ke Miller Road a unguwar Bompai, Kano. Matakin na Kwankwaso na zuwa ne a wani lokaci da ake samun sauye-sauyen siyasa a ƙasar, musamman ta fuskar sauya sheka da karban sabuwar shahadar siyasa.

Kara karanta wannan

NNPP ta gaza hakura da jagoranta, za ta yi haɗaka da ADC bayan Kwankwaso ya sauya sheka

Dalilin da ya sa Kwankwaso ya bar NNPP

Jaridar Punch ta ruwaito cewa akwai rikice-rikice da rashin jituwa a cikin NNPP, wanda hakan ya iya taka rawa wajen yanke shawarar ficewar tasa.

Ana ganin cewa komawar Kwankwaso zuwa ADC na iya sauya fasalin siyasar Najeriya, musamman a yankin Arewa, inda yake da tasiri mai ƙarfi.

Kwankwaso ya tara masoya a bikin komawa ADX
Tsohon ɗan takarar Shugaban ƙasa, Rabi'u Musa Kwankwaso yana jawabi a wani taro Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

A yayin wannan sauya sheƙa, an ga ko aka ambaci fitattun ‘yan siyasa da dama da ake alaƙanta su da wannan sabon tafiyar.

Daga cikinsu akwai tsofaffin Ministoci da gwamnoni, yayin da ake da wadanda ke rike da zabbiyar kujera a yanzu.

Wasu wadanda suka karbi Kwankwaso zuwa ADC

Rohoton nan ya tattaro jerin manyan 'yan siyasar da aka gani a gidan Kwankwaso.

Daga cikinsu akwai shugabannin jam'iyyar ADC na kasa baki daya, Sanata David Mark da kuma sakatarensa Rauf Aregbesola.

Haka zalika an ga Peter Obi wanda ya yi wa LP takara a zaben 2023, wasu sun fara rade-radin hada shi a tikiti tare da Rabiu Kwankwaso.

Kara karanta wannan

A karshe: Gawuna ya tafi gidan Kwankwaso zuwa shiga ADC bayan barin APC

  1. Sanata David Mark
  2. Peter Obi
  3. John Odigie-Oyegun
  4. Aminu Tambuwal
  5. Rauf Aregbesola
  6. Emeka Ihedioha
  7. Babachir Lawal
  8. Dr. Mustapha Muhammad
  9. Kashim Ibrahim Imam
  10. Lawal Daura
  11. Ahmad Babba Kaita
  12. Rotimi Amaechi
  13. Sanata Dino Melaye

Wadannan mutane fitattu ne a siyasar Najeriya, wanda ake ganin za su iya kawo gagarumin canji a babban zaben 2027 da ke tunkaro Najeriya.

Jim kadan bayan ya sauya sheka, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya umarci dukkanin magoya bayansa da sauran ƴan Kwankwasiyya da su koma ADC.

Ya bayyana cewa wannan ita ce sabuwar tafiyar da za a kawo canjin da Najeriya ke buƙatar, kuma su tabbata APC ba ta koma mulkin kasar nan ba.

Ɗan Kwankwaso zai koma jam'iyyar ADC

A baya, mun wallafa cewa tsohon Kwamishina a Kano, Mustapha Rabi'u Musa Kwankwaso ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP bayan nazari mai zurfi.

Ya bayyana cewa a yanzu haka yana kan hanyar kammala shigar jam’iyyar hamayya ta ADC domin fara sabuwar tafiyar siyasa a jihar Kano da Najeriya a zaben 2027.

Ya bayyana cewa ADC na da damar kawo sauyi mai ma’ana a Kano da Najeriya bayan mahaifinsa ya koma can, yayin da ake ƙoƙarin haɗe kan yan adawa su fatattaki APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng