A Ƙarshe, Kwankwaso Ya Yanki Katin Zama Ɗan Jam'iyyar ADC, Ya Haɗe da Su Atiku

A Ƙarshe, Kwankwaso Ya Yanki Katin Zama Ɗan Jam'iyyar ADC, Ya Haɗe da Su Atiku

  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi rajistar zama 'dan jam'iyyar ADC a hukumance tare da karbar katin mamba a birnin Kano
  • Manyan 'yan siyasa kamar Peter Obi da David Mark da Aminu Tambuwal sun halarci taron karbar Kwankwaso zuwa jam'iyyar 'yan adawa
  • Tsohon gwamnan ya bayyana cewa ya bar jam'iyyar NNPP ne domin samar da sabon tsarin siyasa da zai tafi da kowa a 2027

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP kuma tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya sauya sheƙa zuwa ADC a hukumance.

Jagoran na Kwankwasiyya ya kammala rajista tare da karɓar katin zama mamba na ADC a yau Litinin, a wani gagarumin taro da aka gudanar a gidan Kwankwasiyya dake Miller Road a birnin Kano.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Uban NNPP ya yi magana mai zafi kan ficewar Kwankwaso daga jam'iyya

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya shiga jam'iyyar ADC a hukumance.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso rike da katinsa na zama cikakken dan jam'iyyar ADC. Hoto: @KwankwasoRM
Source: Twitter

Kwankwaso ya shiga ADC a hukumance

Wannan mataki ya biyo bayan sanarwar murabus ɗinsa daga NNPP a ranar Lahadi, inda ya bayyana buƙatar sauya fasalin siyasa domin fuskantar zaben 2027, in ji rahoton Punch.

Taron karɓar Kwankwaso ya samu halartar manyan jigajigan siyasar Najeriya daga jam'iyyu daban-daban, ciki har da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar LP, Peter Obi.

Sauran waɗanda suka halarta sun haɗa da shugaban jam'iyyar ADC na ƙasa David Mark, Sanata Aminu Tambuwal, Rotimi Amaechi, Sanata Dino Melaye, da kuma tsohon shugaban APC John Odigie-Oyegun.

Kasancewar waɗannan manyan fuskoki ya nuna cewa ana ƙoƙarin kafa wani gagarumin kawance na siyasa dake hararar babban zaɓen shekarar 2027 dake tafe a faɗin ƙasar nan.

Dalilin Kwankwaso na barin ADC

Sanata Kwankwaso ya bayyana cewa ficewa daga NNPP ba abu ne mai sauƙi a gare shi ba, duba da irin lokacin da ya ɗauka yana gina jam'iyyar a matsayinsa na mamba na gari.

Kara karanta wannan

Jerin manyan Najeriya da suka halarci jana'izar mamar El Rufa'i

Ya bayyana cewa:

"Ganin yadda yanayin siyasar ƙasar nan yake a halin yanzu, wanda ke buƙatar sabon tsari na bai ɗaya, na ga ya dace in shiga wani dandali da zai ba mu damar kawo canji."

Kwankwaso ya gode wa shugabancin jam'iyyar NNPP ƙarƙashin Ajuji Ahmed, sannan ya jinjina wa 'yan Kwankwasiyya bisa jajircewarsu wajen bin umarninsa na siyasa.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bukaci dukkan 'yan Kwankwasiyya su shiga jam'iyyar ADC.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yana sa hannu a rajistar zama dan jam'iyyar ADC. Hoto: @KwankwasoRM
Source: Twitter

Makomar tafiyar Kwankwasiyya a ADC

Tsohon ministan tsaron ya tabbatar wa magoya bayansa cewa wannan sauya sheƙar za ta buɗe wani sabon babi na ci gaba da kuma samar da wadata ga daukacin 'yan Najeriya, in ji rahoton Vanguard.

Ya bayyana cewa:

"Za mu ci gaba da haɗa kai da yin aiki tare domin tsara kyakkyawar makoma mai fa'ida ga ƙasarmu, wadda kowa zai yi alfahari da ita."

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun kai mummunan hari Filato, an kashe Musulmai da Kirista

Sanarwar ta ƙara da cewa an umarci daukacin mambobin Kwankwasiyya da su bi sahu wajen yin rajista da jam'iyyar ADC a mazaɓunsu domin ƙarfafa sabuwar tafiyar.

Wannan mataki ya janyo ce-ce-ku-ce a duniyar siyasa, inda ake ganin cewa haɗewar Kwankwaso da Peter Obi a jam'iyya ɗaya za ta iya zama babban ƙalubale ga jam'iyyar APC mai mulki.

Uban NNPP ya magantu kan Kwankwaso

A wani labari, mun ruwaito cewa, wanda ya kafa NNPP, Boniface Aniebonam, ya bayyana matsayarsa bayan ficewar Sanata Rabiu Kwankwaso daga jam’iyyar.

Boniface Aniebonam ya tabbatarwa 'yan Najeriya cewa mambobin NNPP ba sa cikin shirin komawa sabuwar jam’iyyar da Kwankwaso ya nufa.

Ya ce yanzu jam’iyyar ta fara tuntubar 'ya'yanta a duka sassan kasar nan domin fara shirye-shiryen zaben 2027, inda ya ce duk masu neman takara za su bi tsarin zaben fitar da gwani.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com