2027: Hadimin Buhari Ya Rabu da APC, Ya Koma Jam'iyyar Hamayya a Kano

2027: Hadimin Buhari Ya Rabu da APC, Ya Koma Jam'iyyar Hamayya a Kano

  • Nasiru Saidu Adhama, hadimin tsohon Shugaban kasa, marigayi Muhammadu Buhari sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC
  • Nasiru Saidu Adhama ya ce dole ce ta da ya hakura da APC ganinncewa su ne suka yi tsayin daka don tabbatar da kafuwarta a Kano
  • Daga cikin matsalolin, ya ce a halinda ake ciki, jam’iyyar APC mai mulki ta kauce daga manufofin ci gaba da aka kafa ta a kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Tsohon jigo a jam’iyyar APC a jihar Kano, Nasir Saidu Adhama, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar saboda wasu dalilai.

Ya sanar da cewa daga yanzu ya sauya sheka zuwa jam'iyyar hamayya ta ADC, yana mai cewa matakin ya biyo bayan sauyin yanayin siyasa da kuma sabbin tunani.

Kara karanta wannan

A karshe, Kwankwaso ya yi murabus daga NNPP, ya jero manyan dalilan barinta

Nasiru Sa'idu Adhama ya koma ADC
Tsohon hadin Buhari da ya koma ADC tare da alamar jam'iyya a dama Hoto: Nasir Sa'idu Adhama
Source: Facebook

A cikin sanarwar da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Nasiru Sa'idu Adhama ya ce yana daga cikin kusoshin da suka yi tsayin daka aka kafa APC a baya.

Hadimin Buhari ya koma ADC

A cikin sanarwar, Nasiru Saidu Adhama ya bayyana cewa sai da ya zauna da masoya, magoya baya da abokan siyasa kafin ya amince da barin APC.

Ya ce:

"Ina sanar da ficewata daga jam’iyyar APC nan take, cikin godiya da girmamawa ga irin gudunmawar da muka bayar a baya.”
Nasir Adhama ya koma ADC saboda APC ta sauka daga layi
Taswirar jihar Kano inda hadimin Buhari ya koma ADC Hoto: Legit.ng
Source: Original

Adhama ya bayyana cewa dangantakarsa da APC ta samo asali ne tun daga kafuwarta, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen ginata da bunkasa ta a Kano da ma kasa baki ɗaya.

Ya ce ya kasance cikin mambobin farko da suka kafa tubalin jam’iyyar, inda ya zama ɗaya daga cikin wakilan jam’iyyar CPC biyu da aka nada a kwamitin wucin gadi na farko a Kano.

Kara karanta wannan

An rage mugun iri: Cikin jimami, ISWAP ta sanar da mutuwar babban kwamandanta

Mukaman da Adhama ya riƙe a APC

Nasiru Saidu Adhama rike mukamin sakataren jin daɗin jama’a na mataimaki na farko a APC a Kano, sannan daga bisani ya zama mai ba tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara na musamman.

Ya kara da cewa:

"Ina alfahari da irin rawar da muka taka wajen samun nasarar zaben shugaban kasa na 2015 wanda ya sauya akalar dimokuradiyyar Najeriya.”

Sai dai ya ce a yanzu ya lura cewa jam’iyyar APC ta fara kaucewa manufofin da aka kafa ta a kai

A cewarsa: ko

"APC ta fara karkata daga manufofin ci gaba da hadin kai da suka jawo kafa ta, tana kuma kara karkata zuwa wasu bukatu da ba su dace da burin farko ba.”

Adhama ya bayyana cewa bayan tuntubar masu ruwa da tsaki, ya yanke shawarar shiga sabuwar tafiya ta siyasa wacce za ta ba shi damar ci gaba da hidima cikin gaskiya da nagarta.

Ya ce:

“Na yanke shawarar komawa jam’iyyar ADC, wacce manufofinta suka dace da kudirina na shugabanci mai gaskiya, adalci da ci gaban kasa.”

Kara karanta wannan

Tinubu ya cika shekaru 74 a duniya, ya aika muhimmin sako ga 'yan Najeriya

Ya kuma bayyana cewa an riga an ba shi mukami a cikin kwamitin rikon kwarya na shugabancin ADC a Kano, wanda ya karɓa da tawali’u.

Adhama ya jaddada cewa wannan sauyi ba ya nufin barin hidimar jama’a ba ne, illa dai ci gaba da ita ta wata hanya

Ya kuma gode wa magoya bayansa da abokan aikinsa bisa goyon baya da suka ba shi, yana mai fatan ci gaba da hadin kai a sabuwar tafiya.

ADC ta magantu kan sauya sheka

Mai magana da yawun jam’iyyar ADC a Kano, Sa’idu Bello, ya shaida wa Legit cewa yawaitar sauya sheƙar ‘yan siyasa na faruwa ne sakamakon rashin dimokuraɗiyya a cikin jam’iyyun siyasa.

Ya ce sauya sheƙar ‘yan siyasa ta zama tamkar wata guguwa a dimokuraɗiyyar Najeriya saboda matsalolin da suka dabaibaye siyasar jam’iyyun ƙasar.

A cewarsa, da dama daga cikin ‘yan siyasa na barin jam’iyyunsu ne idan ba a ba su dama ko an tauye muradunsu ba.

Ya kara da cewa rikice-rikicen cikin gida da rashin adalci sun raunana manyan jam’iyyu tsawon lokaci.

Kwankwaso zai koma ADC

Kara karanta wannan

APC ta yi babban rashi, manyan wakilan jam'iyyar 3 sun mutu a hatsarin mota

A baya, mun wallafa cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kammala shirye-shiryen komawa jam'iyyar ADC domin fuskantar zaben shekarar 2027 mai zuwa.

Kakakin kungiyar Kwankwasiyya ya bayyana cewa jagoran nasu ya fice daga jam'iyyar NNPP a hukumance a gidansa na Miller Road kuma an saka ranar komawa ADC.

An ba dukkan mambobin Kwankwasiyya umarnin gaggawa na su garzaya mazabunsu domin yin rajista da jam'iyyar hamayya da ke tashe a yanzu, wato ADC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng