Asiri Ya Tonu: An Gano Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa da PDP Za Ta Marawa baya a 2027

Asiri Ya Tonu: An Gano Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa da PDP Za Ta Marawa baya a 2027

  • Ministan Abuja, Nyesom Wike ya tabbatar da cewa zai marawa Shugaba Bola Tinubu baya domin sake cin zaben 2027
  • Wani tsage na jam'iyyar PDP mai biyayya ga Wike ya fara kulla kawancen "Rainbow Coalition" domin hada kan mambobin APC da na PDP
  • Gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde ya nuna rashin amincewarsa da wannan mataki inda ya ce ba zai taba marawa Shugaba Tinubu baya ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Ministan babban birnin tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya fito fili ya bayyana cewa zai marawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya domin sake cin zaɓe a shekarar 2027.

Wannan mataki da Wike ya dauka, ya janyo rarrabuwar kawuna a jam'iyyar PDP, kasancewar akwai tsagin da ke goyon bayansa tun asali, da kuma wadanda ke adawa da shi.

Kara karanta wannan

Wike ka iya bijirewa Tinubu a 2027, ya fadi abin mamaki da PDP za ta yi

Ana zargin tsagin PDP zai goyi bayan Tinubu a 2027
Shugaba Bola Tinubu ya gana da Wike da tsofaffin gwamnonin PDP. Hoto: @OlayinkaLere
Source: Twitter

Tsagin PDP zai goyi bayan Tinubu a 2027

Wani bincike da sashen siyasa na jaridar BusinessDay ya gudanar ya nuna cewa tsagin PDP dake biyayya ga Wike ya fara shirin dakile duk wani ɗan takarar adawa don marawa Tinubu baya.

Wike, wanda babban ɗan PDP ne dake aiki a gwamnatin APC, ya jaddada cewa goyon bayansa ga Tinubu zai dore har zuwa shekarar 2031 mai zuwa.

Majiyoyi na kusa da ministan sun tabbatar da cewa magoya bayansa sun fara kafa rassan ƙungiyar "Rainbow Coalition" a jihar Rivers domin yaƙin neman zaɓen.

Wannan ƙungiya tana haɗa magoya bayan PDP da na APC wuri guda domin tabbatar da cewa Tinubu ya samu gagarumar nasara a zaɓe mai zuwa yau.

Tsagin na Wike ya riga ya tsayar da ranar 25 ga Mayu, 2027 domin gudanar da zaɓen fitar da gwani na waɗanda za su fafata a zaɓukan da ke tafe.

Kara karanta wannan

Ja'oji: Ana tsakiyar taron APC, 1 daga cikin manyan hadiman Tinubu ya yi murabus

Rikicin cikin gida a jam'iyyar PDP

Wannan mataki na Wike ya haifar da gagarumin rarrabuwar kawuna a cikin jam'iyyar PDP, inda sauran shugabannin jam'iyyar suka nuna rashin amincewarsu da hakan.

Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana cewa kodayake Wike yana da damar zaɓar wanda yake so, amma shi ba zai taɓa goyon bayan Tinubu ba.

Ana zargin cewa babban burin Wike shi ne ya dakile jam'iyyar PDP ta yadda ba za ta iya tsayar da wani ɗan takara mai ƙarfi ba, in ji rahoton The Cable.

An ce tsagin Tinubu sun sha alwashin dakile PDP daga fitar da d'an takara mai karfi a 2027.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Nyesom Wike wajen kaddamar da wasu ayyuka a Abuja. Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Source: Facebook

Dabarun siyasar tsagin Nyesom Wike

Tsagin Wike yana amfani da kotuna wajen tabbatar da ikonsa a kan shugabancin jam'iyyar PDP domin dakile tasirin shugabannin jam'iyyar dake Arewacin ƙasar.

Wannan dabarar tana nufin tura jam'iyyar PDP cikin rikici ta yadda ba za ta iya kalubalantar Shugaba Tinubu ba lokacin da zaɓen 2027 ya ƙataro.

A halin yanzu, an fara tsare-tsare na haɗin gwiwa tsakanin jam'iyyar APC da tsagin na Wike a jihohi daban-daban domin tunkarar babban zaɓen ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Aminu Gwarzo: "Abin da yasa na hakura da kujerar Mataimakin gwamnan Kano"

Wike ya hango makomar PDP a 2027

A wani labari, mun ruwaito cewa, ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana tasirin da jam'iyyar PDP mai adawa za ta yi a zaben 2027.

Wike ya bayyana cewa taron kasa na jam’iyyar da aka shirya ranar 29 da 30 ga watan Maris, 2026 zai gudana kamar yadda aka tsara.

Ya kuma bayyana cewa PDP za ta bai wa ‘yan Najeriya mamaki a zaben 2027, yana mai cewa jam’iyyar za ta nuna karfinta a zaben mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com