Aminu Gwarzo: "Abin da Ya sa na Hakura da Kujerar Mataimakin Gwamnan Kano"
- Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu AbdusSalam ya bayyana dalilan da suka jawo ya yi murabus daga mukaminsa
- Ya jaddada cewa ya yi murabus ne da son ransa ba tare da an yi masa tilas ba bayan ya yi dogon nazari a kan lamarin
- An samu karin bayanin ne awanni kaɗan da ƙungiyar Kwankwasiyya ta sanar da cewa Mataimakin gwamnan ya yi murabus
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano –Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu AbdusSalam Gwarzo, ya bayyana cewa dalilin da ya sa ya yi murabus daga mukaminsa na neman zaman lafiya ne.
Ya ce ya yanke shawarar ya ajiye mukaminsa ne domin tabbatar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da kuma gudanar da mulki a cikin sauƙi a jihar.

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa ya bayyana hakanne a cikin wata wasika mai dauke da kwanan wata 27 ga Maris, 2026, wacce ya aike wa gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf.
Yadda Mataimakin gwamnan Kano ya yi murabus
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Aminu AbdusSalam Gwarzo ya ce ya dauki matakin ne da kansa kuma da niyya mai kyau don Kanawa su amfana.
Ya ce:
“Na dauki wannan mataki ne a cikin kwarewa domin bai wa gwamnati damar ci gaba ba tare da wata tangarda ko hayaniya ba.”
Gwarzo ya kara da cewa shawarar ta biyo bayan tuntuba mai fadi da kuma zurfin nazari kan halin siyasar da ake ciki a jihar a wannan lokaci.
A cewarsa, bai kamata a fassara murabus dinsa a matsayin amincewa da wani kuskure ko laifi ba, illa dai mataki ne na kare martabar hukumomi da dimokuradiyya.
Ya ce:
“Na yi wannan murabus ne da son rai, kuma bai kamata a dauke shi a matsayin amincewa da wani laifi ba, sai dai a fahimce shi a matsayin mataki domin hidimar jama’a."
Doka ta goyi bayan murabus dina – Gwarzo
Aminu AbdusSalam Gwarzo ya jingina murabus dinsa da tanadin Sashe na 306(2) na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima).

Source: Twitter
Wannan sashe ya bayar da dama ga masu rike da mukaman gwamnati su sauka daga mukamansu idan sun ga dama ba tare da wata tangarda ba.
Ya kuma yi godiyarsa ga al’ummar jihar Kano bisa damar da suka ba shi na yi musu hidima na tsawon lokacin nan.
Haka zalika, ya gode wa gwamnan jihar, majalisar zartarwa, ‘yan majalisar dokoki, jam’iyyar NNPP, sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki bisa goyon bayan da suka ba shi a lokacin da yake kan mukami.
Murabus din na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da takaddama ta siyasa da kuma shari’a kan kujerar mataimakin gwamna a jihar. har aka fara batun tsige shi.
Mataimakin Gwamnan Kano ya yi murabus
A baya, kun ji cewa Mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdussalam ya yi murabus daga mukaminsa a ranar Juma'a, 27 ga watan Maris, na shekarar 2026.
Kwankwasiyya ta bayyana cewa Aminu Gwarzo ya yi murabus ne bisa kishin kasa, da son wanzar da zaman lafiya a Kano da bayar da damar yinsa mutanen Kano aiki.
Haka kuma Aminu AbdusSalam Gwarzo ya yi martani ga yunkurin da majalisar dokokin jihar ta fara na tsige shi, yana mai cewa bai aikata laifin komai ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


