Shirin Kifar da Tinubu: Kwankwaso Ya Gana da Manyan Jam'iyyar ADC a Abuja
- Yayin da rade-radin sauya shekar Sanata Rabiu Kwankwaso ke kara karfi, jagoran NNPP ya gana da wasu shugabannin ADC a Abuja
- Tsohon gwamnan jihar Osun kuma sakataren jam'iyyar ADC na kasa, Rauf Aregbesola ya ziyarci Sanata Rabiu Kwankwaso a gidan shi
- Baya ga haka, wasu shugabannin jam'iyyar ADC a jihar Kano sun gana da Rabiu Musa Kwankwaso domin tattauna lamuran siyasa
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Yayin da zaben 2027 ke kara karatowa, Rabiu Musa Kwankwaso ya gana da Rauf Aregbesola da shugabannin ADC a Abuja
Hakan na zuwa ne yayin da ake rade-radin cewa Sanata Rabiu Kwankwaso zai fita daga NNPP zuwa jam'iyyar hadakar 'yan adawa ta ADC.

Source: Facebook
Legit Hausa ta gano cewa Sanata Rabiu Kwankwaso ya wallafa sako game da ganawar shi da Rauf Aregbesola a shafin shi na Facebook.

Kara karanta wannan
Tinubu: Arewa ta Tsakiya ta gama shiri, ta fitar da 'dan takarar Shugaban kasa a 2027
Kwankwaso ya hadu da Aregbesola
Jagoran tafiyar Kwankwasiyya a Najeriya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya sanar da ganawar shi da sakararen jam'iyyar ADC, Rauf Aregbesola.
Bayan ganawarsu, Kwankwaso ya ce:
"Na ji daɗin karɓar baƙuncin tsohon gwamnan jihar Osun kuma sakataren jam'iyyar ADC na kasa, Rauf Aregbesola, a gidana da ke Abuja."
Duk da Kwankwaso bai yi karin bayani game da abubuwan da suka tattauna ba, ana hasashen ganawarsu na da nasaba da shirin shigarsa ADC.
Wata ganawar Kwankwaso/Aregbe
A watan Fabrairun 2025 ma dai Kwankwaso ya gana da Aregbesola a wani zama na sirri a gidansa da ke Lagos. Sai dai a lokacin ma ba a bayyana cikakken abin da suka tattauna ba.
Punch ta wallafa cewa majiyoyi daga reshen NNPP na jihar Osun, waɗanda suka nemi a ɓoye sunansu, sun ce tattaunawar ta shafi batutuwan siyasar ƙasa.
Manyan ADC sun gana da Kwankwaso
Haka kuma, a ranar Alhamis, 26 ga Maris, 2026, Rabiu Kwankwaso ya karɓi shugabannin ADC na jihar Kano a birnin tarayya Abuja.
Hadimin Kwankwaso, Saifullahi Hassan ya wallafa a Facebook cewa 'yan ADC sun ziyarci Kwankwaso ne ƙarƙashin jagorancin shugaban jam'iyyar, Musa Shuaibu Ungogo.

Source: Facebook
Kwankwaso na tattaunawa da ADC
A gefe guda kuma, ƙungiyar Kwankwasiyya ta tabbatar da cewa Kwankwaso na tattaunawa da jam’iyyun adawa na ADC da NDC.
Daily Trust ta wallafa cewa daya daga cikin masu magana da yawun ƙungiyar, Mansur Kurugu, ya tabbatar da hakan, yana mai cewa tattaunawar na iya kaiwa ga haɗa kai tsakanin jam’iyyun.
Ya ƙara da cewa har yanzu ba a yanke hukunci kan jam’iyyar da za a zaɓa a ƙarshe ba, yana mai jaddada cewa tattaunawar na ci gaba.
Madugun Kwankwasiyya ya yabi Gawuna
A wani labarin, kun ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yabawa dan takarar gwamna karkashin APC a zaben 2023 a Kano.
Kwankwaso ya bayyana cewa Nasiru Yusuf Gawuna yana cikin kwamishinoninsa masu daraja kuma bai taba masa kalamman batanci ba.
Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da rade-radin cewa Gawuna zai koma tafiyar Kwankwasiyya yayin da Abba Kabir ya koma APC.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
