Akpabio Ya Fadi Sabuwar Jihar da Za a Kirkira, Ya Bayyana Babban Birninta

Akpabio Ya Fadi Sabuwar Jihar da Za a Kirkira, Ya Bayyana Babban Birninta

  • Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya yi magana game da kirkirar sabuwar jiha a Najeriya domin kawo ci gaba
  • Ya bayyana cewa gwamnatin Bola Tinubu na goyon bayan shirin kirkirar sabuwar jihar wanda za ta kasance mai muhimmanci a Kudancin kasar
  • Akpabio ya ce idan an kirkiri jihar Anioma, Warri zai zama babban birnin sabuwar jihar Delta yayin da aka zabi babban birnin sabuwar jihar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Asaba, Delta - Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya sake jaddada cewa akwai cikakken goyon bayan majalisa da siyasa wajen kirkirar jiha a Najeriya.

Akpabio ya bayyana shirin majalisar dattawa na tabbatar da kirkirar jihar Anioma a Kudancin Najeriya domin kara samun ci gaba a yankin.

Akpabio ya magantu kan sabuwar jiha da za a kirkira a Najeriya
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio yayin zaman mambobinta. Hoto: The Nigeria Senate.
Source: Facebook

Akpabio ya magantu kan kirkirar sabuwar jiha

Akpabio ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga ‘yan jam’iyya a taron yankin kudu maso kudu na jam’iyyar APC da aka gudanar a Asaba, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Ana rade radin Sheikh Khalifa Zariya ya rasu, Atiku ya yi magana

Ya ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na nan daram wajen tabbatar da wannan shiri ya tabbata.

Akpabio ya kuma bayyana cewa idan aka kirkiri jihar Anioma, birnin Warri zai zama babban birnin jihar Delta.

Ya ce Warri na da muhimman ababen more rayuwa kamar filin jirgin sama, ofisoshin gwamnati, kamfanonin mai, tashar jiragen ruwa da kuma filin wasa.

Gwamnonin jihohin Delta, Edo, Bayelsa, Akwa Ibom, Rivers da Cross River sun halarci taron tare da sauran shugabannin siyasa daga yankin.

Akpabio ya ce bukatar kirkirar jihar Anioma na da tushe mai karfi tun tarihi, yana mai cewa hakan zai kawo daidaito, ingantaccen shugabanci da ci gaba mai dorewa.

Ya kara da cewa shirin, wanda Sanata Ned Nwoko ke jagoranta, na ci gaba da samun kulawar majalisa.

An fadi sabon birni da za a ba sabuwar jiha da za a kirkira
Taswirar jihar Delta da za a kirkiri jiha a cikinta. Hoto: Legit.
Source: Original

Manyan abubuwa muhimmai a gaban majalisar dattawa

A cewarsa, kirkirar jihar Anioma na daga cikin manyan abubuwan da Majalisar Dattawa ta 10 ke bai wa muhimmanci, tare da amfanin tattalin arziki da na shugabanci.

Ya bayyana cewa hakan zai raba jihar Delta gida biyu domin inganta gudanarwa da kawo ci gaba a yankin.

Kara karanta wannan

Yakin Iran da abubuwan da suka jawo karancin lantarki a Najeriya

“Anioma za ta zama jiha, tare da Asaba a matsayin babban birni. Majalisar dattawa na goyon bayan wannan shiri.
“Da zarar an mayar da Asaba babban birnin Anioma, Warri zai zama babban birnin sabuwar Delta.”

Akpabio ya bukaci masu ruwa da tsaki su mara wa manufofin Tinubu baya, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen bunkasa kasa da hadin kai, cewar Leadership.

A watan Nuwamban 2025, Sanata Ned Nwoko ya ce yunkurin kirkirar jihar Anioma na samun gagarumar nasara tare da goyon bayan kwamitocin gyaran kundin tsarin mulki da kuma gwamnatin Tinubu.

Ya kuma bayyana cewa sanatoci 97 sun sanya hannu a takardar goyon bayan shirin, yana mai cewa wannan goyon baya ba a taba ganin irinsa ba.

Sabuwar jiha: Tinubu ya ba da hadin kai

An ji cewa majiyoyi sun nuna cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da kirkiro jiha daya a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.

An ce majiyoyi daga fadar shugaban kasa ne suka bayyana hakan, sun ce Tinubu na duba yiwuwar share hawayen inyamurai.

Rahotanni suka ce Tinubu ya fi aminta da kafa jihar Anioma, wacce Sanata Ned Nwoko na jihar Delta ke jagorantar fafutukar samar da ita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.