Mataimakin Gwamnan Kano Ya Ga Ta Kansa, Kotu Ta Shure Rokon Hana Majalisa Ta Tsige Shi
- Mataimakin gwamnan Kano Kwamred Aminu AbdulSalam Gwarzo ya samu matsala a fafatawarsa da majalisar dokokin jiha
- A kwanakin baya, majalisar dokokin Kano ta sanar da shirin fara tsige Mataimakin gwamnan bisa wasu zarge-zarge
- Lamarin ya tilasta wa Kwamred Aminu AbdulSalam Gwarzo garzaya wa kotu domin neman a taka wa majalisa birki
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta yi kwarya-kwayan hukunci a kan bukatar da mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya shigar gabanta.
Mataimakin gwamnan ya kai kara gaban kotu domin dakatar da shirin tsige shi daga mukaminsa da aish ke yi.

Source: Facebook
Jaridar The Guardian ta wallafa cewa lauyansa, Barista Umar Danbaito, ne ya shigar da ƙarar ta gaggawa inda ya roƙi kotu da ta bayar da umarnin wucin gadi domin dakatar da yunkurin.
Korafin da Mataimakin gwamnan Kano ya kai kotu
Jaridar Daily Post ta wallafa cewa Kwamred Aminu AbdulSalam Gwarzo ya kuma buƙaci a dakatar da shirin tsige shi har sai an saurari ƙarar farko da aka shigar a gaban wannan kotu.
Sai dai a hukuncin da ya yanke, Mai Shari’a S.M. Shaibu ya bayyana cewa mai ƙara bai cika sharuddan da ake buƙata domin samun irin wannan umarni na wucin gadi ba.
Wannan al'amari ya jawo ta ki amincewa da bukatar Mataimakin gwamnan na neman a hana majalisa ta raba shi da kujerarsa.
Duk da haka, kotun ta umarci mai ƙarar da ya miƙa takardun ƙorafinsa ga waɗanda ake ƙara domin su samu damar mayar da martani yadda ya kamata.
An dage shari'ar Mataimakin gwamnan Kano
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta riga ta bai wa mataimakin gwamnan takardar sanarwar tsige shi, bayan zarginsa da aikata rashawa da kuma amfani da ofis ba bisa ƙa’ida ba.

Kara karanta wannan
Bayan fiye da shekara 1, gwamnatin Kano ta waiwayi iyalan mafarautan da aka kashe a Uromi
An ba shi wa’adin makonni biyu domin ya kare kansa daga waɗannan zarge-zarge ko kuma ya fuskanci shirin tsige wa daga majalisa.

Source: Facebook
Akalla ‘yan majalisa 38 na jam’iyyar APC ne suka sanya hannu kan wannan mataki, karkashin jagorancin shugaban masu rinjaye na majalisar, Hon. Lawan Husaini mai wakiltar mazabar Dala.
Haka kuma, wasu ‘yan majalisa biyu daga jam’iyyar NNPP sun nuna goyon baya ga matakin.
Daga cikin manyan zarge-zargen da ake yi masa akwai karɓar cin hanci daga ƙananan hukumomi 44 na jihar tsakanin Yuni 2023 zuwa Janairu 2024.
An ce yana karɓar kimanin Naira miliyan 1.5 daga kowace ƙaramar hukuma a kowane wata, wanda ya kai kusan naira miliyan 66 a wata, da jimillar Naira miliyan 462 a cikin watanni bakwai.
Haka kuma, ana zargin cewa tsakanin Fabrairu zuwa Yuli 2024, ya sake karɓar wasu kuɗi da suka kai Naira miliyan 726, da sunan gudanar da wasu ayyuka na musamman ga ƙananan hukumomi.
Tuni dai ya kalubalanci shirin da 'yan majalisa ake yi na tsige shi matukar ya gaza kare kansa yadda ya dace, amma kotu ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 16 ga Afrilu, 2026.
Kano: Tsohon Mataimakin gwamna ya gigita APC
A baya, mun wallafa cewa tsohon dan takarar Gwamnan Kano Nasiru Yusuf Gawuna ya fara tayar wa da hankalin APC a matakin kasa a kan kusancinsa da Kwankwasiyya.
Rahotanni 'yan kwanakin nan sun fara nuna yadda Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da Gawuna ke 'dasawa sosai, musamman bayan gwamna Abba Kabir Yusuf ya bar NNPP.
Sai dai Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya shiga ya fara neman hana 'kara karfin alaka a tsakanin Kwankwaso da Gawuna, kuma ya tayar da tawaga domin a rarrashe shi.
Asali: Legit.ng

