Yadda Aka Cafke Matashi saboda Fada wa Gwamna Bago 'Gaskiya' yayin Taro a Niger
- Rundunar yan sanda a Niger ta yi magana kan cafke wani mutum mai suna Hamisu Abdullahi mai shekaru 38
- Majiyoyi sun ce matashin ya shiga hannu bayan ya yi ihu “ba ruwa, ba wuta” lokacin ziyarar gwamnan Niger a Suleja
- ‘Yan sanda sun ce an kama shi ne bisa zargin tayar da hankali da kuma kokarin hana ayyukan gwamnati gudana
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Suleja, Niger - Rundunar yan sanda a Niger ta tabbatar da cafke wani mutum mai shekaru 38 mai suna Hamisu Abdullahi bayan ya yi ihu “ba ruwa, ba wuta”
Lamarin ya faru ne yayin da gwamna Mohammed Umaru Bago ya kai ziyara ga Sarkin Suleja bayan sallar idi a ranar Juma’a da ta gabata.

Source: Twitter
Dalilin yan sanda na cafke matashi a Niger
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, SP Wasiu Abiodun, ya ce an kama wadanda ake zargin ne saboda kokarin tayar da hankali, cewar Daily Trust.
Ya kara da cewa an mayar da shi zuwa sashen binciken manyan laifuka na jihar da ke Minna a ranar 20 ga watan Maris, 2026 domin ci gaba da bincike.
A cewarsa, ana zargin mutumin da aikata ta’addanci da kuma kokarin hana gudanar da ayyukan Gwamna Bago yayin ziyarar Sallah ta gwamnan.
Sai dai daga baya jami’an tsaro sun bayar da belinsa yayin da bincike ke gudana kan abin da ya faru a fadar Sarkin Suleja.
Dan uwansa, Haruna Abdullahi, ya tabbatar da cewa an sako shi a ranar Talata 25 ga watan Maris, 2026 a yamma bayan ya shafe kwanaki biyar a tsare.

Source: Original
Yadda aka kama matashin a fadar Sarki
Rahotanni sun ce an kama Hamisu ne a fadar Sarkin Suleja bayan ya yi ihu kan matsalar rashin ruwa da wutar lantarki a yankin.
An kuma samu rade-radin cewa kama shi ya biyo bayan umarnin gwamnan, amma ba a tabbatar da wannan zargi ba daga wata majiya mai zaman kanta.

Kara karanta wannan
Yayin da Amurka ke ikirarin tattaunawa, Iran ta yi wa Isra'ila illa da makamai masu linzami
Lokacin da aka tuntubi mai bai wa gwamnan shawara kan harkokin yada labarai, Bologi Ibrahim, ya ce bai da masaniya kan faruwar lamarin.
A wani bangare kuma, 'International Press Institute Najeriya' ta bukaci Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gargadi Gwamnan jihar Niger, cewar Sahara Reporters.
Kungiyar ta bayyana cewa wasu matakan da gwamnati ke dauka na iya tauye ‘yancin ‘yan jarida da kafafen yada labarai wajen gudanar da aikinsu yadda ya kamata.
Sanarwar da shugabannin kungiyar suka fitar ta ce dole ne a kare ‘yancin fadin albarkacin baki da aikin jarida a fadin jihar da kasa baki daya.
An yi wa Gwamna Fintiri ihu
Mun ba ku labarin cewa wasu matasa sun fusata Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri a Ganye, Adamawa, yayin taron neman goyon bayan PDP, lamarin da ya jawo maganganu.
A cikin bidiyon, an ji matasa suna ihu “ba mu yi” yayin jawabin gwamnan, abin da ya sa Fintiri ya dakata kuma ya mayar masu da martani cikin fushi.
Gwamna Fintiri ya kalubalanci masu adawa da shi kan zabe, yana mai cewa su tsayar da dan takara, shi ma ya tsayar, a ga wanda zai ci zabe.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
