'Falle 1 ce,' Shirin da Kwankwaso Ya Fara Yi na Kifar da Gwamnatin Abba a 2027

'Falle 1 ce,' Shirin da Kwankwaso Ya Fara Yi na Kifar da Gwamnatin Abba a 2027

  • Sanata Rabiu Kwankwaso ya sake caccakar Gwamna Abba Yusuf kan butulce masa da ya yi bayan ya bar jam'iyyar NNPP ya koma APC gabanin 2027
  • Kwankwaso ya bayyana cewa matakin sauya shekar gwamnan tamkar mutum ne ya dabawa kansa wuka, inda ya kira matakin da 'juyin kwakwalwa'
  • Jagoran Kwankwasiyyar ya jaddada cewa Allah SWT ba zai bar wadanda suka ci amana ba, yayin da yake jaddada taken "falle daya ce" ga Abba a Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kano - A yayin da siyasar 2027 ke ci gaba da karatowa, kallo ya koma jihar Kano don ganin yadda za ta kaya tsakanin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Gwamna Abba Yusuf.

Tun daga lokacin da Abba ya shiga APC bayan ya bar NNPP, Sanata Rabiu Kwankwaso ke shelanta wa duniya cewa gwamnan ya ci amanarsa, ya darikar 'yan Kwankwasiyya.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi magana kan shirin hada tafiya da Nasiru Gawuna a Kano

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce falle daya e ga Abba a jihar Kano.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yana daga hannun Abba Kabir Yusuf da Kwamared Aminu Gwarzo bayan nasarar zabensu a 2023. Hoto: @KwankwasoRM
Source: Twitter

"Falle 1 ce," Kwankwaso ya soki Abba

A wani taron magoya bayan darikar Kwankwasiyya, wanda Sulaiman Uwaisu Idris ya wallafa bidiyon a shafinsa na X, Sanata Rabiu ya yi kakkausar suka kan Gwamna Abba Yusuf.

Da fari, Sanata Kwankwaso ya karbi wani sabon take da 'yan siyasar Kano da ma Arewa ke amfani da shi, watau 'Falle daya ce,' wanda ke nufin, 'wa'adi daya kawai mai mulki zai yi."

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce:

"...saboda harkoki ne na siyasa, kuma ga shi matasa suna 'falle daya ce.' Yanzu wannan abin da ya yi babu mai hakalin da zai yi shi, yanzu duk a cikinku nan (yana nuna mahalarta taron) wanda zai iya yin abin da Abba ya yi ya daga hannunsa mu gani."

Gaba daya mahalarta taron suka amsa da cewa, "babu."

Sanata Kwankwaso ya ci gaba da cewa:

"Saboda haka wannan wani abu ne na kwakwalwa ta juya. In ban da juyin kwakwalwa babu yadda za ka dauki wuka ka dabawa cikinka. Dama wurin da ka tafi fada ake yi, kuma sai kawai ka je ka ce duk wadanda ke fadan za ka share su. Saboda hakan wannan rashin ganewa ne, mafi mahimmanci, zuciya ba kyau."

Kara karanta wannan

Awanni da raka mahaifinsa kotu, Bello El-Rufai ya ziyarci babban dan siyasa a Kaduna

Ana ganin cewa, yanzu Kwankwasiyya za ta rika amfani da taken 'falle daya ce' a yakin neman kada gwamantin Abba, la'akari da cewa tuni mawaki Tijjani Gandu ya fitar da waka da wannan taken.

Kalli bidiyon a kasa:

Kwankwaso ya jaddada cin amanar Abba

Game da abin da ya kira 'cin amana' saboda sauya shekar Gwamna Abba Yusuf zuwa APC, a wani bidiyon na daban da Sulaiman Uwaisu ya wallafa a shafinsa na X, an ji Kwankwaso yana misalta siyasar wata jiha da ta jihar Kano.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce mai hankali ba zai iya yin irin cin amanar da Abba ya yi masa ba.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yana jawabi a kusa da Gwamna Abba Yusuf a Kano. Hoto: @KwankwasoRM
Source: Twitter

Kwankwaso ya ce akwai wani gwamna, a jihar da ke makwabtaka da Kano, ya fito ya ce 'da ya ci amanar ubangidansa, gwanda ya mutu', yana mai cewa, irin hakan ta sa gwamnan ya fito da darajar maigidan nasa.

Sai dai, Kwankwaso ya ce abin takaici ne yadda Kanawa suka wahala, tun a zaben 2019 da Abba ya ci zabe aka kwace, har zuwa 2023 da ya samu nasara saboda jajurcewar al'umma, amma yanzu Abba ya koma wajen wadanda jama'a ke kyamatar halayensu.

"Mutane da yawa sun yi magana, ba a taba ganin butulci irin wannan wannan ba, kuma na tabbata Allah ba zai barsu ba. Wasu har yanzu ba su yarda ba, saboda abin ya yi nisan da hankali ma ba zai dauka ba."

Kara karanta wannan

An zo wajen: Gwamna Abba ya yi magana kan lokacin cire jar hular Kwankwasiyya

- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Kalli bidiyon a nan kasa:

Abba ya tabo batun cire jar hula

A wani labari, mun ruwaito cewa, Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi magana kan daina sanya jar hular Kwankwasiyya.

Gwamna Abba ya sake tabbatar wa magoya bayansa cewa zai ci gaba da sanya sananniyar jar hular nan ta Kwankwasiyya, duk da komawarsa jam’iyyar APC.

Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya ce har yanzu ba a ba da wani umarni na cire hular ba domin "lokacin yin hakan bai yi ba".

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com