Kano: Hadimin Ganduje Ya Sauya Sheka, Ya Bar Ubangidansa a APC
- Hadimin tsohon Shugaban APC Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya sanar da cewa ya fice daga jam'iyya mai mulki a Kano
- Salihu Tanko Yakasai ya bayyana dalilan da suka jawi ya sauya sheka, duk da har yanzu ubangdidansa a siyasa, Ganduje na APC
- 'Dan siyasar, wanda aka fi sani da Dawisu a kafafen sada zumunta ya mika bukata ga dukkanin masu goyon bayansu ta yi watsi da jam'iyyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Salihu Tanko Yakasai, tsohon hadimin Shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC.
Ya bayyana cewa kafin ya dauki wannan mataki, ya zauna tare da tattaunawa mai zurfi da iyalai, abokai da kuma abokan aikinsa na siyasa.

Source: Facebook
Wannan na dauke a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, wanda ke dauke da takardar murabus daga APC da shaidar zama dan sabuwar jam'iyyar adawa.
Hadimin Abdullahi Ganduje ya bar APC
A cikin wata sanarwa da ya wallafa, Salihu Tanko Yakasai da aka fi sani da Dawisu ya ce wannan mataki ya biyo bayan shawarar da suka cimma.
Ya ce an cimma matakin ne bayan duba alkiblar siyasa da kuma bukatar sabon tsari da zai taimaka wajen cimma manufofinsu.
Dawisu ya bayyana cewa sauyin na daga cikin kokarin neman sabuwar hanya da za ta kawo cigaba ga harkokin siyasa da kuma al’umma baki daya.
Kiran tsohon hadimin Ganduje ga masoyansa
Salihu Tanko Yakasai ya bayyana cewa ya zauna, tare da gana wa da dukkanin wadanda suka kamata kafin ya amince da koma wa jam'iyyar hamayya ta ADC a Kano.

Source: Twitter
Ya ce:
“Bayan tuntuba mai yawa da iyalai, abokai da kuma abokan hulɗarmu na siyasa da muka dade muna aiki tare, mun yanke shawarar komawa jam’iyyar ADC a matsayin wata sabuwar alkibla.”
Hakazalika, ya tabbatar da cewa ya riga ya kammala dukkannin matakan da suka dace na ficewa daga tsohuwar jam’iyyarsa ta APC, tare da shiga sabuwar jam’iyyar ADC a hukumance.
Ya ce:
“Saboda haka, na mika takardar murabus dina daga APC, sannan na kammala rijista da sabuwar jam’iyyarmu ta ADC."
Ya kuma yi kira ga duk wanda ke da sha’awar shiga jam’iyyar ADC da su yi anfani da damar da aka samar ta hanyar yin rijista cikin sauki ta wayar hannu.
Dawisu ya bayyana cewa tsarin rijistar na zamani ne, wanda zai saukaka wa mutane shiga jam’iyyar ba tare da wahala ba.
Ganduje ya bude masallaci a Kano
A wani labarin, kun ji cewa tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da sabon masallacin da gidauniyarsa ta gina a jihar Kano.
Rahotanni sun nuna cewa Abdullahi Ganduje ya gayyaci mai martaba Aminu Ado Bayero buden masallacin, wanda za a rika gudanar da Sallar Juma'ah a cikinsa.
Manyan 'yan siyasa, malamai daga ciki da wajen Kano da sun shaida bude masallacin da aka ba Sheikh Lawal Shuaibu Abubakar, inda aka yi addu'o'i samun ci gaba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

