Kano: APC Ta Wanke Kanta daga Zargin Hannu a Harin da Ya Jikkata Ƴan NNPP

Kano: APC Ta Wanke Kanta daga Zargin Hannu a Harin da Ya Jikkata Ƴan NNPP

  • Jam'iyya mai mulki ta APC ta musanta zargin cewa tana da hannu a harin da aka ce an kai wa ‘yan NNPP a Kano
  • Jam’iyyar ta ce zargin ba shi da tushe, kuma tana hasashen yana da nasaba da rikicin cikin gida na NNPP kai tsaye
  • APC ta goyi bayan gudanar da bincike mai zaman kansa kan lamarin domin a hukunta mutanen da suka kai harin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Jam’iyyar APC a jihar Kano ta fito ta musanta zargin da ake yi mata na cewa tana da hannu a harin da aka ce an kai wa wasu ƴan NNPP a yankin Ruwan Bago, da ke karamar hukumar Rogo.

Zargin dai ya samo asali ne bayan NNPP ta yi ikirarin cewa wasu ‘yan daba da ake zargin suna da alaka da APC ne suka kai hari ga ƴaƴanta yayin wani taron siyasa da suka gudanar a yankin.

Kara karanta wannan

Yadda gwamnati ta yi ganawar sirri da Sarki gabanin sanar da hawan Sallah a Kano

APC ta ce ba fa da hannu a harin da aka kai wa NNPP
Shugaban APC na Kano, Umar Haruna Doguwa Hoto: Umar Kakisu Yalwa
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa sai dai APC ta ce wannan zargi ba gaskiya ba ne, kuma wani yunkuri ne na jefa ta cikin rikicin da ba ta da hannu a ciki.

APC ta yi magana kan harin Kano

Trust Radio ta ruwaito cewa a cikin wata sanarwa da APC mai mulki a jihar Kano ta fitar, ta bayyana cewa jam’iyyar su tana bin doka da oda.

Ta bayyana cewa haka kuma ba ta taba amincewa da duk wani nau’i na tashin hankali a harkokin siyasar ƙasar nan ba.

Ya jaddada cewa jam'iyyar APC ba da tarihin gudanar da siyasa a cikin lumana da bin tsarin dimokuradiyya a Najeriya.

Sanarwar ta kuma ce abin mamaki ne yadda NNPP ta zabi dora alhakin lamarin a kan APC maimakon ta mayar da hankali wajen magance matsalolin cikin gida da ke addabar jam’iyyar.

APC ta yi nuni da cewa a baya-bayan nan ana samun sauye-sauyen siyasa da sauya sheka a cikin NNPP, wanda hakan ke haifar da rashin jituwa a tsakanin mambobinta.

Kara karanta wannan

Iran ta 'ki hakura, ta taso Amurka a gaba game da kashe yan mata a makaranta

Jam'iyya APC na son a binciki harin NNPP

Duk da cewa APC ta yi watsi da zargin, ta bayyana goyon bayanta ga duk wani yunkuri na hukumomin tsaro na gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Jam’iyyar ta ce hakan zai taimaka wajen gano gaskiya a kan yadda aka kai harin tare da tabbatar da adalci ga duk wanda abin ya shafa.

APC na son a binciki harin da aka kai wa NNPP
Taswirar jihar Kano inda aka samu rikicin siyasa Hoto: Legit.ng
Source: Original

APC ta kuma bukaci hukumomi da su tabbatar da cewa duk wanda aka samu da hannu a harin, ba tare da la’akari da jam’iyyarsa ba, ya fuskanci hukunci bisa tanadin doka.

Ta kara da cewa wannan ne kadai zai kawo karshen irin wadannan zarge-zarge da kuma dakile tashin hankali a harkokin siyasa a fadin jihar Kano.

Jam’iyyar ta yi kira ga dukkanin bangarorin siyasa da su guji kalaman da ka iya haddasa rikici, tare da mayar da hankali kan gina dimokuradiyya mai dorewa a jihar Kano da kasa baki daya.

'Dan majalisa Kano ya koma APC

Kara karanta wannan

Isra'ila ta yi fariya, ta fadi nasarar da ta samu a kan fadar Ayatollah Khamenei

A baya, mun wallafa cewa ɗan majalisar wakilai daga karamar hukumar Dala, Aliyu Sani Madakin Gini, ya sanar da ficewarsa daga NNPP baki daya zuwa APC mai mulki.

Kamar sauran 'yan siyasa, Madakin Gini ya bayyana cewa rikicin cikin gida a jam’iyyar NNPP ne ya sa ya dauki wannan mataki na rabuwa da ita zuwa APC.

Ya yi karamin bayani da cewa rabuwar kawuna tsakanin bangaren Boniface Aniebonam da na Rabiu Musa Kwankwaso ta jawo masu gagarumar matsala.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng