Ana Rade Radin Tsohon Minista zai Rabu da Tinubu, Babban Makusancinsa Ya Fice daga APC

Ana Rade Radin Tsohon Minista zai Rabu da Tinubu, Babban Makusancinsa Ya Fice daga APC

  • An fara ganin na jikin Mohammed Abubakar Badaru, tsohon Ministan tsaro sun fara barin jam'iyya mai mulki
  • Tsohon shugaban karamar hukumar Gwaram, Zahraddeen Abubakar, ya yi murabus daga jam’iyyar APC
  • Ya ce jam’iyyar ta kauce daga manufofin da aka kafa ta a kansu tun 2013, kuma tuni aka fara hasashen jam'iyyar da zai koma

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Jigawa–Tsohon shugaban karamar hukumar Gwaram a jihar Jigawa, Zahraddeen Abubakar, ya sanar da murabus dinsa daga jam’iyya mai mulki a Najeriya, APC.

Zahraddeen Abubakar na daga cikin na kusa da tsohon ministan tsaro, Mohammed Badaru, wanda ya taba zama gwamnan jihar Jigawa na wa’adi biyu.

Makusancin tsohon Minista ya bar APC
Tsohon Ministan tsaro Mohammed Abubakar Badaru, Zahradeen Abubakar Hoto: Tijjani Muazu Kila
Source: Facebook

Jaridar Premium Times ta wallafa cewa a lokacin wa’adin mulkinsa na biyu ne Zahraddeen Abubakar ya rike mukamin shugaban karamar hukumar Gwaram a jihar Jigawa.

Kara karanta wannan

Hadimin Osinbajo ya raba wa ADC gardama, ya fadi mutum 2 da suka dace da yin takara a 2027

Makusancin tsohon Minista ya bar APC

Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa Zahraddeen Abubakar ya rubuta wasikar murabus mai dauke da kwanan wata 28 ga Fabrairu, 2026 wacce ya aike wa shugaban APC na mazabar Zandam Nagogo tare da aika kwafinta ga INEC.

A cikin wasikar, Zahraddeen Abubakar ya bayyana cewa jam’iyyar APC ta kauce daga muhimman manufofi da aka kafa ta a kansu tun bayan hadewar jam’iyyun da suka samar da ita a shekarar 2013.

Ya ce wannan sauyi da ya faru a cikin tafiyar jam’iyyar ne ya sa ya ga dacewar yin murabus daga APC domin bin wata sabuwar hanya ta siyasa.

Ana hasashen sabuwar jam'iyyar Zahradeen bayan APC

Bayan sanarwar murabus din nasa, ana sa ran cewa zai shiga jam’iyyar adawa ta ADC, wacce a baya-bayan nan ta fara jan hankalin wasu jiga-jigan ‘yan siyasa a sassan kasar.

A halin yanzu, Zahraddeen Abubakar shi ne shugaban jihar Jigawa na kungiyar tsofaffin zababbun shugabannin kananan hukumomi ta kasa, wato NALGON

Kara karanta wannan

An samu sunayen Sanatan Kaduna da wasu sanatoci 8 da suka sauya sheka zuwa ADC

Ana hasashen makusancin Badaru zai koma ADC
Alhaji Atiku Abubakar tare da tsohon Shugaban ƙaramar hukumar Gwaram, Zahradeen Abubakar Hoto: Tijjani Muazu Kila
Source: Facebook

Har ila yau, ba da dadewa ba aka nada shi a matsayin ɗan kwamitin tantance masu takarar shugabannin mazabu da kananan hukumomi na jam’iyyar APC a jihar Ogun. Murabus din Zahraddeen Abubakar na zuwa ne bayan ganawa masu muhimmanci da aka rika yi tsakanin jagoransa na siyasa, Mohammed Badaru Abubakar, da wasu ‘yan adawa a jihar Jigawa.

Wadannan ganawa sun haifar da rade-radin cewa tsohon ministan tsaron na shirin ficewa daga APC zuwa jam’iyyar ADC bayan ya rabu da kujerarsa ta Minista.

Ana zaton tsohon Minista zai bar APC

A baya, kun ji cewa Mohammed Abubakar Badaru ya gana da Mustapha Lamido, wanda shi ne dan takarar gwamna na PDP a zaben 2023 a jihar Jigawa, kuma dan fitaccen dan siyasa Sule Lamido.

Sai dai Badaru ya bayyana cewa manufar wadannan ganawa ba wai shirin sauya sheka ba ne, illa kokarin karfafa hadin kai a cikin jam’iyyar APC a jihar Jigawa da kuma yankin Arewa maso Yamma.

Ya kuma ce tattaunawar na daga cikin shirye-shiryen da ake yi domin tunkarar babban zaben shekarar 2027 tare da gina goyon baya ga sake zaben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng