Hadimin Osinbajo Ya Raba wa ADC Gardama, Ya Fadi Mutum 2 da Suka Dace da Yin Takara a 2027
- Hadimin tsohon Mataimakin Shugaban kasa, Laolu Akande ya bayyana wadanda za su iya kayar da Bola Tinubu a zaben 2027 a ra'ayinsa
- Tsohon hadimin na Yemi Osinbajo ya ce Rotimi Amaechi da Peter Obi su ne suka fi dacewa su kalubalanci Bola Tinubu a babban zaben
- Ya jaddada cewa dimokuradiyya mai dorewa tana bukatar adawa mai karfi, ya bukaci jam’iyyun adawa su mara wa dan takara daga kudu baya
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja –Tsohon mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Laolu Akande, ya yi hasashen yadda za a iya fitar da gwamnatin APC daga Aso Rock.
Ya ce tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, da tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, su ne suka fi dacewa su kalubalanci Bola Tinubu a zaben 2027

Source: Twitter
Akande ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin da yake magana a shirin Sunrise Daily na gidan talabijin na Channels Television.
An shawarci jam'iyyar ADC kan zaben 2027
Jaridar The Cable ta wallafa cewa a baya dai Amaechi, wanda ya taba zama dan takarar shugaban kasa a karkashin ADC, ya bukaci jam’iyyar ta yi la’akari da tsayar da dan takara daga yankin kudu a zaben 2027.
Haka kuma kwanaki kafin hakan, Obi ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takarar shugaban kasa bayan ya taba zama dan takarar jam’iyyar LP a zaben baya.
Akande ya bayyana cewa dimokuradiyya mai inganci na bukatar adawa mai karfi wacce za ta iya kalubalantar gwamnati.

Source: Facebook
Ya ce irin wannan kalubale yana da muhimmanci domin tabbatar da dorewar tsarin dimokuradiyya a kasa. A cewarsa:
“Kalubale mai ma’ana daga bangaren adawa abu ne da ake bukata domin dimokuradiyya ta ci gaba da dorewa.”
2027: Yadda ADC za ta hada kai
Ya kara da cewa dole ne a samu tattaunawa da wayar da kan jama’a domin inganta tsarin siyasa a Najeriya gabanin 2027.
Akande ya kuma yi nuni da cewa idan jam’iyyun adawa na son kalubalantar jam’iyya mai mulki, ya kamata su fahimci cewa shugabancin kasa zai ci gaba da kasancewa a hannun yankin kudu.
Ya ambaci yiwuwar sake tsayawar takarar Atiku Abubakar a matsayin daya daga cikin abubuwan da ke haifar da rudani a tsakanin jam’iyyun adawa.
Akande ya bukaci jam’iyyun adawa su hada kai su mara wa fitattun ‘yan siyasar kudu baya domin a samiu nasara a zaben 2027.
Ya ce idan har adawa tana da niyyar kalubalantar gwamnati da gaske, ya kamata ta tallafa wa ‘yan siyasa masu kwarewa kamar Amaechi da Obi.
Tsohon gwamna ya shiga ADC
A baya, kun ji cewa tsohon gwamnan Ribas, Rotimi Amaechi, ya tabbatar da shiga jam’iyyar ADC a hukumance yayin da ake tunkarar babban zaben 2027.
Rahotanni sun ce wasu da ba a san ko su waye ba sun kona ofishin jam’iyyar ADC a Ubima kafin rajistar tsohon Ministan sufuri Amaechi lamarin da ya jawo tashin hankali.
Ya roƙi magoya bayansa su guji tashin hankali, yana cewa babu wanda zai hana su taruwa a yankinsu, ya kuma yabawa jami’an tsaro a kan kokarinsu na murkushe matsalar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


