"Ba za Mu Lamunci Cin Amana da Rashin Biyayya ba": Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gargadi 'yan majalisar zartarwa su daina fitar da bayanan gwamnati sakaka ga jama'a
- Ya ce dole su hada kai domin ci gaban Kano da jin dadin al’umma, kuma ba za a kara lamuntar masu kawo tasgaro ga haka ba
- Gwamnan ya kuma tabbatar da murabus na kwamishinoni biyar bayan gwamnatin jihar ta sauya sheka daga NNPP zuwa APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gargadi 'yann majalisar zartarwar jihar da su guji rashin biyayya, rikicin cikin gida da kuma fitar da bayanan gwamnati.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin taron majalisar zartarwa na 38 da ya yi da 'yan majalisar gwamnati, inda ya jaddada muhimmancin aiki tare domin cika manufofin gwamnatin jihar.

Kara karanta wannan
Isra'ila ta ji ruwan wuta, ta fara karaya a shirin da ta yiwa gwamnatin Musulunci ta Iran

Source: Facebook
A sanarwar da hadiminsa Sanusi Bature D-Tofa ya wallafa a shafin Facebook, Gwamnan ya ce lokaci ya yi da ya kamata kowa ya daina sabanin ra’ayi gwamnati.
Gwamnan Kano ya gargadi Kwamishinoni
Sanarwar ta kara da cewa haka kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nemi mukarraban gwamnati da su kauce wa rikicin cikin gida.
Ya ce:
“Zamanin rikici, zamanin rashin biyayya, zamanin fitar da bayanan gwamnati, da kuma cin dunduniyar juna ya wuce."
Ya kara da cewa dole ne 'yan majalisar zartarwar su hada kai wajen tabbatar da cigaban jihar Kano da kuma kyautata rayuwar al’ummar jihar.
Abba ya magantu kan sauya sheka a Kano
Gwamna Abba ya kuma yi bayani kan dalilan sauyin siyasar da ya kai shi da wasu manyan siyasa na jihar zuwa APC. A cewarsa, an dauki wannan mataki ne bayan tattaunawa da 'yan majalisar zartarwar jihar, da ‘yan majalisar dokoki na jiha da na kasa.

Source: Facebook
Ya tabbatar da cewa an kuma gana da shugabannin kananan hukumomi 44 na jihar Kano, da kuma sauran masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa.
Gwamnan ya bayyana cewa burinsu shi ne su samar da karin ci gaban tattalin arziki da kuma ayyukan more rayuwa a jihar, tare da samun hadin kai daga gwamnatin tarayya.
Ya ce:
"Muna bukatar ci gaban tattalin arziki da kuma ababen more rayuwa a cikin jiharmu, kuma hakan na bukatar goyon baya da hadin kai daga gwamnatin tarayya.”
Gwamnan ya kuma tabbatar da cewa kwamishinoni biyar sun ajiye mukamansu sakamakon sababbin sauye-sauyen siyasa da aka samu a jihar, inda ya ce ya amince da murabus din nasu.
An tsige Shugaban ma'aikatan gwamnatin Kano
A baya, mun wallafa cewa Gwanna Abba Kabir Yusuf ya tsige shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar Kano, Abdullahi Musa kuma ya nada Hajiya Bilkisu Maimota a kujerarsa.
Wannan mataki na daga cikin kokarin sake fasalin aikin gwamnati bayan sauyin shekar Gwamnan Kano daga jam'iyyar NNPP zuwa APC a watan Janairu na shekarar 2026.
Gwamnan ya gode wa tsohon shugaban ma'aikatan bisa kokarinsa sannan ya bukaci ya mika ragamar ofishin ga Hajiya Bilkisu a matakin Shugaba ta rikon kwarya.
Asali: Legit.ng
