An Samu Sunayen Sanatan Kaduna da Wasu Sanatoci 8 da Suka Sauya Sheka zuwa ADC
- Jam'iyyar hadaka ta ADC ta fara karfi a Majalisar dattawa yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen babban zabe mai zuwa a 2027
- A zaman majalisar na yau Alhamis, 12 ga watan Maris, 2026, sanatoci tara sun mika takardar ficewa daga jam'iyyunsu zuwa ADC
- ADC ita ce jam'iyyar da manyan kusoshin adawa a Najeriya suka ayyana a matsayin dandalin hadaka da nufin kifar da gwamatin APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Sanatoci tara daga jam’iyyun adawa sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar hadaka ta ADC a zauren Majalisar Dattawan Najeriya.
Sanatocin sun fito ne daga jam’iyyun PDP, LP, da kuma APGA, inda dukansu suka mika takardar tabbatar da komawarsu ADC a hukumance a zaman Majalisa na yau Alhamis, 12 ga watan Maris, 2026.

Source: Twitter
Wani mai amfani sa kafar sadarwa ta X, wacce aka fi sani da Twitter, Imran Muhammad ne ya tabbatar da hakan a wani sako mai hade da bidiyo da ya wallafa a shafinsa.
Jerin sanatocin da suka koma ADC
1. Sanata Ireti Kingibe – Mai wakiltar babban birnin tarayya Abuja (LP zuwa ADC)
2. Sanata Mohammed Ogoshi Onawo – Mai wakiltar Nasarawa ta Kudu (PDP zuwa ADC)
3. Sanata Aminu Waziri Tambuwal – Mai wakiltar Sakkwato ta Kudu (PDP zuwa ADC)
4. Sanata Binos Dauda Yaroe – Mai wakiltar Adamawa ta Kudu (PDP zuwa ADC)
5. Sanata Austin Akobundu – Mai wakiltar Abia ta Tsakiya (PDP zuwa ADC)
6. Sanata Enyinnaya Abaribe – Mai wakiltar Abia ta Kudu (APGA zuwa ADC)
7. Sanata Victor Umeh – Mai wakiltar Anambra ta Tsakiya (LP zuwa ADC)
8. Sanata Tony Nwoye – Mai wakiltar Anambra ta Arewa (LP zuwa ADC)
9. Sanata Lawal Adamu Usman –Mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya (PDP zuwa ADC).
'Yan adawa sun yi hadaka a ADC
ADC ita ce jam'iyyar da manyan jagororin adawar Najeriya suka yi hadaka a cikinta da nufin hada karfi da karfe wajen kwace mulki daga hannun jam'iyyar APC a zaben 2027.
Manyan jiga-jigan da ke jagorantar wannan hadaka sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar da tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi.

Source: Twitter
Sauran jiga-jigan tafiyar sun kunshi tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai da manyan 'yan siyasa daga sasaa daban-daban na kasar nan.
Ana ganin sauya shekar 'yan Majalisar dattawa zai karawa jam'iyyar ADC karfi yayin da ake shirye-shiryen tunkarar babban zaben 2027, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Kabir Abdullahi, wani mamban ADC a karamar hukumar Danja ta jihar Katsina ya yi maraba da wannan ci gaba, yana mai cewa sun shirya ba APC mamaki a zaben 2027.
Matashin dan siyasar ya byyana cewa talakawa ba su tare da wannan gwamnati, inda ya ve galibin yan Najeriya sun gaji da wahalhalun da APC ta kawo.
"Wane ci gaba aka samu a mulkin APC? Babu sai dai yunwa da matsalar tsaro, don haka ina da yakinin talakawa sun shirya zaba wa kansu mafita a zaben 2027," in ji shi.
Sanatan Bayelsa ya fice daga PDP

Kara karanta wannan
Hadimin Osinbajo ya raba wa ADC gardama, ya fadi mutum 2 da suka dace da yin takara a 2027
A wani rahoton, kun ji cewa sanata mai wakiltar Bayelsa ta Yamma, Seriake Dickson, ya fice daga PDP a Najeria saboda rigingimu da suke damun jam'iyar mai adawa.
Seriake Dickson wanda tsohon gwamnan jihar Bayelsa ne ya sauya sheƙa daga PDP zuwa sabuwar jam’iyyar NDC da INEC ta yi wa rijista kwanan nan.
Sanatan ya kuma zargi wasu gwamnonin PDP da raunana jam’iyyar ta hanyar yin aiki tare da jam’iyya mai mulki ta APC.
Asali: Legit.ng

