Shugaban PDP Ya Bi Gwamnan Zamfara, Ya Sauya Sheka zuwa Jam'iyyar APC

Shugaban PDP Ya Bi Gwamnan Zamfara, Ya Sauya Sheka zuwa Jam'iyyar APC

  • Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Zamfara, Dr. Jamil Jibo Magayaki, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki
  • Dr. Jamil Jibo Magayaki ya dauki wannan mataki ne bayan sauya shekar gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, zuwa APC
  • Ya kara da cewa sauya shekar da ya yi ta samo asali ne daga bukatar shiga sahihiyar siyasa domin amfanin Zamfarawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Zamfara – Shugaban jam’iyyar PDP a jihar Zamfara, Dr. Jamil Jibo Magayaki, ya sanar da sauya shekarsa zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

Rahotanni sun nuna cewa Dr. Jamil Magayaki ya bi sahun wasu manyan ‘yan siyasa a jihar wajen komawa APC.

Shugaban PDP na Zamfara ya koma PDP
Tsohon Shugaban PDP na Zamfara, Dr. Jamil Jibo Magayaki @Kdankasa
Source: Twitter

Daily Trust ta wallafa cewa matakin da ya biyo bayan sauya shekar gwamnan jihar, Dauda Lawal, wanda shi ma ya shiga jam’iyyar mai mulki.

Kara karanta wannan

Tambuwal ya gaji da raba kafa, ya tattara kayansa daga PDP zuwa jam'iyyar ADC

Shugaban PDP a Zamfara ya koma APC

Daily Post ta wallafa cewa sauya shekar shugaban PDP na jihar na zuwa ne a wani lokaci da ake ganin siyasar Zamfara na kara daukar sabon salo, inda wasu jiga-jigan PDP ke komawa APC.

A wata sanarwa da Dr. Jamil ya fitar, ya tabbatar da cewa ya yanke shawarar ficewa daga PDP tare da komawa APC, yana mai bayyana cewa wannan mataki ya dace da yanayin siyasar da ake ciki yanzu a jihar.

Sanarwar ta jaddada cewa sauya shekar tasa ba ta zo ba zato ba tsammani ba, domin a cewarsa, akwai bukatar yin nazari kan halin da ake ciki a siyasar jihar domin daukar matakin da zai amfani al’ummar Zamfara.

Dalilan sauya shekar shugaban jam'iyyar PDP

A cikin sanarwar, Dr. Jamil Jibo Magayaki ya bayyana cewa matakin da ya dauka na komawa APC ya samo asali ne daga yadda siyasa ta sauya a jihar Zamfara a halin yanzu.

Kara karanta wannan

'Yaƙi ya kare': Abin da Matawalle ya ce bayan Dauda Lawal ya koma APC

Shugaban PDP ya bar jam'iyya kwanaki kadan da Dauda Lawal ya sauya sheka
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

Ya ce:

“Ni, Dr. Jamil Jibo Magayaki, shugaban jam’iyyar PDP na jihar Zamfara, ina sanar da sauya sheka ta a hukumance zuwa APC mai mulki.”

Dr. Jamil ya bayyana cewa burinsa shi ne ganin an samu ingantaccen tsaro, ci gaba da kyakkyawan shugabanci domin amfanin al’ummar jihar.

Ya ce shiga APC zai ba shi damar hada kai da sauran shugabanni domin fuskantar kalubalen da Zamfara ke fuskanta, musamman a bangaren tsaro da ci gaban tattalin arziki.

Sauya shekar tasa na kara nuna yadda siyasar Zamfara ke canzawa, musamman bayan sauyin da ya faru a matakin gwamnati da kuma jam’iyyun siyasa a jihar.

Dauda Lawal ya koma APC

A baya, mun wallafa cewa Mataimakin gwamnan Zamfara, Mani Malam Mummuni ya kawo karshen jita-jitar da ake yadawa kan shirin Gwamna Dauda Lawal na komawa APC.

Rahotanni sun nuna cewa Mani ya sanar da ficewar Gwamna Dauda Lawal tare da mukarrabansa, daga PDP zuwa APC mai mulkin Najeriya bayan an yi shawarwari.

Wannan na zuwa ne makonni kadan bayan gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya raba gari da jam'iyyar NNPP, tare da komawa APC gabanin zaben 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng