Tambuwal Ya Gaji da Raba Kafa, Ya Tattara Kayansa daga PDP zuwa Jam'iyyar ADC
- Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar adawa ta PDP bayan dogon nazari da shawarwari
- Tsohon gwamnan Sakkwato ya ce rikice-rikicen cikin gida da sabanin shugabanci sun sa ya kasa ci gaba da zama a jam’iyyar
- Tambuwal ya tabbatar da cewa ya koma jam’iyyar hamayya ta ADC tare da magoya bayansa domin ci gaba da fafutukar siyasa
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Sokoto – Tsohon gwamnan jihar Sokoto kuma tsohon kakakin majalisar wakilai ta kasa, Aminu Waziri Tambuwal, ya sanar da ficewarsa daga PDP.
Ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce ya dauki wannan mataki ne bayan tunani da kuma tuntuba da abokan siyasa da magoya bayansa.

Source: Twitter
Wannan na kunshe a cikin sanarwar da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya bayyana dalilan da suka sa ya rabu da PDP.
Sanata Aminu Tambuwal ya sauya sheka
Tambuwal ya ce ya riga ya mika takardar murabus dinsa ga shugaban jam’iyyar a mazabarsa a rubuce domin tabbatar da matakin da ya dauka.

Source: Facebook
A cewarsa, PDP ta taka muhimmiyar rawa a tafiyarsa ta siyasa tsawon shekaru da dama da ya taka matakai masu girma.
Ya bayyana cewa jam’iyyar ta ba shi damar yin hidima ga kasa a manyan mukamai, daga ciki har da lokacin da ya rike mukamin kakakin majalisar wakilai.
Ya kuma jinjina wa jam'iyyar da ta ba shi damar yin takara da zama gwamnan Sakkwato har sau biyu.
Daga shekarar 2007 zuwa yau, Tambuwal ya canza sheka sau da dama daga jam'iyyar ANPP da aka fara sanin shi da ita zuwa DPP kafin ya sake dawowa.

Kara karanta wannan
Tsautsayi ya gitta, harin kasar Iran ya rutsa da 'dan Najeriya da wasu mutane sama da 100
Daga baya ya cigaba da tsalle tsakanin ANPP da PDP a majalisar wakilai. A 2014 Tambuwal ya shiga APC har ya zama gwamna, ya kuma bar ta gabanin zaben 2019.
Me ya sa Tambuwal ya koma jam'iyyar ADC?
Sai dai Tambuwal ya ce duk da irin gudunmawar da jam’iyyar ta bayar a rayuwarsa ta siyasa, rikice-rikicen cikin gida da rashin jituwa tsakanin shugabanni sun kara tsananta.
Ya ce wadannan matsaloli sun janyo rarrabuwar kawuna a cikin PDP tare da raunana hadin kai da alkiblar da jam’iyyar ta taba kasancewa da su a baya.
A cewar Tambuwal, wadannan rikice-rikice na cikin gida ne suka sa ya ga ba zai iya ci gaba da zama a cikin jam’iyyar ba.
Sanatan ya ce hakan ne ya tilasta masa daukar matakin ficewa daga PDP bayan nazari mai zurfi tare da yanke shawarar ficewa daga cikinta zuwa ADC.
Ya ce ya dauki wannan mataki ne bisa imanin cewa Najeriya na bukatar wani dandalin siyasa mai karfi da za ta ginu a kan gaskiya, rikon amana, da kuma hada kan ‘yan kasa ba tare da wariya ba.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga fiye da 40 sun mutu yayin da suka hana mutane sallar Juma'a a Ramadan
Tambuwal ya gano matsala game da zabe
A baya, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Sakkwato kuma tsohon shugaban majalisar wakilai ta kasa, Aminu Waziri Tambuwal, ya bayyana damuwarsa kan zabukan Najeriya.
A cikin wata hira da aka yi da shi a ranar Litinin, 12 ga watan Janairu, 2026, Tambuwal ya ce duk da cewa ’yan Najeriya na fita suna kada kuri’a, ba koda yaushe ake bayyana ra'ayinsu ba.
Ya kara da cewa babban abin damuwa shi ne yadda ake tattara sakamakon zabe daga matakin mazabu zuwa babban kwamiti, inda ya ce ana tafka kura-kurai da dama.
Asali: Legit.ng
