Kano: NNPP Ta Kuma Rasa 'Dan Majalisar Tarayya ga APC gabanin 2027
- 'Dan majalisar wakilai daga karamar hukumar Dala, Aliyu Sani Madakin Gini, ya sanar da ficewarsa daga NNPP baki daya
- Kamar sauran 'yan siyasa, Madakin Gini ya bayyana cewa rikicin cikin gida a jam’iyyar NNPP ne ya sa ya dauki wannan mataki
- Ya ce rabuwar kawuna tsakanin bangaren Boniface Aniebonam da na Rabiu Musa Kwankwaso ta jawo masu gagarumar matsala
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Dala a majalisar dokokin tarayya, Aliyu Sani Madakin Gini, ya sanar da ficewarsa daga NNPP.
Madakin Gini, wanda a yanzu yake rike da mukamin mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai, ya bayyana matakin nasa ne cikin wata wasika mai kwanan watan 10 ga Maris, 2026.

Source: Facebook
Jaridar Aminiya ta wallafa cewa an aike da wasikar ga shugaban jam’iyyar NNPP na mazabar Yalwa a karamar hukumar Dala ta jihar Kano.
'Dan majalisar NNPP ya sauya sheka
21st Century Chronicle ta wallafa cewa a cikin wasikar, dan majalisar ya bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne bayan tuntubar abokan siyasa da magoya bayansa da dama a fadin jihar Kano.
Ya ce tuntubar da ya yi ta shafi mutane da dama musamman daga dukkanin mazabu 12 da ke cikin mazabar tarayya ta Dala da ya ke wakilta.

Source: Twitter
Madakin Gini ya kara da cewa yanke shawarar barin NNPP ba abu ne mai sauki ba, la’akari da irin dogon lokaci da ya shafe yana tare da jam’iyyar da kuma akidar siyasar Kwankwasiyya.
Sai dai duk da wannan alaka mai tsawo, ya ce rikice-rikicen cikin gida da ke kara kamari a jam’iyyar sun sa dole ya sake duba mafitarsa.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Rasha ta yi nasara, ta fi kowa amfana da yakin Iran da Amurka, Isra'ila
Dalilin komawar Madakin Gini cikin APC
A cewar Madakin Gini, jam’iyyar NNPP ta shiga wani yanayi na rarrabuwar kawuna, inda bangarori biyu ke takaddama kan shugabanci da akidar tafiyar jam’iyyar.
Ya bayyana cewa bangare daya na biyayya ga wanda ya kafa jam’iyyar, wato Boniface Aniebonam, yayin da dayan bangaren kuma ke goyon bayan tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.
A cewarsa, wannan rikici ya jawo samuwar shugabanni biyu a matakai daban-daban na jam’iyyar, tun daga matakin mazaba har zuwa na kasa.
Madakin Gini ya ce irin wannan yanayi ya sa jam’iyyar ta kasa tafiyar da harkokinta yadda ya kamata, lamarin da ya jefa ‘ya’yanta cikin rudani.
Ya ce:
“Ina sanar da ku a hukumance cewa daga wannan lokaci na fice daga jam’iyyar NNPP.”
'Dan majalisar zai hakura da mukaminsa
A sakamakon canza shekar da ya yi a hukumance, dole Aliyu Sani Madakin Gini ya hakura da matsayin mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai.
Barin jam'iyyar NNPP mai hamayya ya shiga APC na nufin Hon. Madakin Gini bai cikin 'yan adawa, ya koma bangaren da ke da rinjaye a majalisar tarayyar kasar.
A baya 'dan siyasar yana cikin manyan Kwankwasiyya har ya yi takarar majalisar dattawa a zaben 2019 amma a karshe Ibrahim Shekarau ya doke shi a APC.
Madakin Gini ya magantu a kan Kwankwaso
A baya, kun samu labarin cewa 'dan Majalisar Tarayya a NNPP daga jihar Kano, Hon. Ali Sani Madaki ya magantu kan shirin tuge shi daga mataimakin shugaban marasa rinjaye.
Hon Ali Madakin Gini ya zargi Sanata Rabi'u Kwankwaso da shirya manakisar tsige shi, inda ya ce suna bata lokacinsu saboda tsohon gwamnan ba dan jam'iyyar ba ne.
Wannan na zuwa ne yayin da wasu yan majalisa daga NNPP suka shirya tube shi daga muƙaminsa na mataimakin shugaban marasa rinjaye bayan ya rabu da Kwankwasiyya.
Asali: Legit.ng

