Magana Ta Kare, Gwamna Dauda Lawal Ya Bi Sahun Abba Gida Gida, Ya Sauya Sheka zuwa APC
- Mataimakin gwamnan Zamfara, Mani Malam Mummuni ya kawo karshen jita-jitar da ake yadawa kan shirin Gwamna Dauda Lawal na komawa APC
- Rahotanni sun nuna cewa Mani ya sanar da ficewar Gwamna Dauda Lawal tare da mukarrabansa, daga PDP zuwa APC mai mulkin Najeriya
- Wannan na zuwa ne makonni kadan bayan gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya raba gari da jam'iyyar NNPP, tare da komawa APC gabanin zaben 2027
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara, Nigeria - Rahotanni daga jihar Zamfara na nuna cewa Gwamna Dauda Lawal ya fice daga jam'iyyar adawa ta PDP zuwa APC mai mulkin Najeriya.
Mataimakin gwamnan Zamfara, Mani Malam Mummuni ne ya sanar da hakan a madadin Gwamna Dauda Lawal yau Litinin, 9 ga watan Maris, 2026.

Source: Facebook
Gwamnan Zamfara ya koma jam'iyyar APC
Wani mai amfani da kafar sadarwa ta Facebook, Imran Muhammad ne ya wallafa bidiyon da aka ji mataimakin gwamnan Zamfara na sanar da komawarsu APC.
A sakon da ya walllafa tare da wani gajeren faifan bidiyo, Imran Muhammad ya ce:
"Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara, Mani Malam Mummuni, a madadin Gwamna Dauda Lawal, ya sanar da sauya shekarsu daga PDP zuwa jam'iyyar APC.
A faifan bidiyon, wanda bai wuce dakika 36 ba, an ji Mani Malam Mummuni na mabtar APC a wurin wani taro a fadar gwamnatin Zamfara da ke birnin Gusau.
Haka zalika, mataimakin gwamnan ya umarci duka mahalarta taron da su mike tsaye, domin nuna goyon bayansu ga wannan sauya sheka zuwa APC.
Dauda ya bi sahun gwamnonin adawa
Har kawo yanzu dai babu wani cikakken bayani daga gwamnatin Zamfara kan wannan ci gaban, amma dai wasu majiyoyi da dama suk jima suka ikirarin sauya shekar Gwamna Lawal.
Wannan na zuwa ne makonni kadan bayan Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sauya sheka daga jam'iyyar NNPP zuwa APC mai mulki.
A yanzu jihohin Bauchi da Oyo ne suka rage wa PDP sai kuma LP da APGA da ke mulki a Abia da Anambra.
Dalilan sauya shekar Gwanna Dauda Lawal
Malam Mummuni ya bayyana cewa rikicin cikin gida dake ƙara ruruwa a cikin jam'iyyar PDP da kuma buƙatar samar da haɗin kai mai ƙarfi domin tunkarar ƙalubalen tsaro da ci gaban jihar su ne manyan dalilan wannan sauyin sheka.
Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa ko yana godiya ga mambobin PDP kan goyon bayan da suka ba shi a shekarun baya, in ji The Nation.

Source: Facebook
A cewarsa, yanayin siyasar yanzu ya tilasta masa ɗaukar wannan babban mataki domin kyakkyawan shugabanci da kyakkyawar makomar jihar Zamfara'.
Ya jaddada cewa babban burinsa shi ne kawo ƙarshen rashin tsaro da kuma haɓaka tattalin arzikin jihar ta hanyar yin aiki kafa-da-kafa da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Gwamnoni 2 na iya barin jam'iyyar PDP
A baya, kun ji cewa akwai wasu gwamnonin PDP biyu da za su fice daga PDP, ana ganin daya daga cikinsu zai koma APC, bayan sauya shekar gwamnan Zamfara.

Kara karanta wannan
"Kada a dagula siyasar Kano": NNPP ta aika sako kan shirin tsige Mataimakin gwamna
Wata majiya ta yi zargin cewa gwamnan Bauchi kuma shigabam kungiyar gwamnonin PDP, na cikin wadanda za su iya sauka sheka kafin babban zaben 2027.
Majiyar ta ce ana zargin gwamnan ya gabatar da wasu buƙatu kamar samun tikitin kujerar majalisar dattawa, da kujeru a majalisar dokoki ga magoya bayansa.
Asali: Legit.ng

