Bayan Dauda Lawal, An Gano Gwamnoni 2 da ake Hasashen za Su Bar PDP

Bayan Dauda Lawal, An Gano Gwamnoni 2 da ake Hasashen za Su Bar PDP

  • Ana rade-radin gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, na iya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC nan da mako mai zuwa
  • Rahotanni sun ce gwamnan da wasu magoya bayansa a jam'iyyar hamayya ta PDP na jiran hukuncin kotu kan rikicin shugabanci a jam’iyyar
  • Rahotanni sun kara da ce akwai wasu karin gwamnonin hamayya biyu da za su ne Dauda Lawal wajen rabuwa da PDP gabanin zaben 2027

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Zamfara– Rahotanni sun nuna cewa rade-radin sauya sheƙar gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, daga PDP zuwa APC na iya tabbata nan da mako mai zuwa.

Haka kuma ana zaton bayan Dauda Lawal, akwai wasu gwamnonin PDP biyu da za su fice daga PDP, ana ganin daya d sha cikinsu zai koma APC.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Sunan jigon APC ya fito cikin masu hannu dumu dumu a kisan Sarki

Ana hasashen gwamnan Zamfara na nazarin komawa APC
Gwamna Dauda Lawal Dare na jihar Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

Wani rahoto da ya kebanta ga The Nation ya ce majiyoyi daga Abuja da Gusau da kuma Kaduna sun bayyana cewa gwamnan na cikin jam’iyyar PDP yana jiran hukuncin da kotu.

Gwamnan Zamfara zai sauya sheka

Rahoton ya ce Gwamnati Dauda Lawal na mutanensa na jiran hukuncin kotun daukaka kara a kan shari’o’in da ɓangarori daban-daban suka shigar domin neman iko da shugabancin jam’iyyar.

Ana dai ganin cewa wannan hukunci zai iya zama muhimmin abu da zai taka muhimmiyar rawa kan tantance makomar wasu manyan ‘yan siyasa a PDP.

Wasu majiyoyi sun kuma ce gwamnan ya yi wasu tattaunawa da manyan shugabannin APC kan yiwuwar komawarsa jam’iyya mai mulki.

Majiyoyin sun ce gwamnan ya gana da wasu masu ruwa da tsaki na PDP a jihar Zamfara a makon da ya gabata domin tattauna makomar jam’iyyar a jihar.

Rahotanni sun nuna cewa yawancin waɗanda suka halarci taron sun nuna goyon baya ga yiwuwar sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Ministocin Tinubu 4 na shirin murabus daga mukamansu, an ji dalilin ajiye ayyukansu

Wasu gwamnonin PDP na iya sauya sheka

Rikicin cikin gida a PDP ya jefa jam’iyyar cikin wani yanayi mai sarkakiya, lamarin da ya sa wasu gwamnoni ke duba yiwuwar wasu zabuka na siyasa.

A cikin shekara guda da ta wuce, jam'iyyar hamayya ta PDP ta rasa gwamnoni da dama da suka koma APC.

Daga cikin waɗanda suka rabu da PDP akwai gwamnan Akwa Ibom Umo Eno, na Delta Sheriff Oborevwori da na Enugu.

Sauran sun hada da Gwamnan Bayelsa Duoye Diri, na Rivers Siminalayi Fubara, da na Filato Caleb Mutfwang, Peter Mbah sai kuma na Taraba Agbu Kefas.

Ana hasashen Bala Mohammed na magana da manyan APC
Gwamnan Bauchi Bal Mohammed Hoto: Senator Bala AbdulKadir Mohammed
Source: Twitter

Wata majiya ta kuma ce gwamnan Bauchi Bala Mohammed, wanda shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP, na iya kasancewa yana tattaunawa a boye da APC kan makomarsa ta siyasa. Majiyar ta ce ana zargin gwamnan ya gabatar da wasu buƙatu kamar samun tikitin kujerar majalisar dattawa, da kujeru a majalisar dokoki ga magoya bayansa.

Kara karanta wannan

Za a shiga takarar gwamna, ba a ga sunan jam'iyyun LP da PDP cikin masu fafatawa ba

Haka nan ana raɗe-raɗin, gwamnan Oyo Seyi Makinde zai bar PDP, sai dai ya sha nanata cewa rade-radin da ke cewa yana shirin komawa jam’iyyar ADC ba gaskiya ba ne.

Gwamnan Zamfara ya soki Fadar Shugaban ƙasa

A baya, mun wallafa cewa Gwamna Dauda Lawal ya ce Zamfara ba ta samu tallafin gwamnatin tarayya ba tun 2023 da Bola Tinubu ya hau mulkin Najeriya.

Gwamnan ya danganta hakan da kasancewarsa a jam’iyyar adawa ta PDP, inda ya ya ce akwai kudin tallafi da ake raba wa jihohi amma an mayar da su saniyar ware.

Dauda Lawal ya bayyana cewa duk da haka gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da manyan ayyuka ba tare da sabon bashi da zai zo ya addabi jiharsa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng