Ministocin Tinubu 4 Na Shirin Murabus daga Mukamansu, an Ji Dalilin Ajiye Ayyukansu
- Wasu daga cikin Ministocin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na iya hakura da mukamansu kafin babban zaben shekarar 2027
- Murabus dinsu na iya kasancewa ne saboda tanadin da ke cikin dokar zabe wadda majalisa ta amince da ita
- Daga cikin wadanda ake hasashen za su ajiye mukamanu akwai Muhammad Pate da Yusuf Tuggar wadanda suka fito daga jihar Bauchi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Lissafin siyasa gabanin babban zaɓen shekarar 2027 na iya janyo sauye-sauye a majalisar Ministocin Shugaba Bola Tinubu.
Alamu sun nuna wasu ministoci da ke gwamnatin tarayya suna nazarin yin murabus domin bin muradunsu na siyasa a jihohinsu a takarar badi.

Source: Facebook
Binciken da jaridar The Punch ta gudanar ya nuna cewa aƙalla mambobin majalisar Ministocin Tinubu guda huɗu sun riga sun fara shirin takara a matakin jiha.
Ministocin dai za su yi takara ne musamman a jihohin da gwamnoni masu ci za su kammala wa’adin mulkinsu na biyu a shekarar 2027.
Dokar zaɓe da lokacin murabus
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta sabunta jadawalin lokacin zaɓe, inda ta saka zaɓukan fitar da gwani na jam’iyyu tsakanin 22 ga Afrilu zuwa 20 ga Mayu 2026.
A ƙarƙashin sabuwar dokar zabe, ya zama dole masu riƙe da mukamai wadanda nada su aka yi, su yi murabus kafin ranar zaɓen fidda gwani.
Wannan na nufin ministoci, kwamishinoni, da sauran masu taimaka wa gwamnati dole su bar aikinsu kafin su shiga takara.
Ministocin ne ake hasashen za su yi murabus
Daga cikin waɗanda ake ambata akwai:
- Adebayo Adelabu (Ministan lantarki)
- Muhammad Pate (Ministan lafiya da jin daɗin jama’a)
- Yusuf Tuggar (Ministan harkokin waje)
- Nkeiruka Onyejeocha (karamar Ministar kwadago)
Adebayo Adelabu na da burin zama gwamnan Oyo
Idan babu wani canji, ana sa ran Bayo Adelabu zai yi murabus a makonni masu zuwa domin neman tikitin takarar gwamnan jihar Oyo a ƙarƙashin jam’iyyar APC.
Adelabu, wanda tsohon mataimakin gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) ne, yana neman sake gwada sa'arsa ne bayan shan kashi a hannun Gwamna Seyi Makinde a shekarar 2019 da 2023.
Jaridar Vanguard ta ce a wani bidiyo da ya karade gari a watan Oktoban 2025, Adelabu ya fito fili ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara.

Source: Twitter
Muhammad Ali Pate da Yusuf Tuggar a Bauchi
Akwai alamu masu ƙarfi cewa duka su biyun suna zawarcin kujerar gwamnan jihar Bauchi.
Dr. Muhammad Ali Pate ya taɓa neman takarar gwamna a shekarar 2015 (a PDP), 2019 (a PRP), da kuma 2023 inda ya fafata a zaɓen tsaida gwani na APC amma bai yi nasara ba.
Ana ganin Yusuf Tuggar wanda ya fito daga mazabar Udubo a karamar hukumar Gamawa yana harin neman kujerar gwamna.
Mashawarci na musamman ga ministan kan harkokin yada labarai, Alkasim Abdulkadir, ya tabbatar wa jaridar cewa:
"Ministan yana da sha'awar tsayawa takarar gwamnan jihar Bauchi."
Da aka tambaye shi ko Ministan zai yi murabus daga kan mukaminsa, Alkasim Abdulkadir ya bayyana cewa:
"Akwai jadawalin da hukumar INEC ta fitar wanda ya bayyana dokokin yin takara, Ministan zai yi aiki da su."
Nkeiruka Onyejeocha na son komawa majalisa
Karamar Ministar ƙwadago, Nkeiruka Onyejeocha ta kwashe shekaru 16 (2007-2023) tana wakiltar mazabun Isuikwuato/Umunneochi a majalisar wakilai.
Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa Ministar tana shirin sake komawa majalisa.
"An zaɓe ta sau huɗu zuwa Majalisar Wakilai, kuma tana son komawa can."
- Wata majiya
Sai dai, kokarin jin ta bakinta bai yi nasara ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoto.
Tinubu ya tura jakadun da za su wakilci Najeriya
A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya amince da tura jakadun da za su wakilci Najeriya a kasashen waje.
Shugaba Bola Tinubu ya amince da tura jakadu 65 zuwa kasashe daban-daban da kuma majalisar dinkin duniya (UN) domin karfafa wakilcin Najeriya a kasashen waje.
Jerin sunayen ya kunshi mutane 31 da ba cikakkun ma'aikatan diflomasiyya ba da kuma kwararrun ma'aikatan diflomasiyya guda 34.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


