2027: Sanata Ya Fice daga PDP, Ya Kafa Sabuwar Jam'iyya a Najeriya

2027: Sanata Ya Fice daga PDP, Ya Kafa Sabuwar Jam'iyya a Najeriya

  • Tsohon gwamnan Bayelsa, Seriake Dickson, ya fice daga PDP a Najeria saboda rigingimu da suke damun jam'iyar mai adawa
  • Dickson ya ce PDP ta lalace sosai, yana mai cewa “jam’iyyar na ci gaba da jinya ne" saboda rikicin cikin gida da ke damunta
  • Sabuwar jam’iyyar da ya shiga ta ba shi katin mamba mai lamba 001, alamar cewa yana cikin sahun farko na 'yan jam’iyyar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Yenagoa, Bayelsa - Sanatan da ke wakiltar mazabar Bayelsa ta Yamma a majalisar dattawa, Seriake Dickson, ya watsar da jam'iyyar PDP.

Seriake Dickson wanda tsohon gwamnan jihar Bayelsa ne ya sauya sheƙa daga PDP zuwa sabuwar jam’iyyar NDC da INEC ta yi wa rijista.

Tsohon gwamna ya shiga sabuwar jam'iyya bayan barin PDP
Tsohon gwamnan Bayelsa, Seriake Dickson. Hoto: Henry Seriake Dickson.
Source: Facebook

Dalilin murabus din Sanata Dickson daga PDP

Dickson ya bayyana matakin nasa ne a wani taron manema labarai da ya gudanar a gidansa da ke Abuja, inda ya ce jam’iyyar adawar da ta taba mamaye siyasar Najeriya ta lalace matuka, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar tsohon ministan Tinubu ya yake shi, yana kus kus da kusoshin adawa

Tsohon gwamnan ya nuna damuwa kan halin da PDP ta tsinci kanta, yana cewa jam’iyyar da ta taba kawo farin ciki ga magoya bayansa ta zama mai tsananin rauni.

Ya ce,

“PDP ba ta da lafiya, a halin yanzu tana kwance a dakin kulawa ta musamman watau ICU.”

Sanatan ya kuma zargi wasu gwamnonin PDP da raunana jam’iyyar ta hanyar yin aiki tare da jam’iyya mai mulki ta APC.

Sanata ya yi watsi da jam'iyyar PDP
Sanata daga jihar Bayelsa da ya yi murabus daga PDP, Seriake Dickson. Hoto: Henry Seriake Dickson.
Source: Facebook

A cewarsa, wannan lamari ya kara tsananta rikicin cikin gida a PDP tare da rage karfinta a matsayin babbar jam’iyyar adawa a Najeriya.

Dickson ya ce wannan hali ne ya sa ya yanke shawarar neman wata sabuwar hanya ta siyasa ta hanyar shiga jam’iyyar NDC, sabuwar jam’iyyar da INEC ta amince da rajistarta.

Ya bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne domin ci gaba da tafiyar siyasar sa a dandalin da ya dace da burinsa na yanzu.

NDC ta yi maraba da Sanata Dickson

Bayan jawabin nasa, shugabannin jam’iyyar NDC sun tarbe shi a hukumance cikin jam’iyyar, cewar Daily Post.

An ba shi tutar jam’iyyar tare da katin mamba mai lamba 001, wanda ke nuna cewa yana daga cikin mambobin farko na jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Duniya labari: Jigo ya mutu awanni 24 bayan ya samu kujera a APC mai mulkin Najeriya

Dickson ya taba zama gwamnan Bayelsa daga shekarar 2012 zuwa 2020 kafin daga bisani a zabe shi sanata a shekarar 2023 karkashin jam’iyyar PDP.

Sauya shekar tasa na zuwa ne a lokacin da ake ci gaba da nuna damuwa kan rikice-rikicen cikin gida a PDP da kuma yadda wasu ‘yan jam’iyyar ke ficewa zuwa wasu jam’iyyu gabanin zaben shekarar 2027.

Sanata Dickson ya karyata cewa ya koma ADC

A baya, an ji cewa tsohon gwamnan Bayelsa, Sanata Seriake Dickson ya musanta rade-radin da ake yadawa cewa ya sauya sheka daga PDP zuwa ADC.

Dickson, sanata mai wakiltar Bayelsa ta Yamma ya ce ya dauke kafa daga harkokin siyasa ne saboda jimamin rasuwar mataimakin gwamna.

Ya ce bayan kammala zaman makoki, zai zauna da abokai da makusantansa kafin yanke kowane irin mataki a siyasance.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.