Murtala Garo da 'Yan Siyasa 6 da ake Gani za a Dauko idan aka Tsige Mataimakin Gwamnan Kano
A wannan rana, 5 ga watan Maris, 2026 Majalisar Dokokin Kano ta sanar da cewa ta fara daukan matakan tsige Mataimakin gwamna, Kwamred Aminu AbdulSalam Gwarzo.
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Mataimakin gwamnan Kano da ya bi tsohon Gwamna, Rabi'u Musa Kwankwaso zai shiga matsala.
Tun bayan sauya shekar gwamna, Kwamred Aminu AbdulSalam Gwarzo ke fuskantar kalubalen tsige shi, sai dai majalisa ta nanata cewa babu wannan maganar.

Source: Facebook
Amma a yanzu, jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Majalisar Dokokin Kano ta fara shirin daukan matakan tsige shi daga kujerarsa.
Legit ta tattaro wasu manyan 'yan siyasa da za su iya maye gurbin Kwamred Aminu AbdulSalam Gwarzo idan tsige shi ta tabbata.

Kara karanta wannan
Abu ya girma: Mataimakin gwamnan Kano na tsaka mai wuya, Majalisa ta tura masa sako
Su wa za su iya zama Mataimakin Gwamnan Kano:
1. Murtala Sule Garo
Wasu na ganin gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, na iya karkata zuwa ga tsohon kwamishina, Murtala Sule Garo, domin ya zama mataimakinsa.
Wannan ra’ayi ya samo asali ne saboda rawar da Garo ya taka wajen neman takarar gwamna a karkashin APC a zaben 2023.

Source: Facebook
Idan aka dauke shi mataimaki, hakan na iya bude kofar sulhu da bangaren Abdullahi Ganduje, tare da hada kan wasu daga cikin tsofaffin magoya bayan APC a Kano.
Haka kuma, Garo na da farin jini a tsakanin matasa da wasu jiga-jigan siyasa da suka dade a jam’iyyar.
Tun bayan barinsa mukamin kwamishina, bai rike wani babban mukami ba, don haka wasu na ganin ba shi irin wannan dama zai iya kara karfafa APC musamman a yankin Kano ta Arewa.
2. Abba Bichi
Hon. Abubakar Sadiq Abubakar, wanda aka fi sani da Abba Bichi, na daga cikin matasan ‘yan siyasa masu tasiri a Kano.
Ya fito daga karamar hukumar Bichi a yankin Kano ta Arewa, inda kuma mataimakin gwamna mai ci yanzu, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya fito.
A lokacin da ya wakilci mazabar Bichi a majalisar wakilan tarayya, Abba Bichi ya samu yabo daga mutane da dama saboda ayyukan ci gaba da ya kawo wa yankinsa.
A yanzu haka akwai masu ganin cewa shugaban kwamitin kasafin kudin na majalisar wakilan tarayya na da damar taka rawa mafi girma a siyasar Kano.
3. Ahmad Garba Bichi
Ahmad Garba Bichi na daga cikin manyan Kwankwasiyya da ake magana a kansu a siyasar Kano.
Saboda matsayinsa a wannan tafiya, wasu na ganin cewa idan Abba Kabir Yusuf ya jawo shi cikin tawagarsa, hakan zai iya zama babban sauyi a siyasar jihar kafin zaben 2027.

Source: Facebook
A baya an dade ana rade-radin cewa za a ba shi wata muhimmiyar takara saboda irin goyon bayan da yake da shi.
Sai dai daga baya aka rika ganin sa a gidan gwamnati, abin da ya kara jawo hankalin masu bibiyar siyasa.
Idris Muhd Abdu Mai sharhi ne kuma dan siyasa a Kano, ya shaidawa Legit cewa:
"Lamba biyun da mu ke sa ran za a ba wa(Mataimakin gwamna) shi ne Shugaban majalisar Kano, Hon. Jibril Isma'ila Falgore ko kuma Ahmad Garba Bichi, tsohon dan takarar gwamna a Kano idan aka tsige Mataimakin gwamna."
4. Kabiru Alhassan Rurum
A yankin Kano ta Kudu kuwa, sunan Rt. Hon. Kabiru Alhassan Rurum na daya daga cikin wadanda ake ambato a matsayin masu yiwuwar zama mataimakin gwamna.
Rurum gogaggen dan siyasa ne da ya dade yana taka rawa a siyasar jihar Kano, kuma tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Kano ne.

Source: Facebook
A halin yanzu yana wakiltar mazaba a majalisar wakilan tarayya. Saboda kwarewarsa da kuma irin tasirin da yake da shi a yankin Kano ta Kudu, ana ganin zai iya kawo kuri'u.
5. Umar Ganduje
Akwai rade-radin da ke cewa Umar Abdullahi Ganduje zai iya samun wannan kujera muddin aka yi nasarar yin waje da Aminu Abdussalam Gwarzo.
A wata hira da ya yi a gidan rediyo, Umar Labaran Danga ya yi ikirarin tsohon gwamnan Kano ya bada sunan ‘dan cikinsa a matsayin mataimakin gwamna.
Sai dai duk da Abba Kabir Yusuf ya hade da Abdullahi Ganduje, babu abin da ke tabbatar da zancen Danga na cewa an kawo sunan Umar Abdullahi Ganduje.
6. Rt. Hon. Jibril Isma'il Falgore
A cewar wasu, Rt. Hon. Jibril Isma'il Falgore ne zai gaji Aminu Abdussalam Gwarzo idan har aka yi nasarar tunbuke shi daga karagar mulki.
Shugaban majalisar dokokin Kano matashi ne da ake ganin yana da goyon bayan ‘yan siyasa da dama da kuma hadin-kan ‘yan majalisar Kano.
Dr. Fahad Danladi wanda Bakono ne da ya saba yin magana a kan harkokin siyasa da shugabanci a Kano bai goyon bayan masu cewa a nada irinsu Falgore.
Dazu ya rubuta a Facebook cewa:
"Takai, Falgore da Garo duk ƴan gargajiya ne da baza su iya ciyar da Kano gaba ba. Indai cigaban jihar Kano za'a kalla, sam bai kamata su zama mataimakan gwamna ba. Kamata yayi a sirka da ƴan gayu irin su Abba Bichi, Rabiu Suleiman Bichi, Ɗangwani, Abba Ganduje da makamantan su.
Babu yadda Kano zata cigaba alhalin shuwagabannin ta na da tinani irin na mutan da."
7. Salihu Sagir Takai
Daily Trust ta rahoto cewa Salihu Sagir Takai yana cikin wadanda ake ganin za su iya dacewa da kujerar mataimakin gwamnan jihar Kano.
Salihu Takai ya dade yana neman zama gwamnan Kano tun a zaben 2011 amma abin ya faskara, ya sha kashi a jam’iyyun ANPP, PDP da kuma PRP.
Rade-radi yana yawo cewa yana da goyon bayan shugaban majalisar dattawa, Barau Jibril sai dai a shekara 70, watakila wasu su ga cewa ya tsufa.
Legit Hausa ta lura sauran mutanen da ake ambata sun hada da irinsu Rabiu Sulaiman Bichi, Yunusa Dangwani wadanda tsofaffin 'yan Kwankwasiyya ne da tuni sun cire jar hula.
Duk yadda ta kaya, ba wannan ne karon farko da aka samu irin wannan canji a gidan gwamnatin Kano ba. Ko a 2018, Hafizu Abubakar ya bar kujerar, sai aka nada kawo Nasiru Gawuna.
Za a tsige Mataimakin gwamnan Kano
A baya, mun wallafa cewa Majalisar dokokin ta fara daukar matakin tsige mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdulsalam Gwarzo, bayan ta aike masa da takardar sanarwa a hukumance.
Rahotanni sun nuna cewa majalisar ta dauki wannan mataki ne bayan gabatar da kudirin neman tsige mataimakin gwamnan da shugaban masu rinjaye, Lawan Hussaini Dala, ya yi a zaman majalisar.
Shugaban masu rinjayen ya bayyana cewa majalisar ta aika wasikar domin sanar da mataimakin gwamnan cewa an fara tsarin tsige shi bisa wasu zarge-zarge da ake yi masa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng




