Ganin Tinubu Ya Yi Biris, MURIC Ta Canza Hanyar Neman a Tsige Shugaban INEC
- Kungiyar kare hakkin addinin Musulunci ta MURIC ta kai karar neman a tsige shugaban hukumar INEC zuwa Majalisar Tarayya
- Kungiyoyin Musulmi sun zargi Farfesa Joash Amupitan da wallafa rahoto da ke zargin kisan kare dangi ga Kiristoci a Najeriya
- Sun bayyana dalilan da ya sa suke ganin cewa Amupitan bai cancanci rike kujerar da za ta tabbatar da shugabannin Najeriya ba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Kungiyar kare hakkin Musulmi ta MURIC ta kara kaimi wajen neman a cire shugaban hukumar zabe ta INEC, Farfesa Joash Amupitan, daga mukaminsa.
Bayan sun dade suna kiraye-kiraye ga Shugaban kasa Bola Tinubu, yanzu MURIC ta canza shawara inda ta garzaya gaban Majalisar Tarayya.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa kungiyar tare da wasu kungiyoyin Musulunci na zargin Amupitan da taka rawa wajen wallafa wani takardar shari’a mai shafuka 80.
MURIC ta kai karar Shugaban INEC gaban majalisa
Daily Post ta wallafa cewa wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba 4 ga watan Maris, 2026 Shugaban MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya bayyana ce sun dade suna mika kukansu a kan Amupitan.
Ya ce watanni uku kenan da kungiyoyin Musulmi suka fara kiran a cire Amupitan daga mukaminsa, amma har yanzu yana ci gaba da rike kujerarsa.
Farfesa Akintola ya zargi fadar shugaban kasa da nuna karancin sha’awa wajen sauraron koken kungiyoyin Musulmi.
Ya ce an yi biris da su duk da abin da ya kira hujjoji masu karfi da ke nuna cewa shugaban INEC ya yi ikirarin karya kan Musulman Najeriya a gaban wasu Amurkawa.
Shakkun kungiyar MURIC kan Joash Amupitan
Farfesa Ishaq Akintola ya kuma nuna shakku kan yadda gwamnatin tarayya ke tafiyar da al'amura da adalci, inda ya yi zargin abubuwa marasa muhimmanci sun fi samun kulawa.
Kungiyar ta bayyana damuwa kan ci gaba da kasancewar Amupitan a matsayin shugaban INEC, tana mai cewa abubuwan da suka gabata na iya jefa shakku a kansa.
A cewar kungiyar, batun nuna wariya ga Musulmi na iya zama daya daga cikin manyan batutuwan da za su taso a rikice-rikicen zabe nan gaba.

Source: Twitter
Ya ce:
“Tun da alamu sun nuna fadar shugaban kasa ba ta nuna sha’awar sauraron koken Musulmi kan Amupitan ba, dole mu kai karar zuwa kotun wakilan jama’a, wato Majalisar Tarayya."
Shugaban na MURIC ya jaddada cewa bukatar tsige Amupitan ba ta da alaka da addininsa, sai dai saboda abin da kungiyar ta kira ra’ayi mai tsauri da kiyayya ga Musulman Najeriya.
An bukaci Shugaban INEC ya yi murabus
A baya, mun wallafa cewa tsohon dan takarar Shugaban kasa, Dr. Gbenga Olawepo-Hashim ya yi fatali da sabon jadawalin zaben 2027 da hukumar INEC ta fitar.
Dr. Gbenga Olawepo-Hashim ya ce bai ga dalilin da zai sa a kayyade lokacin da jam'iyyu za su yi zabukan fitar da yan takara kamar yadda aka yi a sabon jadawalin ba.
Tsohon mai neman takarar shugaban kasar ya ce hukumar INEC ba ta da hurumin tsarawa jam'iyyu yadda za su tsaida yan takara a zabe mai zuwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

