Kwamishinan Abba da Ya Yi Murabus Ya Zama Shugaban APC bayan Awanni a Kano

Kwamishinan Abba da Ya Yi Murabus Ya Zama Shugaban APC bayan Awanni a Kano

  • Kwamishinan ma'aikatar ruwa da ya yi murabus a Kano, Umar Haruna Doguwa ya zama sabon shugaban APC ba tare da hamayya ba
  • A babban taro da jam'iyyar ta yi, an tabbatar da Doguwa tare da sababbin shugabanni 23 bayan amincewar wakilai 2,420
  • Bayan an kammala zabe, tsohon Shugaban jam'iyya Abdullahi Abbas ya nemi afuwa, ya kuma yi kira ga hadin kai gabanin zaben 2027

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano –Tsohon Kwamishinan albarkatun ruwa na jihar Kano, Umar Haruna Doguwa, ya zama sabon shugaban jam’iyyar APC a matakin jiha.

Doguwa ya yi murabus daga majalisar zartarwar Gwamna Abba Kabir Yusuf a ranar Litinin 2 ga watan Janairu, 2026 domin neman kujerar shugabancin jam’iyyar mai mulki.

Kara karanta wannan

Bayan komawa APC, Gwamna ya sace gwiwoyin 'yan Arewa kan zaben shugaban kasa a 2027

Umar Haruna Doguwa ya zama Shugaban APC na Kano
Tsohon Shugaban APC Abdullahi Abbas, Umar Haruna Doguwa sabon Shugaban APC na Kano Hoto: Abba K/Na'isa/Mustapha Kakisu Yalwa
Source: Facebook

Jaridar The Guardian ta wallafa cewa ya samu nasara ba tare da wani ya kalubalance shi ba, inda ya karbi ragamar shugabanci daga hannun Abdullahi Abbas.

An zabi shugabannin APC a jihar Kano

Jaridar Leadership ta wallafa cewa rahotanni sun nuna cewa Doguwa ya taba rike shugabancin jam’iyyar kusan tsawon shekaru hudu a wa’adi na biyu na gwamnatin Rabiu Musa Kwankwaso.

Bayan wannan lokaci ne ya mika ragamar jam'iyyar ga Abdullahi Abbas. Yanzu haka, ya dawo kan kujerar shugabancin jam’iyyar bayan shafe kusan shekaru 10.

Abba Kabir Yusuf da Barau I Jibrin sun halarci taron APC
Gwamna Abba Kabir Yusuf Barau I JIbrin Hoto: Sanusi Bature D-Tofa/Barau I Jibrin
Source: Facebook

An zabi Doguwa tare da wasu shugabanni 23 na jiha ta hanyar cimma matsaya a tsakanin masu ruwa da tsaki, kafin daga bisani wakilai 2,420 su tabbatar da su a taron.

An yi zaben ne a filin wasa na Sani Abacha Stadium da ke Kofar-Mata a Kano a daren Laraba 4 ga watan Fabrairu 2026.

Sauran shugabannin APC na reshen Kano

Sauran sababbin shugabannin sun hada da Salisu Ahmad a matsayin mataimakin shugaba; Farfesa Mohammad Yusuf a matsayin sakataren jiha.

Kara karanta wannan

Abin boye ya fito; Gwamna Fintiri ya fadi dalilinsa na komawa APC bayan ficewa daga PDP

Sai kuma Farfesa Nura Yaro Dawakin-Tofa a matsayin mataimakin sakatare. Haka kuma, an zabi Abdul Adamu Fagge SAN a matsayin mai ba da shawara kan harkokin shari’a.

A yayin babban taron, an tabbatar da Kabiru Sule Rogo a matsayin ma’aji; da sauran mukamai daban-daban na jam’iyyar.

Kamar yadda Arewa Update ta fitar da sunayen a shafin Facebook, Salisu Yahaya Hotoro ya zama shugaban matasa, Fatima Dala kuma ta zama shugabar mata.

Da yake sanar da sakamakon, shugaban tawagar wakilan babban taron daga hedikwatar APC ta kasa, Lateef Daban, ya tabbatar da sahihancin tsarin.

Kano ta yi sabon shugaban jam'iyyar APC

A jawabinsa na bankwana, tsohon shugaban, Abdullahi Abbas, ya gode wa ‘yan jam’iyya bisa damar da aka ba shi na yi wa APC hidima tsawon shekaru 10.

Dan Sarki Ya kuma nemi afuwar duk wanda ya bata wa rai yayin gudanar da aikinsa, tare da jaddada cewa jam’iyyar za ta kara karfi da hadin.

Ya kara da cewa za su jajirce domin sake tabbatar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban kasa da kuma Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan Kano a zaben 2027.

Kara karanta wannan

"Ba da jam'iyyu ba ne"; Atiku ya fadi masu fafatawa da Tinubu a zaben 2027

A nasa bangaren, Doguwa ya yi alkawarin gina tsari mai karfi da hadin kai a cikin jam’iyyar domin tabbatar da gagarumar nasara a zaben mai zuwa.

Taron ya samu halartar Gwamna Abba Yusuf, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibrin, Shugaban Majalisar Dokokin Kano Ismaila Falgore da sauran manyan jam'iyya da wakilin INEC.

Gwamna ya fadi dalilin komawa APC

A baya, mun wallafa cewa Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya yanke shawarar komawa jam'iyyar APC bayan ya fice daga PDP da ke mulki.

Ahmadu Umaru Fintiri ya bayyana cewa bai shiga jam'iyyar APC mai mulki ba domin ya kori wani ko wata daga fagen siyasa ba, sai dai domin ci gaban jiharsa.

Gwamnan ya kuma yi kira ga 'ya'yan APC da su karbi sababbin mambobin hannu bibbiyu tare da yi musu alkawarin biyayya ga shugabancin jam'iyyar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng