Yaron Atiku Ya Yi Murabus daga Gwamnatin Adamawa bayan Sauya Shekar Gwamna
- Alhaji Adamu Atiku ya sanar da murabus daga mukamin Kwamishinan Ayyuka da Ci gaban Makamashi na Jihar Adamawa
- Adamu, wanda dan tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ne ya ajiye mukaminsa bayan Ahmadu Fintiri ya koma APC
- Ya gode wa Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri bisa amincewa da goyon bayan da ya ba shi har ya shekara kusan bakwai a gwamnati
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Adamu Atiku ya sanar da murabus daga mukamin Kwamishinan ayyuka da ci gaban makamashi na jihar Adamawa.
Lamarin da ya kawo karshen shekaru bakwai da ya kwashe yana rike da wannan muhimmin matsayi, inda ya ajiye mukamin bayan sauya shekar Gwamna Ahmadu Fintiri.

Source: Twitter
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, tare da bayyana cewa rabuwa da kujerar kwamishina ba ya nufin na daina siyasa.

Kara karanta wannan
APC ko ADC: Gwamna ya gaji da rikicin PDP, ya fara shirin sauya sheka don zaben 2027
Sakon Adamu Atiku bayan ajiye mukaminsa
Adamu Atiku ya ce samun damar ba da gudunmawa wajen bunkasa ababen more rayuwa da kuma fannin makamashi a Adamawa abu ne da ba zai manta da shi ba.
A cewarsa, rike wannan mukami na daga cikin manyan damarmaki da ya samu a rayuwarsa, yana mai jaddada cewa ya yi bakin kokarinsa wajen ganin an samu ci gaba.

Source: Facebook
Adamu Atiku ya mika sakon godiya ta musamman ga Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, bisa yadda ya nuna masa amincewa da kuma ba shi damar taka rawar gani a gwamnatin jihar.
Ya ce:
“Yin hidima a wannan muhimmiyar kujera na daga cikin manyan karramawa a rayuwata ta jama’a. Ina matukar godiya ga Mai Girma Ahmadu Umaru Fintiri bisa amincewa, yarda da kuma damar da ya ba ni na bayar da gudunmawa wajen bunkasa ayyuka da makamashi a jiharmu.”
Adamu Atiku ya godewa mahaifinsa
Haka zalika, ya gode wa iyayensa, tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, da Hajiya Titi Atiku Abubakar.
Ya ce tarbiyyarsu, addu’o’insu da shawarwarinsu sun kasance ginshikin karfinsa a tsawon lokacin da yake kan mukami.
Tsohon kwamishinan ya kuma yaba wa manyan sakatarorin ma’aikatar ayyuka da makamashi, daraktoci, injiniyoyi da sauran ma’aikata bisa kwarewa da jajircewarsu wajen aiwatar da manyan ayyukan more rayuwa a fadin jihar.
Ya mika godiya ga al’ummar Jada bisa goyon baya da kwarin gwiwar da suka rika ba shi a duk tsawon wa’adinsa, yana mai cewa hadin kan da suka nuna ya zame masa abin alfahari.
Adamu Atiku ya bayyana cewa murabus dinsa ba yana nufin ya janye daga harkokin hidimar jama’a ba ne.
A maimakon haka, ya ce wannan mataki ne na shiga sabon babi na fafutukar raya jihar Adamawa ta hanyar inganta hadin kai, ci gaba da bunkasa tattalin arziki.
Gwamnan Adamawa ya sauya sheka
A baya, mun wallafa cewa Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya tabbatar da ficewarsa daga jam'iyyar hamayya ta PDP zuwa APC mai mulki a Najeriya.
Kakakin Majalisar Adamawa da wasu ‘yan majalisa 14 sun riga sun ajiye mukamansu a PDP wanda ke nuna jam'iyyar ta kara wa APC karfi a jihar tsohon Mataimakin Shugaban kasa.
Ahmadu Fintiri ya ce ya dauki wannan mataki ne domin muradun al’ummar Adamawa da hadin kan kasa, yana mai jaddada bukatar kara daidaitawa da gwamnatin tarayya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
