APC ko ADC: Gwamna Ya Gaji da Rikicin PDP, Ya Fara Shirin Sauya Sheka don Zaben 2027
- Gwamnan jihar Zamfara ya fara tunanin makomarsa a jam'iyyar PDP sakamakon rikicin shugabancin da ya dabaibaye ta
- Dauda Lawal Dare ya kira taron masu ruwa da tsaki domin nemo mafita kan matakin da ya kamata ya dauka a siyasance
- Majiyoyi sun bayyana cewa mahalarta taron sun ba Gwamna Dauda shawarwari uku dangane da abin da ya kamata ya yi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana aniyarsa ta neman tazarce a ƙarƙashin wata jam’iyyar siyasa, ba PDP ba, sakamakon rikice-rikice da dama da suka dabaibaye jam’iyyar.
Dangane da haka, Gwamna Dauda Lawal ya kira wani taron gaggawa na wasu mambobin majalisar zartarwa da masu ruwa da tsaki domin ba shi shawara kan hanyar da ya kamata ya bi.

Source: Facebook
Wata majiya da ke da masaniya kan taron ta shaida wa jaridar Nigerian Tribune cewa, gwamnan ya gana da masu ruwa da tsakin ne a daren ranar Juma’a, 27 ga watan Fabrairun 2026 inda aka yanke wasu muhimman shawarwari.
Gwamna Dauda ya gana da masu ruwa da tsaki
Taron, wanda aka gudanar a babban zauren "Rescue Hall" da ke cikin gidan gwamnati a Gusau, ya sami halartar shugaban jam’iyyar, shugaban ma’aikatan fadar gwamnati, sakataren gwamnatin jiha, da wasu manyan dattawan jam’iyyar.
Wannan taro ya zo ne bayan kwashe watanni ana rade-raden sauya sheƙa, duk da cewa na kusa da gwamnan da wasu jiga-jigan APC sun sha musanta hakan a baya, inda suka ce gwamnan ya nuna sha’awar sa ta komawa APC.
“Gwamnan ya gayyaci masu ruwa da tsaki a daren Juma’a. Ya gaya musu cewa ya kira taron ne domin tattauna hanyar da za a bi, ganin yadda jadawalin da INEC ta fitar ya nuna cewa harkokin siyasa za su kankama a watan Afrilu."
- Wata majiya
Dauda zai jira hukuncin kotu
A cewar majiyar, ya shaida wa masu ruwa da tsakin cewa yana da nufin ci gaba da zama a PDP duk da rikicin da ake ciki, inda ya ce zai jira sakamakon hukuncin kotun ɗaukaka ƙara kafin ya yanke mataki na gaba, jaridar The Nation ta kawo labarin.
Sai dai, taron ya amince baki ɗaya cewa gwamnan ya bar PDP. Amma abin da ba a yi matsaya ɗaya a kai ba shi ne jam’iyyar da zai koma.
Wadanne shawarwar aka ba Gwamna Dauda?
An tattaro daga majiyoyi cewa an samu ra’ayoyi daban-daban; wasu na ganin ya kamata gwamnan ya zauna a PDP duba da nasarar da aka samu a kotu kwanan nan wadda ta tabbatar da shugabancin ɓangaren Turaki.
Wasu kuma sun ba da shawarar ya koma APC duba da cewa shi ne kaɗai gwamnan adawa a shiyyar Arewa maso Yamma, inda dukkan sauran gwamnoni shida ’yan APC ne.
Masu goyon bayan komawarsa APC sun bayyana cewa ya kamata gwamnan ya yi amfani da rarrabuwar kan da ke akwai a reshen jam’iyyar APC na jihar, wanda hakan zai ba shi damar samun iko sosai.
A ɓangare guda kuma, wasu sun ba da shawarar ya koma jam’iyyar ADC, suna masu cewa kamar talakawa ba su tare da APC mai mulki, kuma a ganinsu ADC ita ce jam’iyyar adawa mafi ƙarfi a ƙasar.

Source: Facebook
Za a ci gaba da tattaunawa
Duk da cewa babu wata sanarwa a hukumance daga reshen PDP na jiha, wani jigo a jam’iyyar, Kabir Amadu Mai Palace, ya bayyana cewa taron ya amince da a ci gaba da tuntuɓar sauran mambobi a matakin gundumomi da ƙananan hukumomi.
Haka kuma, an tattaro cewa za a kafa wani kwamiti na musamman, inda bayan kammala aikin sa, gwamnan zai bayyana matsayar sa jim kaɗan bayan kammala bikin karamar Sallah (Eid al-Fitr).
Sheikh Abdulmuddallib zai fito takarar gwamnan Zamfara
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sheikh Abdulmuddalib Muhammad Auwal Gusau ya bayyana aniyarsa ta yin takarar gwamnan jihar Zamfara a zaben 2027.
Malamin addinin Musuluncin ya bayyana a wajen tafsirin azumin watan Ramadan cewa zai fito takarar gwamna a 2027.
Sheikh Abdulmuddalib Gusau ya yi kira ga 'yan jihar Zamfara da su fita su yi katin zabe, inda ya ce ta haka ne za su kwaci 'yancin su a kasar nan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


