Sabon Jadawalin Zaben 2027 Ya Fara Tayar da Kura a Najeriya, ADC Ta Dura kan INEC

Sabon Jadawalin Zaben 2027 Ya Fara Tayar da Kura a Najeriya, ADC Ta Dura kan INEC

  • Jam'iyyar hadaka, ADC ta yi fatali da jadawalin zaben 2027 da hukumar INEC ta fitar, ta ce babu adalci a cikinsa kwata-kwata
  • A wata sanarwa da ta fitar dauke da sa hannun mai magana da yawunta, Bolaji Abdullahi, ADC ta kafa hujja da batun rijistar mambobi ta yanar gizo
  • ADC ta ce wasu daga cikin sharuddan da aka gindaya wa jam'iyyu zalunci ne, domin an ba APC mai mulki dama tare da share mata hanyar nasara

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Jam’iyyar ADC ta yi watsi da sabon jadawalin zaben 2027 da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta fitar.

ADC ta yi zargin cewa jadawalin na dauke da “makirce-makirce” da aka tsara domin ware jam’iyyun adawa da kuma share wa Shugaba Bola Tinubu hanya ya sake lashe zaben 2027 ba tare da hamayya ba.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta tanka bayan 'yan adawa sun yi matsaya kan dokar zabe

Bolaji Abdullahi.
Mai magana da yawun jam'iyyar ADC na kasa, Bolaji Abdullahi Hoto: @BolajiAbdullahi
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa hakan na kunshe ne a wata sanarwa da jam’iyyar ADC ta fitar ranar Alhamis, wadda sakataren yada labarai na kasa, Bolaji Abdullahi ya sanya wa hannu.

ADC ta gano shirin da aka yi a dokar zabe

ADC ta soki sababbin sharuddan da aka gindaya a karkashin Sashe na 77 da 82 na Dokar Zabe ta 2026, tana mai cewa sharuddan ba su yi wa jam'iyyun adawa adalci ba.

A cewar ADC, jadawalin INEC ya wajabta wa jam’iyyun siyasa su gabatar da cikakken kundin rajistar mambobinsu kafin ranar 2 ga Afrilu, 2026, gabanin zaben fitar da gwani da aka tsara tsakanin 23 ga Afrilu zuwa 30 ga Mayu, 2026.

Jam’iyyar adawar ta ce wannan sharadi ya zama “wani kalubale mai wahala matuka” wadda zai iya hana jam’iyyun adawa tsayar da ‘yan takara, in ji Leadership.

Ana zargin an shirya wa 'yan adawa makirci

Kara karanta wannan

Atiku da jagororin adawa a Najeriya sun cimma matsaya kan sabuwar dokar zabe ta 2026

ADC ta kara da cewa Sashe na 77(7) na Dokar Zabe ta 2026 ya tanadi cewa duk jam’iyyar da ta kasa gabatar da rajistar mambobinta cikin wa’adin da aka gindaya “ba za ta cancanci tsayar da dan takara ba."

Jam’iyyar ta ce dokar ta bukaci kowace jam'iyya ta mika bayanan mambobinta ta yanar gizo, wanda ya kunshi bayanan sirri na mambobi, Lambar Shaidar Zama dan Kasa (NIN) da hotunansu.

"Ta kuma haramta amfani da duk wata tsohuwar rajista da ba ta cika wadannan sharudda ba. Ta ce gaza bin wadannan ka’idoji zai kai ga soke cancantar tsaida 'yan takara a jam'iyyar," in ji ADC.

ADC ta kuma yi ikirarin cewa jam’iyya mai mulki, APC, ta fara yin irin wannan rajistar tun daga Fabrairu, 2025, lamarin da ya ba ta damar yin nisa kafin sauran jam’iyyun.

A cewar jam’iyyar, wannan na nuna cewa APC ta yi anfani da kasancewarta mai mulki da bayanan cikin gida, domin yanzu ana sa son sauran jam’iyyu su kammala wannan aiki cikin ‘yan makonni kacal.

ADC da APC
Tambarin jam'iyyar ADC da tutar APC a taron magoya baya a Najeriya Hoto: @ADCParty, @OfficialAPC
Source: Twitter

Wane mataki ADC za ta dauka?

Jam’iyyar ta ce ta hada kai da sauran jam’iyyun adawa wajen kin amincewa da abin da ta kira “gurbatacciyar” Dokar Zabe ta 2026, da kuma jadawalin zaben 2027 da INEC ta fitar

Kara karanta wannan

Amnesty ta hurawa Abba Kabir wuta a Kano, ta zarge shi da cin zarafin 'yan adawa

Ta yi gargadin cewa ba za ta lamunci abin da ta kira tsarin zabe na yaudara ba, tana mai cewa tana nazarin matakan da za ta dauka, kuma za ta sanar da jama’a nan gaba kadan.

Jagororin adawa sun yi fatali da dokar zabe

A wani rahoton, kun ji cewa jagororin jam'iyyun hamayya a Najeriya sun yi zama kan sabuwar dokar zabe da Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu.

Shugabannin jam'iyyun hamayyar Najeriya sun yi watsi da dokar zabe ta 2026 wadda Majalisar Tarayya ta amince da ita kwanan nan.

'Yan adawar sun yi kira ga Majalisar Tarayya da ta gaggauta fara wani sabon tsari na yi wa dokar kwaskwarima domin cire abin da suka kira "munanan tanade-tanade."

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262