Daga Adamawa zuwa Legas: Jerin Jihohi 30 da Ke Karkashin APC gabanin Zaben 2027

Daga Adamawa zuwa Legas: Jerin Jihohi 30 da Ke Karkashin APC gabanin Zaben 2027

Adamawa - Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyya mai mulki ta APC a ranarmadu Juma'a.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sauya shekar Fintiri ta sanya jam'iyyar APC ta kara samun rinjaye a Najeriya, inda a yanzu take da iko kan jihohi 30 yayin jam'iyyun adawa suka tsira da jihohi shida kacal.

Gwamnonin jam'iyyasr APC sun kara yawa bayan Gwamna Ahmadu Fintiri ya sauya sheka.
Tutar APC a wani gangamin jam'iyyar da aka gudanar. Hoto: @OfficialAPCNg
Source: Twitter

Sauya shekar gwamnan Adamawa

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Fintiri ya bayyana cewa babban dalilinsa na komawa APC shi neciyar da Jihar Adamawa gaba.

Sanarwar gwamnan ta ce:

"A yau a Yola, I dauki babban mataki da ya shafi makomar jihar Adamawa. Bayan doguwar tattaunawa, mun yanke shawarar hada kai da jam'iyyar APC don daidaita jiharmu a siyasar kasa.
"Sannan hakan zai ba jiharmu damar amfana da shirin Renewed Hope na Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Amma, kudurorinmu na 2019 da 2023 suna nan ba su canja ba.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta tanka bayan 'yan adawa sun yi matsaya kan dokar zabe

"Mun sauya wannan shekar ne tare da dukkan tsare-tsarenmu na siyasa. Yanzu Adamawa ta hau teburin sauyi a matakin kasa."

Tasirin sauya shekar Fintiri ga APC

Wannan sauya sheƙa ta kawo gagarumin sauyi a yawan jihohin da kowace jam'iyya ke iko da su a cikin jihohi 36 na Najeriya.

Yanzu haka jam'iyyar APC tana iko da jihohi 30, yayin da jam'iyyar PDP ke da jihohi 3 kacal bayan sauya shekar Gwamna Fintiri, in ji rahoton The Nation.

Ga yadda rabon jihohin yake a halin yanzu:

Jam'iyya

Yawan Jihohi

APC

30

PDP

3

APGA

1

Labour Party

1

Accord Party

1

Jihohin da APC ke da iko da su a yanzu

Jam'iyyar APC yanzu tana da rinjaye a kusan dukkanin shiyyoyi shida na ƙasar nan yau:

  • Kudu-maso-Kudu (6)

Delta, Akwa Ibom, Edo, Cross River, Rivers, da Bayelsa

  • Arewa-ta-Tsakiya (6)

Benue, Niger, Kwara, Nasarawa, Kogi, da Plateau.

  • Kudu-maso-Gabas (3)

Enugu, Ebonyi, da Imo.

  • Kudu-maso-Yamma (4)

Lagos, Ekiti, Ogun, da Ondo.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta rasa jigo, Gwamna Fintiri ya koma APC bayan zuwan Tinubu Yola

  • Arewa-maso-Gabas (5)

Borno, Yobe, Taraba, Gombe, da Adamawa.

  • Arewa-maso-Yamma (6)

Katsina, Jigawa, Sokoto, Kebbi, Kaduna, da Kano.

Najeriya na da tafiya a tsarin tarayya, kuma tana kunshe da jihohi 36 da kananan hukumomi 774.
Ministan watsa labarai, Mohammed Idris da wasu gwamnonin Najeriya. Hoto: @Hope_Uzodimma1
Source: Twitter

Tambihi kan jihohin Najeriya

Najeriya babbar ƙasa ce da ke gudana a matsayin tarayya, inda take da jihohi 36 waɗanda kowannensu yake da ikon gudanar da kansa.

Waɗannan jihohi suna raba iko ne da gwamnatin tarayya kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada, cewar bayanan da aka samu daga shafin WikiPedia.

Kowace jiha tana da nata gwamnan da majalisar dokoki, waɗanda ke da ikon kafa dokoki da gudanar da ayyukan ci gaba a iyakokin jiharsu.

To sai dai, baya ga jihohi 36, akwai babban birnin tarayya Abuja. Watau ita dai Abuja ba jiha ba ce; yanki ne na gwamnatin tarayya wanda minista ke jagoranta a madadin shugaban ƙasa.

A ƙasa da matakin jiha, akwai ƙananan hukumomi waɗanda su ne mafi kusa da jama'a. Najeriya tana da jimillar ƙananan hukumomi 774 a faɗin ƙasar.

Kara karanta wannan

Magana ta fito, an samu karin gwamnan PDP da yan Majalisa da za su koma APC

Martanin gwamnati kan sauya shekar Fintiri

A wani labari, mun ruwaito cewa, fadar shugaban kasa ta yi martani ga Atiku Abubakar, babban dan adawa da ta ke ganin ya rasa gidansa ga jam'iyya mai mulki.

Gwamnatin Bola Tinubu ta yi martanin ne bayan gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri da 'yan majalisar zartarwarsa, da 'yan majalisar dokoki suka sauya sheka zuwa APC.

Fadar shugaban kasa ta ce wannan sauya sheka ta Fintiri ta zama babbar kalubale ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da ya fito daga Adamawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com