Fadar Shugaban Kasa Ta Jefawa Atiku Magana da Finitiri Ya Koma APC
- A wannan rana ta 27 ga watan Fabrairu, 2026 Gwamna Umaru Fintiri ya sauya sheka daga PDP zuwa APC a jihar Adamawa
- Sauya shekarsa ta jawo dukkanin ‘yan majalisa, kwamishinoni da manyan jiga-jigan PDP zuwa sabuwar jam’iyya
- Tuni Fadar Shugaban kasa ta y i martani ga Atiku Abubakar, babban dan adawa da ta ke ganin ya rasa gidansa ga jam'iyya mai mulki
FCT Abuja - Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC, lamarin da ya girgiza siyasar jihar.
Gwamnan ya sanar da matakin nasa ne a wani jawabi da ya yi wa al’ummar jihar a ranar Juma’ar nan, 27 ga watan Fabrairu 2026.

Source: Facebook
A sakon da hadimin Shugaban kasa Bayo Onanuga ya wallafa a shafin Facebook, Fintiri ya ce sauyin ba wai ya tsaya kansa kadai ba ne.
Fintiri ya bar PDP zuwa APC
Gwamnan ya bayyana cewa bai bar tsohuwar jam’iyyarsa shi kadai ba, domin dukkannin 'yan majalisar zartarwa ta jiharsa, ‘yan majalisar dokoki da sauran manyan jami’an PDP a Adamawa sun sauya sheka tare da shi.
Wannan lamari ya kara karfafa matsayin APC a Adamawa, inda masu sharhi ke ganin cewa wannan sauyi zai sauya akalar siyasa a yankin Arewa maso Gabas baki daya.

Source: Facebook
A kalamansa, Gwamna Fintiri ya ce:
“Na dauki wannan mataki ne bisa la’akari da bukatar ci gaba da muradun jama’ar Adamawa. Lokaci ya yi da za mu hada kai domin samun karin cigaba.”
Fadar Shugaban kasa ta soki Atiku
A sanarwar, Fadar Shugaban kasa ta ce wannan sauyi ya zama babban kalubale ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da ya fito daga Adamawa.
Fadar ta ce yayin da zaben shugaban kasa ke karatowa cikin kasa da shekara guda, sauyin sheka na Fintiri zai zama babban koma baya ga Atiku.
Haka kuma tana ganin koma bayan zai kara karfi musamman ganin cewa sabuwar jam’iyyarsa ta ADC ba ta da karfi sosai a jihar.
Ya ce:
“Da zaben shugaban kasa ya rage kasa da shekara guda, sauyin Fintiri babu shakka babban koma baya ne ga takarar shugaban kasa ga Atiku Abubakar. Jam’iyyarsa ta ADC ba a santa sosai ba a Adamawa. Lallai ya kamata ya sake nazarin burinsa, domin gwamnan jiharsa ya mayar da APC jagora a jihar.”
“Idan dan siyasa ba shi da karbuwa sosai a gida, ba shi da hurumin tallata kansa ga waje. Lokaci ya yi da Atiku zai yi tunanin yin ritaya daga siyasa ya koma hutu a gidansa na biyu da ke Dubai.”
Fintiri ya karbi bakuncin manyan APC
A baya, mun wallafa cewa shugabannin jam'iyyar APC reshen jihar Adamawa sun kai ziyarar ban girma ga Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri a gidan gwamnati.
Wannan ziyara da aka kai yau Juma'a, 20 ga watan Fabrairu, 2026 na zuwa ne a daidai lokacin ya shirya barin jam'iyyarsa ta PDP ya koma APC mai mulkin Najeriya.
Wannan ta sa Fintiri ya zama gwamna na 30 da APC ke da shi a cikin jihohin Najeriya 36 yayin da babban zaben 2026 ke kara matsowa wanda za a yi a Fabrairun 2027.
Asali: Legit.ng

