Saura Watanni 11 Zabe, Attahiru Jega Ya Fadi Barazanar da ake Fuskanta a Najeriya

Saura Watanni 11 Zabe, Attahiru Jega Ya Fadi Barazanar da ake Fuskanta a Najeriya

  • Tsohon Shugaban hukumar zaben Najeriya Farfesa Attahiru Jega ya yi gargadi kan karuwar rashin sha’awar kada kuri’a a Najeriya
  • Ya ce rashin fitowa zabe yana taimaka wa Shugabannin da ba su cancanta ba su dare kujerun iko saboda jama'a sun gaza yin abin da ya kamata
  • Attahiru Jega ya jawo hankalin al’umma kan bukatar amfani da fasaha cikin tsarin zabe don tabbatar da ingancinsa da kuma adalci

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Tsohon Shugaban hukumar zabe ta kasa (INEC), Farfesa Attahiru Muhammadu Jega, ya nuna damuwa kan yadda mutane ke janye kansu daga zabe a Najeriya.

Ya bayyana cewa wannan hali na ko-in-kula ga zaben kasar nan na iya raunana tsarin dimokuradiyya baki dayanta.

Kara karanta wannan

Atiku da jagororin adawa a Najeriya sun cimma matsaya kan sabuwar dokar zabe ta 2026

Farfesa Attahiru Jega ya bayyana damuwa kan rashin son fitowa zabe
Attahiru Jega, tsohon Shugaban hukumar INEC Hoto: Abba Mu Azu Bazzah
Source: Twitter

The Guardian ta wallafa cewa Jega ya bayyana haka a ranar Laraba 25 ga watan Fabrairu 2026 a Fatakwal yayin da ya ke gabatar da lacca mai taken "Muhimmancin zabe mai inganaci ga ci gaban kasa."

Jega ya bayyana damuwa kan zabe

Farfesa Attahiru Jega, wanda farfesa ne a fannin Kimiyyar Siyasa a jami'ar Bayero da ke Kano ya bayyana rashin halartar zabe a matsayin barazana.

Ya kara da bayyana cewa hakan yana baiwa wadanda ba su da cancanta ba damar mamaye shugabanci.

Tsohon Shugaban na INEC ya kara da cewa:

“Idan mutane suka ci gaba da janye kansu daga zabe, masu niyyar cuta za su ci gaba da mamaye madafun iko. Dole ne mu karfafa gwiwar ‘yan kasa su shiga cikin tsarin zabe domin kare ingancin zabuka da kyautata shugabanci.”

Jega ya ce a yayin da rashin sha’awar zabe ke karuwa, kudin yakin neman zabe na ci gaba da hauhawa, abin da ya bayyana a matsayin abin mamaki da damuwa.

Kara karanta wannan

Bayan maganganu sun yi yawa, Tinubu ya yi bayani kan murkushe adawa a Najeriya

Ya yi kira ga duk masu ruwa da tsaki da su gane nauyin da ke kansu su kuma hada hannu don tabbatar da inganci da gaskiyar zabuka.

Kiran Jega ga yan Najeriya kan zabe

Farfesa Jega ya ce matasa da yawa da suka yi rajista don kada kuri’a kan kasa zuwa wajen kada kuri’a, duk da bukatar su na ganin sauye-sauye kamar aika sakamakon zabe ta intanet.

Jega ya shawarci jama'a su rika fitowa zabe
Wani dan Najeriya yana kada kuri'a a Abuja Hoto; INEC Nigeria
Source: Facebook

Duk da goyon bayan fasahohin zamani, Jega ya gargadi cewa dole ne a daidaita su da yanayin Najeriya.

Ya bayyana cewa ingancin zabe yana da mahimmanci ga ci gaban dimokuradiyya, inda ya ce dole ne 'yan kasa su yarda cewa kuri’unsu na da tasiri.

Ya shawarci jama'a da su rika fitowa suna kada kuri'a a lokutan zabe domin ta haka ne za a samu sauyin da ake nema.

INEC canja lokacin zabe

A baya mun wallafa cewa hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta fitar da sabon jadawalin zabukan 2027, tare da sauya ranakun sabanin wadanda ta saka a baya.

An mayar da zaben shugaban kasa zuwa Janairu, bisa tanadin Dokar Zabe ta 2026 bayan korafe-korafe daga al'ummar Musulmi da aka saka lokacin zaben a Fabrairu.

Kara karanta wannan

Kisan masu sallar tarawihi a masallaci ya tayar da hankali, ana ta magana

Sauyin jadawalin ya shafi zaben gwamnoni, domin bin doka da kuma daidaita tsarin gudanar da zabuka a fadin kasar nan yayin da 2027 ke kara matsowa kusa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng